Connect with us

KASUWANCI

Layuyyukan Samar Da Wutar Lantarki A Nijeriya Na Fuskantar Matsaloli

Published

on

Fannin samar da wutar lantarki na kasar nan ya fuskanci gazawar da ta kai har sau 100 a cikin shekaru biyar da suka shige a cikin kasar nan. Yau kusan shekaru biyar da watanni uku ke nan da aka sayar da hannun Karin fannin, amma had yanzu bata sake zani ba. A lokacin mulkin Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ne aka sayar da Kamfaninonin rabar da wutar guda 11 da kuma kamfanonin shida da suka zuba jari su a fannin a ranar 1 ga watan Nuwambar shekarar 2013. Kamfanin rkbar da wutar na kasa TCN dake kula da babban Latin samar da wutar ta kasa, wanda har yanzu TCN yake kula da samar da wutar a madadin gwamnati. Kamar yadda bayanan da aka samo a ranar Juma’ar daga Kamfanin TCN ya nuna, manyan layukan samar da wutar na kasa guda 97 sun kai jimla 73, inda kuma guda hudu 24 suka gaza yin wani katabus daga ranar 1 ga watan Nuwambar shekarar 2013 da kuma ranar 31 ga watan Janairun shekarar 2019. Acewar Hukumar dake sanya ido akan wutar lantarki ta kasa NERC, sakamakon wannan jimlar ta gazawar manyan layukan na kasa, hakan ya nuna cewar, za’a fuskanci karancin samun wutar a daukacin fadin kasar nan ko kuma a samu dan nakasun gazawar fannin. Har ila yau, fannin na samar da wutar a babban layin na kasa zaici gaba da fuskantar gazawar in har ba ‘a dauki matakan da suka dace ba, inda dauki wutar data dinga sahafe mintuna goma kafin a cike gibin rashin samun wutar da aka rasa. Daga cikin kamfanonin samar da wutar guda biyar, daukacin su basu da tsarin adana wutar har zuwa karfe 6 na safiyar ranar Alhami data gabata, inda megawatts din su ta kai 295. Tashoshin samar da wutar na Egbin dake a cikin jihar Delta ta Olorunsogo NIPP, Geregu NIPP da kuma ta Omotosho NIPP. A cikin rahoton NERC na karshen zangon Hukumar ta bayyana cewar, don a tabbatar da kiyaywar ci gaba da samun raguwar daidaiton a babban layin samar da wutar na kasa ta hanyar yin hadaka da Hukumar TCN, an kara yin kaimi wajen sanya ido da kuma dubawa don a tabbatar da cewar kamfanonin dake ranar da wutar suna kiyaye sharuddan da aka gindaya. Bugu da kari, Hukumar ta kuma amince da kara samar da ma’adanar tara wutar da nufin tara isasshiyar wutar don baiwa babban layin samar da wutar na kasa. Manajin Daraktan kuma babban jami’I na Kamfanin TCN Usman Mohammed a ranar Alhamis data gabata ya bayyana cewar, ya samu cin nasaar kular data kai 49.80 Hertz da kuma 50.20Hz na kashi 65 bisa dari daga ranar 29 ga watan Nuwamba zuwa yau. Wannan ya kuma kai daidai da irin ingancin kular da aka samar a fannin samar da wutar na kasar Ghana. Burin mu shine, mu kara zuwa wani mataki na gaba kuma munada yakinin kaiwa matakin na gaba. A yadda babban layin samar da wutar na kasa yake a yanzu, baida wata ma’adana kuma a haka muka riske shi kafin mu karmi ragamar. Amma a karo na farko, munyi kokari saosai wajen samar da ma’adanar kuma tuni muka turawa Hukumar NERC ma’adanar megawatts 260. Muna kuma sa ran Hukumar ta NERC zata amince da hakan a cikin ko wanne lokaci daga yanzu saboda munyi duk tuntubar data dace ta amincewar kuma in har Hukumar ta amince,komai zai daidaita. Ina kuma son in baku tabbacin ciyar, wannan gazawar ta babban layin sadarwar na kasa, zai zamo tarihi a kasar nan.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!