Connect with us

SIYASA

Muna Yaba Wa Da Irin Jagoranci El-rufaI – Jarimi

Published

on

Shugaban Karamar hukumar Kaduna ta Kudu, Honarabul Yakubu Kabeer Jarimi, ya yi kira ga daukacin Al’ummar Jihar Kaduna, da su fito kwansu da kwarkwatarsu domin ganin su kara zaben Malam Nasiru Ahmad Elrufai a karo na biyu, domin ya ci gaba da dimbin Ayyukan alherin da ya dauko yima Al’ummar Jihar Kaduna.
Kabeer Jarumi, ya bayyana haka ne a yayin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa dake Kaduna. ya ce, Gwamnatin APC karkashin jagorancin Malam Nasiru Ahmed Elrufai, ta gama ma Al’ummar Jihar Kaduna komai, tun da ta samar masu da cikakken zaman lafiya mai daurewa a fadin Jihar baki daya.
Shugaban Karamar hukumar Kaduna ta kudu ya ce, Mutanan Jihar Kaduna sun shaida irin Namijin kokarin da Malam Nasiru El-Rufai ya yi game da shawo kan matsalar harkar rashin tsaro a Jihar fadin Jihar, wanda shi ne babban abin da gwamnan ya sanya a gaba babu dare ba rana, tun daga lokacin da Allah ya kawo shi kujerar Gwamnan Jihar Kaduna.
Jarumi ya kuma janyo hankalin masu zabe da kar su yarda su hau Dokin danasani domin babu wani abun azo-a-gani da wata Jam’iyar adawa zata iya kawo masu, wanda a tsawon shekaru goma 16, da sukayi suna mulkin Jihar Kaduna, wanda basu samar masu ba, sai a yanzu. Sannan ya kara da tabbatar ma Mutanen Jihar Kaduna alkawarin karin ayyukan ci gaba idan Allah ya sake dawo da jam’iyyar mulkin kaduna a zango karo na biyu.
Shugaban Karamar hukumar Kaduna ta kudu, ya ci gaba da bayyana cewa, “ Gwamna Malam Nasiru Ahmed Elrufai, shi ne gwamna na farko a tarihin Jihar Kaduna, wanda ya taba baiwa kananan hukukomi ‘yan cin kansu, ba tare da ya yi masu wani katsalanda a harkokin kananan hukumominsu ba. Gaskiya wannan ba karamin abin a yaba masa ba ne, kuma da izinin Allah zamu tabbatar mun kada masa gaba daya kuri’unmu, domin ganin ya kammala irin ayyukan alherin da ya dauko yima Al’ummar Jihar Kaduna.”
Honarabul Jarumi ya kara da bayyana cewa, a cikin ‘Dan kankanin lokacin da Allah ya basu shugabancin Karamar hukumar Kaduna ta kudu, sun fara samar da abubuwan more rayuwa ga Al’ummar yankin, wandanda suka hada da, samar da motocin sintiri domin samar da ingantaccen tsaro ga Al’ummar yankin. Samar da Tiransfoma na lantarki, domin wadata Al’ummar yankin da wutan lantarki, biyan bashin hakkokin ma’aikata da suka dade suna bin gwamnatin baya, tsawon shekara da shekaru, sun samarwa Daliban yankin da litattafan karatu, domin inganta harkokin iliminsu.
Honarabul Yakubu Kabir Jarimi, ya siffanta Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmed Elrufai, a matsayin jagoran Gwamnonin Nijeriya, domin tuni gwamnan ya yi ma sauran takwarorinsa gwamnonin zarra a Ayyukan ci gaban Al’umma, samar da ayyukan yi, inganta ilimi, gina sabbin Makarantun, inganta harkokin Noma, da dai sauransu.
Honarabul Yakubu Kabir Jarumi, ya kuma yabama Tsohon Mai Baiwa Gwamnan Jihar Kaduna shawara akan harkokin siyasa, kuma Dan takarar Sanatan Kaduna ta Tsakiya a inuwar Jam’iyyar APC, Malam Uba Sani, da irin kaunar da yake nuna ma Al’ummar Karamar hukumar Kaduna ta kudu, a cewarsa, tabbas Uba Sani, alheri ne ga Al’ummar Kaduna ta Tsakiya, domin Mutum ne mai fada da cikawa.
Ya kara da cewa, da yardar Allah zasu tabbatar da cewa, ranar zabe sun fito kwansu da kwarkwatansu domin ganin sun kada masa gaba daya kuri’unsu idan Allah ya kaimu ranar zabe, domin ganin ya lashe kujerar Sanatan Kaduna ta Tsakiya domin zuwa majalsar Dattawa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: