Connect with us

LABARAI

Gwamnati Ta Yi Tsimin Dala Miliyan 550 Ta Hanyar Korar Ma’aikatan Bogi

Published

on

Shugaba Buhari ya ce, Gwamnatin tarayya ta yi tsimin dala milyan 550 ta hanyar koran ma’aikatan bogi daga asusun biyan ma’aikatan gwamnatin tarayya.
Shugaba Buhari, ya bayyana tabbacin sa na cewa, za a kara gano wasu kudaden ta hanyar tsarin nan na ‘Yan fallasa, domin a yanzun haka an kwato sama da dala milyan 370 daga lokacin da aka kaddamar da shirin a 2016.
Ya ce, “Za a kara gano ma’aikatan bogi da suke ci a asusun gwamnati.
Don haka sai ya nemi ‘yan Nijeriya, musamman masu zabe da su tabbatar da sun yi zabe mai kyau a zaben Shugaban kasa da ke tafe, ta hanyar sake zaban Jam’iyyar APC domin dorewa da ci gaban yaki da cin hanci da karban rashawa.
Ya bayar da tabbacin ci gaba da bin tsarin gwamnati a kan yakin da ake yi da cin hanci da rashawa duk da cewa gwamnatinsa ta canza hanyan da take bi wajen yaki da cin hancin da rashawa a kasar nan.
Shugaban ya kara da cewa: “Wata karin magana ta Yarabawa tana cewa, marar lafiya ne kadai zai iya tatsan Zaki. Kamar haka ne, yaki da cin hanci da rashawa mawuyacin al’mari ne, amma dai ba mai gagara ne ba. Na san ‘yan Nijeriya masu yawa za su so ganin an gaggauta ne. Ni ma haka. Amma duk da hakan, tilas ne mu bi ta hanyar da ta dace.
“Zabin da ke gaban masu zabe guda daya ne: Shin za mu ci gaba ne a kan wannan tafarkin na yakar cin hanci da rashawa? Ko kuma mu koma baya ne, mu koma kan karya, yanda ake yin abubuwa a baya? Ni na san wanda ya kamata na zaba. domin hakan ne nake neman ‘yan Nijeriya da su kara mani wasu shekarun guda hudu na yi masu aiki.”
Ya kuma sha alwashinsa a matsayinsa na Shugaban Nijeriya zai ci gaba da sauke nauyin da aka dora ma shi, wajen magance matsalar cin hanci da rashawa , samar da tsaro, da farfado da tattalin arziki.
Sai dai, Shugaban ya bayyana cewa, yaki da cin hanci da rasahawa ne zai baiwa mahimmanci domin tabbatar da samun nasarar shirye-shiryen gwamnati na farfado da tattalin arzikin kasa.
Duk suna da mahimmanci. Amma dayansu duk ya fi su mahimmanci, shi ne kuwa kawar da cin hanci da rashawa.
“Duk wani tsarin da ba zai yaki cin hanci da rashawa daga tushen sa ba, tabbas wannan tsarin zai ruguje ne. yaki da cin hanci da rashawa shi ne ya kamata ya zama tushen gyara kasarmu, gina tattalin arzikinmu, samar da kyawawan manyan ayyukan raya kasa da ilmantar da zuriyarmu.
Karatun Likitoci 14 Da Jihar Kano Ta Dau Nauyinsu Zuwa Indiya Na Fuskantar Barazana
Rahotanni sun bayyana cewa; Dalibai guda 14 wadanda aka tura kasar waje domin karatun Likitanci suna dab da rasa takardar kammala karatun na su bayan watsi da su da gwamnatin jihar Kano din ta yi na kin biyan kudaden karatun na su.
Daya daga cikin daliban ya kokawa LEADERSHIP HAUSA A YAU da cewa; “Kuna magana da daya daga cikin dalibai 14 da gwamnatin jihar Kano ta tura karatun Likitanci kasar Indiya (SSIMS & RC DABANGERE, KARNATAKA INDIA). Yau kusan shekara biyu ke nan gwamnatin jihar Kano ta manta damu, ba kudin abinci balle kudin kula da sauran al’amuran rayuwa.”
Har wala yau dalibin ya ci gaba da cewa; “hakan yasa rayuwa ta tsananta garemu amma duk da haka bamu gaza ba muka dage mu ka yi karatun har Allah ya bamu nasara muka gama. Yanzu haka mun yi aiki na shekara daya a nan domin samun gogewa (Internship), amma sakamakon bashin da makaranta take bin gwamnati kimanin naira miliyan 22 na baki dayanmu mu 14 yasa sun ci alwashin ba za su saka sunayenmu cikin wadanda za a yaye ba a wannan shekarar muddin gwamnati bata biya kudin ba kafin lokacin yaye dalibai ba wanda za a yi cikin wannan watan da muke ciki.”
Dalibin ya tabbatar da cewa; sun yi iya bakin kokarinsu domin su sanar da wadanda suke da hakkin biyan kudin, amma abin ya ci tura. “Wajen wata 9 ke nan muna rokon a taimaka mana abin ya faskara. Wannan ce tasa muka yanke shawarar mu biyo ta wajen ku watakila Gwamna zai sami labarinmu ya fidda mu daga wannan halin da muke ciki.” Dalibin ya jaddada.
A karshe daliban sun nemi da a taimaka musu domin Iyayensu ba masu karfi bane, ya ce; idan ba a biya kudin ba; “Zamu yi asarar karatunmu domin ba zamu sami shaidar kammalawa ba.”
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!