Connect with us

WASANNI

Mourinho Zai Fara Sharhin Wasanni A Kasar Rasha

Published

on

 

Tsohon kocin Manchester United wato Jose Mourinho zai yi sharhin wasannin kwallon kafa kan gasar cin kofin Zakarun Turai a Russia Today.

Wannan shi ne karo na biyu da zai yi aikin da gidan talabijin din Rasha, bayan wanda ya yi a lokacin gasar cin kofin duniya da kasar ta karbi bakunci a 2018.

Gidan talabijin din ya sanar da cewa Mourinho zai rika yi musu sharhin wasannin gasar cin kofin zakarun Turai da manyan batutuwan da suka shafi kwallon kafa a duniya.

Tsohon kocin na Manchester United zai fara sharhi kan wasannin gasar zakarun Turai (Champions League) da za a fara a ranar Talata da wadanda za a yi Laraba har zuwa karawar karshen gasar.

Mourinho ya kai United wasan zagaye na biyu a gasar zakarun Turai, daga baya ta sallame shi, bayan da ya kasa taka rawar gani ta kuma nada kocin rikon kwarya Ole Gunnar Solskjaer.

Tun bayan da Solskjaer ya karbi aiki a Old Trafford ya ja ragamar karawa 11, inda ya yi wasa 10 cas a jere.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!