Connect with us

LABARAI

Miyetti Allah Ta Kaddamar Da Gidauniyar Naira Miliyan 30 A Jihar Nasarawa

Published

on

Kungiyar Fulani ta Miyetti Allah ta kaddamar gidauniyar naira miliyan 30 domin sayen filin gina makaranta, azuzuwa da dakin kwanan dalibai na kungiyar.
Ciyaman din kungiyar na reshen jihar Nasarawa, Alhaji Muhammad Hussaini, ya bayyana cewa, za a gina makarantar ne a Sabon-Gida da ke karamar hukumar mulki ta Kokona da ke jihar.
‘Abin da aka san Fulani da shi sune kiyo da noma, wadannan abubuwan biyu har sun sa mun manta da sha’anin karatu, wanda yake kuma da gayar muhimmanci, inji Hussaini a wuribn taron gidauniyar.
A cewar sa, rashin karatu ne jigon matsalar fadace-fadacen da ake fama da su, kan haka suka ga dacewar samar da makaranta.
Alhaji Hussaini ya ce, ‘mun dade da fara aikin samar da makarantar, amman dai ba a cimma wata natija ba saboda matsalar kudi, muna rokon gwamnati da ta tallafa mana domin ida ginin makarantar.’
‘Da yawan ‘yayan mu basa makaranta, wannan ba abu ne mai dadi a wurin m u ba,’ inji shi. Ya kara da cewa, ‘Da yawan su sai dai yawon barace-barace a kan hanya, wanda hakan ke kara yawaitar rashin tarbiya da aikta miyagun halaye a cikin gari.
A cewar Alhaji Hussaini, ‘idan har zasu iya samun ingantaccen karatu, to za a iya samun fatan zaaman su wani abu nan gaba’
Alhaji Hussaini ya koka da irin yanda yara matasa da yawa suka tsunduma cikin harkar shaye-shaye, ya bayyana cewa, samar da makarantar zai rage ire-iren wadannan ayukkan a cikin matasan.
Da yake jawabi a wurin, Sakataren makarantar na kasa, Mista Retson Tedheke, cewa ya yi, rayuwar Fulani zata kara inganta idan har suka samu ilimi.
“Fulani mutane ne masu hazaka da amana. Zaka iya sanya Fulani kula da biliyoyin naira ba tare da ya sace wani abu ba. Hakan zai nuna maka irin kirki da kyakyyawar dabi’ar su,’ inji shi.
Ya ci gaba da cewa, ‘Matasan Fulani na bukatar ilimi, kuma wannan shi ne abin da muke son mu samar ta hanyar wannan aikin.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: