Connect with us

SIYASA

‘’Annur Multi Purpose Co- operatibe Society’’ Ta Yi Gaggarumin Taro A Zariya

Published

on

Fitacciyar kungiyar ci gaban mata, wadda aka fi sani da ANNUR ‘’MULTI PURPOSE CO-OPERATIBE SOCIETY’’ wadda cibiyar ta ke birnin Zariya, ta yi babban taron kungiyar , wanda ya sami halartar mambobin kungiyar fiye da dari biyar , kuma taron ya gudana ne a makarantar firamare tan a tunawa Sarkin Zazzau Shehu Idris, a birnin Zariya.
Tun farko a jawabinta, shugabar kungiyar Hajiya Hajara Shehu,da farko muma matukar jin dadin tat a yin a yadda mambobin kungiyar da suka fito daga sassa daban – daban na karamar hukumar Zariya, da kuma wasu kananan hukumomi da suke makotaka da Zariya.
Game da ayyukan wannan kungiyar kuma, Hajiya Hajara ta ce, tun farko an kafa wannan kungiyar ce domin ba mata da suka yi rijista da wannan kungiya rancen makudan kudade, a matsayin jari, da za su yi amfani da kudin, wajen yin sana’ar da za su dogara da ita, ko kuma samun wata sabuwar sana’a, da za su rika juya wadannan kudade na sayen wasu abubuwa da suke bukata da za su juya wadannan kudade.
A cewar Hajiya Hajara, wannan kungiya da ta ke yi wa shugabanci, ba su taba samun tallafi daga kamnatin karamar hukumar Zariya ko jihar Kaduna ko kuma tarayyar Nijeriya ba, dukkan rancen kudaden da suke mata takwarorinsu, a tsakaninsu suke hada kudaden, daga nan sais u zabi mata da suke cikin wannan kungiyar, sais u danka ma su kudaden domin yin kasuwancin da suke bukata da kudin da aka ba su.
Hajiya Hajara Shehu ta kara da cewar, a wasu lokuta, in sun ba mambar kungiyar rance, in ta nemi shawarar yadda za ta juya kudin da aka ba ta, ba tare da bata lokaci ba, a kan ba wadda ta nemi shawarar yadda za ta fara kasuwancin da kudin da aka bat a a matsayin rance, in kuma, kamar yadda Hajiya Hajara ta ce, in wadda aka bat a rancen tan a da idon yin sana’ar , da zarar an ba ta kudin, sai ta ci gaba da sana’a ko kuma kasuwancin da ta saba yi da wannan rance da ke hannunta.
A dai jawabinta, shugabar wannan kungiya, Hajiya Hajara Shehu ta nuna matukar damuwar ta ga wasu mambobin kungiyar da bayan an ba su rancen,sai su manta rance aka ba su a karkashin wannan kungiya, ba tallafi aka ba su ba, wato, sai su juya bayansu da tunanin dawo da kudaden da aka danka ma su a matsayin rance, sai dai kuma shugabar ta yaba wa wasu mambobin kungiyar, na yadda suke biyan rancen da aka ba su, kamar yadda aka yi taraliya da su, kafin a ba su rancen.
Hajiya Hajara Shehu ta kammala da yaba wa kwamishinan harkokin mata a jihar Kaduna, Hafsat Mohammed Baba, na yadda ta ke tallafa wa kungiyoyin mata a jihar Kaduna, sai Hajiya Hajara ta yi kira ga kwamishinar da ta sa kungiyar ANNUR a cikin sahun wadanda suke amfana da tallafin da gwamnatin jihar Kaduna ke yi wa kungiyoyin da aka kafa su domin ci gaban al’umma, musamman kungiyar mata da suke karamar hukumar Zariya.
Hajiya Halima Aliyu, tsohuwar kansila ce a karamar hukumar Zariya, ta farad a yaba wa shugabar wannan kungiya, na yadda ta fara bayar da rancen ga mata ita kadai, daga baya, ta jawo wasu suka kafa wannan kungiya, wanda a yau, kamar yadda ta ce, ayyukan da wannan kungiya ke aiwatarwa, gwamnati ne ke yi, ba kungiya ba. A kan haka, sai ta shawarci mambobin kungiyar da su rika cika alkawarin da aka yi da su a rubuce domin wasu mambobin kungiyar su sami damar amfana da wannan rance da zai inganta rayuwarsu.
Wasu mambobin kungiyar da wakilinmu ya sami damar zantawa da su, sun yaba wa shugabar wannan kungiya, Hajiya Hajara Shehu, na yadda ta jajirce, na ganin ta yi amfani fa dukiyar tat un da farko, domin tallafa wa mata da suke son yin kasuwanci ko kuma sana’ar dogaro da kai.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!