Connect with us

LABARAI

Har Yanzu Leah Sharibu Na Raye -Lai Mohammed

Published

on

Ministan yada labarai, Lai Mohammed, ya ce Leah Sharibu, ba ta mutu ba.
Leah Sharibu, ita ce kadai Kirista a cikin dalibai ‘yan mata 119 na Makarantar Sakandare ta Dafchi, Jihar Yobe, da ‘yan Ta’addan Boko Haram suka sace a watan Fabrairu, 2018.
Duk sauran ‘yan matan an sake su tun da jimawa.
Kusan shekara guda da sace, Leah Sharibu, yanzun akwai jita-jitar da ke yawo mai nuna cewa ta mutu a hannun wadanda suka sace ta. Da yake magana da manema labarai a Jihar Kwara ranar Lahadi, Ministan ya ce, “Wannan labarin karya ne” duk makirci ne na abokanan hamayya na ganin sun dusasar da kimar gwamnatin Jam’iyyar APC.
“A kullum suna kara firgita ne da irin goyon bayan da Shugaban kasa yake samu a duk sassan kasar nan, don haka suka yanke shawarar yayata labarun karya, su kunna wutar rikicin da za ta nuna zaben ana yin sa ne a tsakanin Musulmi da Kirista, ko kuma tsakanin Kudu da arewa, amma duk mutane ba za su saurare su ba.
Ministan ya ce, Jam’iyyar ta APC a Jihar ta Kwara tana ta yin taruka ne domin ta tabbatar da nasarar ziyarar kamfen da Shugaban kasa zai kai a Jihar a ranar Litinin.
“Mun ga yanda tarukan suka gudana a sauran kasan nan, don haka muna son tabbatar wa da Shugaban kasan ne cewa, taron na Jihar Kwara ya zama daya daga cikin mafiya kyau, a kan yawan Jama’a, kayatarwa da makamantan hakan.
Mohammed ya ce, “Jama’an da za su fito tarban Shugaban kasan za su kasance na kwarai ne, domin mu Jam’iyyarmu ba ta aminta da yin hayan jama’a domin su cika wuri ba.”
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: