Connect with us

LABARAI

Ba Jirgin Da Zamu Bari Ya Yi Aiki A Nijeriya Da Tayar Da Ta Cinye  -Hukumar NCAA

Published

on

Hukumar dake kula da jigilar jiragen sama ta Nijeriya (NCAA) ta ce babu wani jirgin da zai yi aiki a Nijeriya da tayar da ta cinye, saboda dokokin da hukumar ta sanya na tsare rayukan al’ummar Nijeriya da suke hawa  jiragen, babban janar manaja na hulda da jama’a na hukumar ne ya kara tabbatar da hakan yau Litinin a ofishin hukumar dake jihar Legas.

Manajan yace; wannan bayan ya wajaba ma hukumar ta yi, saboda wani hoton tayar jirgi da ta cinye, ana ta yawo da hoton a shafukkan intanet cewa, wannan hoton na wata tayar wani jirgi ne a daya daga cikin filayen sauka da tashin jiragen sama na Nijeriya, manajan ya ce, sam wannan hoton jirgin ba a Nijeriya bane ma, saboda yadda hukumar ta ke bin dokokin jigilar jiragen sama ta duniya sau da kafa.

Manajan ya tabbatar da cewa babu jirgin saman da za a bari ya yi aiki a fadin kasar nan, har sai hukumar ta tabbatar da cewa jirgin ya cika duk ka’idojin da suka dace da dokokin jigilar jiragen sama ta duniya da ta Nijeriya, akwai shaida da ake baiwa duk wani jirgi da ya cika wadannan ka’idojin, don haka ba zai taba yiwuwa a samu hakan ba a Nijeriya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!