Connect with us

KASUWANCI

Bankuna Za Su Tallafa Wa Matatun Mai A Nijeriya

Published

on

Bankin First Bank dake cikin kasar nan, ya yi alkawarin ci gaba da tallafawa kamfanonin dake sarrafa man fetur da isakar gas dake cikin Nijeriya na kudin da suke bukata don ciyar da fanonin gaba. Babban Jami’in Bankin na First Bank Adesola Adeduntan ne ya bayyana hakan a lokacin da yake yin jawabin sa a taron kasa da kasa na makamashi na EFF a garin Abuja. Adesola Adeduntan ya kara da cewar, Bankin ya jima yana bayar da iron wannan tallafin ga kamfanonin masu sarrafa man fetur da kuma iskar gas musamman na cikin gida Nijeriya yadda zasu inganta ayyukan su a cikin nasara. Babban Jami’in Adeduntan wanda Babban Darakta na Bankin na First Bank Abdullahi Ibrahim ya wakilce shi a gurin taron ya ci gaba da cewa,talkafin na kudin zai taimaka gaya wajen samar da ci gaba a fannonin a cikin sauri. Ya kara da cewar, hakan zai kuma kara taimakawa wajen janyo hankalin wadanda zasu zuba jari a fannonin na dogon zango. Ya sanar da cewar, Bankin ya jima yana bayar da iron wannan tallafin ga fannonin ta hanyar zuba kudi akan wasu kayayyaki da suke samar da kudade ga fannonin. Acewar Adeduntan, fannin mai na kwangilar bankin an tsara shine don bukatar kudin da wadanda suke dashi na kudi na cikin gida Nijeriya wadanda kuma dama can abokan huldar bankin ne ko kuma suna son su zamo abokan hudda da bankin. Ya ce, irin wannan tallafin ya amfani kamfanonin da suke a cikin fannonin kuma tallafin ya inganta kasuwanci su matuka a shekaru da dama da suka shige. Acewar Adeduntan, bankin ya kuma bayar da tallafin kudi ga albarkatun mai na kasan ruwa. Albarkatun man sun hadada na samfarin mai na PMS, Dizil da kuma Kalanzir. Ya bayyana cewar, bankin yana kuma bayar da tallafin ga abokan huddar sa da ya jima dasu da kuma sababbin abokan huddar sa da suka yi rijista da kungiyin mai dake kasar nan. A karshe Adeduntan ya ce, irin wannan tallafin ya kara ciyar da kasuwanci su gaba da kuma toshe gibin da ka iya kunno kai.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!