Connect with us

WASANNI

Guardiola Ya Ce Ba Za Su Sake Komawa Na Biyu Ba

Published

on

Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, Pep Guardiola ya bayyana cewa kungiyarsa bazata taba yarda ta sake sakkowa daga saman teburin firimiya ba a halin yanzu da suka sake komawa na daya.
Manchester City ta sake dare kan teburin firimiya, bayan da ta ragargaji kungiyar kwallon kafa ta Chelsea a wasan mako na 26 da suka fafata a Ettihad a ranar Lahadi inda Manchester City ta yi nasarar doke Chelsea da ci 6-0, kuma Sergio Aguero ne ya ci kwallaye uku, sai Raheem Sterling da ya ci biyu sannan Ilkay Gundogan da ya zura daya a raga.
Kwallayen da Aguero ya ci uku rigis a karawar sun sa ya yi kankankan da tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Newcastle da Ingila, Alan Shearer da ya yi bajintar zura kwallaye uku sau 11 a tarihin gasar firimiya.
Da wannan sakamakon Manchester City ta koma mataki na daya da maki 65 a kan teburin firimiya, inda Liberpool ta koma ta biyu duk da maki 65 da take da shi, sannan Tottenham ta uku da maki 60.
Chelsea kuwa ta koma ta shida da maki 50, Arsenal ta zama ta biyar kenan duk da maki 50 da take da shi, inda Manchester United ta koma ta hudu, bayan da ta yi nasarar doke Fulham 3-0 a ranar Asabar.
Manchester City ta taba doke Chelsea 6-2 a ranar Asabar 26 ga watan Nuwambar 1977 tun a wasan rukuni na farko kan a kai sauya wa firimiya fasali wanda hakan yasa rabon da wata kungiya tayiwa Chelsea irin wannan cin yau shekara 26.
Chelsea da Manchester City za su sake haduwa a wasan karshe a gasar cin kofin Caraboa Cup a ranar Lahadi 24 ga watan Fabrairu a filin wasa na Wembley dake babban birnin kasar wato Landan.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: