Connect with us

LABARAI

Kungiyar CAN Ta Shirya Gangamin Addua A Kan Zabe A Kaduna

Published

on

Akalla mabiya addinin kirista dubu 3 ne suka gudanar da gangamin addu’a na kan zaman lafiya a zabe mai zuwa a fadibn Nijeriya.
Shugaban kungiyar Kiristocio ta kasa reshen jihar Kaduna CAN, Rabaran John Hayab ne ya shaidawa manema labarai jiya a Kaduna, inda y ace, an gudanar da gangamin cocin ‘Albarka Fellowship Baptist’.
Hayab ya ce, manufar yin addu’ar shi ne, don ganin irin yanda guguwar rikicin siyasa ke kara habbaka, da kuma tsoron tashin hankali da fadace-fadace.
‘Mun yi imani da cewa, ba abin da ya gagari Ubangiji, dan haka muka kira Kiristoci da mu zo mu mika kukan mu ga Ubangiji domin samun zaman lafiya da kuma gudanar da ingantaccen zabe ba tare da wani rikici ba,’ inji Rabaran Hayab.
Ya ci gaba da cewa, ‘za a yi zabe a kare, dan haka, bai kamata mu raba kanmu saboda zabe ba, mu ci gaba da hankuri da juna.’
Haka kuma, shugaban kungiyar ya yi kira ga hukumar zabe ta kasa INEC, da jami’an tsaro da su gudanar da ayukkan su bisa doka da oda, da nuna gogewa da kwarewar aiki.
‘Muna addu’a, ga wadanda za su gudanar da aikin zabe, Allah ya yi masu jagoranci su gudanar da ayukkan su yanda ya kamata. Domin ko da mutum ya so yin abin da bai kamata ba, to Allah zai iya canza niyar sa,’ inji shi
daag karshe, ya yi kira ga masu jefa kuri’a da su zama cikin lumana ba tare da taayar da hargitsi ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!