Connect with us

WASANNI

Juventus Za Ta Hakura Da Pogba Domin Siyan Isco Da James

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Jubentus ta bayyana cewa ta hakura da neman tsohon dan wasanta, Paul Pogba daga Manchester United inda zata koma neman Isco na Real Madrid da James Rodriguez shima na Real Madrid wanda yake zaman aro a Bayern Munchen.
Kungiyar kwallon kafa ta Juventus tayi alkawarin kashe makudan kudade a kasuwar siyan ‘yan wasa mai zuwa domin kara karfi inda ta shirya komawa domin siyan dan wasa Paul Pogba dan kasar Faransa.
Kamar yadda rahotanni suka bayyana kungiyar kwallon kafa ta Juventus tana shirin kashe makudan kudade wajen siyan manyan ‘yan wasa a kakar wasa mai zuwa kuma Paul Pogba yana daya daga cikin ‘yan wasan da ake ganin kungiyar zata nema.
Isco da Rodriguez dai kwantaraginsu zai kare a kungiyar Real Madrid a kakar wasa mai zuwa kuma kociyan kungiyar, Santiago Solari baya anfani da Isco a wasannin kungiyar akai akai wanda hakan yasa dan wasan yake ganin zai bar kungiyar.
Dan wasa Paul Pogba dai bashi da niyyar barin kungiyar tun bayan da kungiyar ta kori Mourinho wanda daman dashi ne basa shiri kuma har ya dinga ajiyeshi a wasu daga cikin wasannin kungiyar.
Kawo yanzu dai Manchester United bazata yarda ta siyar da dan wasan nata ba wanda ya taimakawa kasar Faransa ta lashe gasar cin kofin duniya wanda aka buga a kasar Rasha a shekarar data gabata.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!