Connect with us

SIYASA

An Yiwa APC Ihu a Abeokuta A Yayin Kamfen Din Buhari

Published

on

Jam’iyyar APC ta bayyana bacin ranta dangane da abin kunyar da ya faru wajen taron gangamin da ta yi a Abeokuta da ke jihar Ogun, inda wadansu da ake zargin magoya bayan Gwamnan Jihar ne, wato Ibikunle Amosun, suka yi ta ihu da jifan rumfar da manyan baki suke zaune a yayin da shugaban kasa ke tsaye a rumfar.

Wanda wannan ya tilastawa jami’an tsaro killace shugaban kasa Muhammadu Buhari domin tabbatar da cewar babu abin da ya same shi. Wannan matsala da APC ta samu a Ogun ya biyo bayan rarrabuwar kan da aka samu wajen tsayar da dan takarar gwamnan jihar,  wanda Gwamna Ibikunle Amosun ke goyan baya ya fadi zaben fidda gwani, abin da ya sa shi komawa wata Jam’iyya domin yin takara.

Wannan ya haifar da dangantakar ta yi tsami tsakanin Gwamnan Jihar da shugabannin Jam’iyyar APC ta kasa. Yayin da yake jawabi wajen taron na jiya, shugaban Jam’iyyar Adams Oshiomhole ya yi ta fuskantar ihu daga masu goyan bayan Gwamnan.

Wannan ya sa Gwamnan ya fto fili yana rokon masu jifar da su kwantar da hankalin su, kada su bashi kunya, inda yake cewa; “Ina rokon ku dan girman Allah, ka da ku bani kunya, Babanmu yana nan.”

Daga karshe shugaban kasa Muhammad Buhari ya daga hannun dan takarar Gwamnan Jihar, Dapo Abiodun, inda ya bukace su da su zabi Jam’iyyar APC ranar Asabar mai zuwa.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: