Connect with us

KASUWANCI

FRSC Ta Horas Da Direbobi 2,000 A Shekarar 2018

Published

on

Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa FRSC ta horas da samada Direbobi 2,000 na Kamfanin Peace Mass Transit. Kamfanin ne ya sanar da hakan a cikin sanarwar da ya fitar a ranar Alhamis data gabata. Acewar sanarwar, direbobin da aka horas sune na rukunun farko kuma za’a shafe sati shida ana yi masu horon. Mataimakin Shugaban Kamfanin Cif Emilia Onyishi ya ce, kamfanin zai kuma ci gaba da baiwa direbobin nasa horon yadda zasu dinga gudanar da tukin su akan manyan hanyoyin kasar nan ba tare da haifar da wata matsala ba. Cif Emilia Onyishi ya sanar da hakan ne a lokacin da aka fara gudanarwa da direbobin horon a yankin Emene dake cikin jihar Enugu. Ya yi nuni da cewar, aikin mu ne mu baiwa direbobin horon, musamman yadda za’a magance aukuwar hadurra a mayan titunan dake kasar nan. Ya yi alwashin cewar, Kamfanin bk zaiyi kasa a gwaiwa ba wajen kashe dukkan kudaden da suka dace don kare lafiyar direbobin sa da kuma ta matafiyan da suke hudda da Kamfanin. Acewar mataimakin shugaban akwai kuma wani horon da Kamfanin ya sabawa yiwa direbobin nasa wanda manajan kula da bayar da kariya na Kamfanin ne yake sanya ido akan horon. Ya sanar da cewar, Kamfanin zai kuma ci gaba da bayar da irin wannan horon domin sauka lafiya, ita ce babbar mahimmanci ga direba da kuma matafiyi a gare mu. Onyishi ya kuma yi kira ga direbobin da suka amafa da horon su yi amfani da damar don fuskantar kalubalen dake gaban su na yin tuki. Shi kuwa Mista Ugah Okoronkwo wanda ya wakilci Kwamandan Hukumar na jihar Enugu ya yabawa Kamfanin akan baiwa direbobin sa horon, tare shawartar Kamfanin kada yo kasa a gwaiwa wajen zuba jari don kare rayukan direbobin sa da kuma ta matafiyan dake hudda da Kamfanin.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!