Connect with us

LABARAI

Mantu Ya Shawarci ‘Yan Siyasa A Kan Hanyoyin Bunkasa Dimokradiyya

Published

on

Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa ta kasa, Ibrahim Mantu, ya shawarci ‘yan siyasa a kan gyara halayya domin ci gaba da bunkasar dimokradiya.
Mantu, wanda yake memba na cikin kwamitin amintattu na jam’iyar PDP, ya bayyana hakan ne a yayin taron kaddamar da wani littafi kan ayukkan Atiku da aka yi wa take da “The Legacy of Atiku on Nation Building.”.
A cewar Mista Mantu, tsawon lokacin da aka dauka ana mulkin Dimokradiya ba tare da yankewa ba a Nijeriya, ya kamata ace abubuwa sun wuce inda suke a yau Nijeriya
To sai dai, abin takaici, har yanzu Nijeriya bata ginu a kan ginshikan Dimokradiya ba, haka suma jam’iyun siyasa, ba wani banbanci, inji shi.
Mista Mantu yashawarci ‘yan siyasa da cewa, ‘ina mai bawa abokaina ‘yan siyasa shawara, da mu canza salon yin abubuwa, tun da mun ga ba wata riba da ci gaba da suke kawowa Nijeriya.’
‘Nijeriya ba zata ci gab aba har sai mun canza halayenmu da kuma yanda muke yin abubuwa, tare da bin doka da saka tsoron Allah a cikin ayukkanmu,’ inji shi.
Ya ci gaba da cewa,’Ni a wurina, canza sheka zuwa wata sheka bai canza mutumin kirki zuwa na kwarai; ko mutumin banza zuwa na kirki. Wadanda ke tunanin za su tsarkaka idan sun canza sheka suna yaudarar kansu ne kawai da mutane, domin wannan bai canza su ba.’
Mista Mantu ya ce, abin da ake bukata ba canjin sheka ba; canjin hali da dabi’a ne. sannan, ‘yan siyasa su zama masu akida na zama wuri daya, wanda hakan zi basu gogewa nay au da kullum.
Da yake sharhi kan littafin, Mantu ya ce, abin a yaba ne a ce, wani daga jihar Delta ya rubuta littafi kan Atiku wanda yake daga Adamawa, hakan na nuni da samun sauyi a Nijeriya, inji shi.
Da yake bayani kan Litaffin, marubucin ya bayyana cewa, duba ga ayukkan Atiku ne dalilin da ya sanya shi rubuta littafin.
‘idan aka yi duba ga irin harkokin kasuwancin sat un yana yaro, kamar yanad ya ginawa mahaifiyarsa gida, za a fahimci cewa Atiku zai iya ci gabantar da Nijeriya,’ inji Mista Eke.
‘Wannan littafin, an yi sa ne domin nazarin ayukkan Atiku da manufofinsa na ci gabantar da Nijeriya.’
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!