Connect with us

LABARAI

APC A Zamfara: Gamayyar ’Yan Takara 8 Sun Fallasa Asirin Gwamna Yari

Published

on

Gamayyar ‘yan takarar gwamna takwas karkashin inuwar jam’iyyar APC a Jihar Zamfara sun fallasa wani shiri na gwamna Abdul’aziz Yari na son yin amfani da karfin gwamnati wurin shirya makarkashiya da kotu don a tilastawa INEC wurin amsar ‘yan takarar APC tsagin gwamnan.
Gamayyar ‘yan takarar sun yi wannan tonon silili ne a wurin taron manema labarai da suka gudanar shekaran jiya Lahadi a Jihar Kaduna.
Sanata Kabir Garba Marafa, wanda shi ne ya yi jaawabi a madadin gamayyar ‘yan takarar, ya bayyana cewa, wannan shiri na gwamna Yari ba komi bane face yarinta da rashin sanin ciwon kai.
Tawagar gamayyar ‘yan takarar G8 din sune; Sanata Marafa, Dakta Dauda Lawal (Gamjin Gusau), Malam Ibrahim Wakala, Mahmuda Shinkafi, Mansur Dan-Ali, Aminu Sani Jaji, Abu Magaji, da kuma Mohammed Sagir Hamidu.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta haramtawa Jam’iyyar APC tsayar da kowane dan takara a Jihar a bisa yanda Jam’iyyar ta gaza gudanar da zaben fitar da gwani a iya lokacin da hukumar ta kayyade saboda rigingimun cikin gida da suka addabi Jam’iyyar a lokacin.
Sai dai, kwamitin gudanarwar Jam’iyyar ya cimma yarjejeniyar tsayar da Lawal a matsayin sasanci, wanda a yanzun haka maganan tana gaban kotun daukaka kara.
A ranar Juma’a, Gwamna Yari ya ce, ba za a yi zabe a Jihar ba matsawar babu ‘yan takaran Jam’iyyar APC a cikin zaben, ya nemi hukumar zaben da ta yi aiki da hukuncin da babbar kotun Jihar ta zartas wacce ta tabbatar da cewa, tabbas an gudanar da zaben fitar da gwanin a Jihar.
“A kan haka, ‘yan takaran Takwas suke yin kira ga hukumar shari’a ta kasa da ta gaggauta shiga tsakani a kan lamarin,” in ji Marafa.
“In ba a manta ba, ‘yan takara Tara ne suka sayi fom din shiga zaben fitar da gwani na dan takaran Gwamna a wanan zaben na 2019. Takwas daga cikin Taran sai suka hada kansu suka kafa abin da ake kira da G-8, a bisa yanda rikici ya mamaye zaben fitar da gwani na Jam’iyyar a Jihar.
“Bayan yanke hukuncin da babbar kotun Jihar ta yi kamar yanda muka ambata a baya ne sai biyu daga cikin wadanda ake karan, Sanata Kabiru Garba Marafa da Honorabul Aminu Sani Jaji, suka shigar da daukaka kara daban-daban a kan hukuncin da babbar kotun ta Jihar ta zartas.
“Babban abin lura a kan daukaka karan shine, ba wani Lauya da ya taba ganin inda kotun daukaka kara ta taba tabbatar da wani hukunci wanda wata kotun da ke karkashinta ta zartas.
“Sai dai mu zura ido mu ga hukuncin da shari’an za ta zartas a kan lamarin, musamman in an yi la’akari da hukuncin da kotun koli ta zartas a ranar Juma’a 8 ga watan Fabrairu, 2019, inda ta tabbatar da cewa hukumar zaben ta yi daidai da ta hana Jam’iyyar ta APC tsayar da kowane dan takara a Jihar a bisa yanda Jam’iyyar ta sabawa ka’idar zaben fitar da gwanin a Jihar.
Wata kotun daukaka kara da ke Sakkwato, ta dage sauraron maganan har sai ranar 19 ga watan Fabrairu, inda ta baiwa dukkanin sassan biyu damar gabatar da korafin su.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: