Connect with us

LABARAI

Hukumar DSS Za Ta Tuhumi  Mai Magana Da Yawun PDP Na Kaduna A Kotu Bisa Zargin Kalaman Harzuka Al’umma

Published

on

Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta ce zata gurfanar da mai magana da yawun kamfen din jam’iyyar PDP na jihar Kaduna a kotu, hukumar ta bayyana hakan ne yau Talata, inda ta ce za ta tuhumi Mista Ben Bako da furta kalaman da zasu iya harzukka al’umma.

A cikin bayanan da darektan hukumar na jihar kaduna, Mista AI Koya ya fitar yau Talata a Kaduna, ya ce da zarar an kammala bincike za a gurfanar da Mist Bako a gaban kotu, a ranar 9 ga watan Fabrairu hukumr ta gayyaci Mr Bakon don ya yi karin bayani kan wasu kalaman harzukka jama’a da ya furta, Bako ya furta wadannan kalaman ne a daidai lokacin da jam’iyyar PDP take gudanar da yakin neman zabe a garin Kafanchan.

A cikin kalaman da ake zargin Mista Bakon ya furta harda cewa, magoya bayan jam’iyyarsu su hallaka duk wanda ya zabi wata jam’iyyar in dai ba jam’iyyar PDP Ba, tuni dai aka dinga yada hoton bidiyon wannan kalamai na Mista Bako, wadanda hukumar tace suna cike da hadari sosai, musamman a daidai lokacin da kasar nan take cikin wani hali.

Hukumar ta ce sam wannan ba abu bane da yakamata a kyale shi, don haka hukumar tana kan gudanar da bincike, kuma da zarar ta kammala zata gurfanar da shi a gaban kotu, akwai sauran mutanen da ake bincika ma, shi dai Mista Bako tsohon kwamishinan yada labarai ne na jihar Kaduna a zamanin gwamnatin PDP da ta shude.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!