Connect with us

KASUWANCI

Babban Bankin Nijeriya Ya Zuba Dala Miliyan 279.13 Don Bunkasa Kasuwancin

Published

on

Babban Bankin Nijeriya CBN ya zuba dala miliyan 279.13 da kuma kudin kasar China na CNY miliyan 46.92 a cikin kasuwar SMIS a matsyin daukin yin musayar kudaden kasar waje. Adadin cinikayyar da akayi a ranar Juma’ar data bata ta Nina cewar, an zuba daka miliyan 279. 13 din ce saboda bukatar da masu hada-hadar a fannonin aikin noma, masu jiragen sama, albarkatun man fetur, sarrfa kayayyaki da kuma masu injinoni suka nuna bukata. Daraktan sashen bayanai na, Babban Bankin Nijeriya CBN, Isaac Okorafor ya bayyana cewar, kudin kasar China na CNY miliyan 46.92 an zuba sune saboda dimbin bashin na Renminbi da suka mamaye wasikun na bashin fannonin noma da kuma kayayyaki. Hada-hadar da aka gudanar a ranar ta Juma’a ta Nina cewar, yin kari me na dala miliyan 210 da aka zuba a manyan kasuwanci, kananan da kuma matsakaita kamar yadda hada-hadar ta ranar Talata 5 ga watan Fabirairun shekarar 2019 ta nuna. Da take bayyana gamsuwar sa akan yadda mahukuntan bankin na CBN sukayi wajen samar da daidaito akan bangarorin da ban-da ban na samar da kudin musayar na kasar waje a kasuwar, Okorafor ya dangknta hakan bin ka’idar da bankin na CBN ya yi wajen tabbatar da yin gaskiya akan hada-hadar ta kudin musayar na kasar waje. Sakamakon musayar da akayi data rufe akan naira 358 sabanin dala daya a ranar ta Juma’a Okorafor ya bayyana kwarin gwaiwar sa akan cewar, naira zataci gaba da morewa saboda daukin da Babban Bankin Nijeriya CBN ya samar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: