Connect with us

LABARAI

Rundunar Sojojin Nijeriya Ta Gargadi Masu Shirin Zagon Kasa

Published

on

A ranar Lahadi ne rundunar sojojin Nijeriya ta gargadi duk masu shirin yi zagon kasa da su nisanci fadawa cikin lamarin shugabancin siyasa. Wannan bayani ya fito ne daga bakin mukaddashin darakta Kanal Aliyu Yusuf, a kan lamarin siyasa za mu ci gaba gudanar da aikinmu yadda doka ta tanada. Yusuf ya maida martani ne a kan zargin da tsohon jigo jam’iyyar APC, Timi Frank ya yi a wani sashin jarida wanda aka wallafa.
Ya ce, a cikin zargin da Frank ya yi wanda aka wallafa ya bayyana cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma shugaban hukumar zabe mai zaman kanta sun yi wani ganawar sirri tare da shugaban rundunar sojojin Nijeriya Lt. Janaral Tukur Burutai da niyyar yin magudin zaben shugaban kasa na ranar Asabar. Ko da yake ya bayyana cewa, rundunar sojojin sun kai rahoton kalamun Timi Franka ga rundunar ‘yan sandar Nijeriya, inda suka bukaci a cafke shi nan take tare da gurfanar da shi a gaban kuliya sakamakon bayar da labarin karya ga shugaban rundunar sojojin. Yusuf ya danganta Frank a matsayin mutumin banza wanda yake kokarin cutar da Burutai a lokuta da dama.
‘Timi Frank ya zama makaryaci tun da ya kasa kawo shaida a kan wannan zargi na ganawar sirrin. ‘Domin haka, muna fadakar wa mutane musammam ire-iren su Mista Timi Frank cewa, shugaban kasa shi ne kwamandar rundunar tsaro yana da damar yin taro ga dukkan rundunonin tsaro a kowani lokaci, bal ma wannan taro ba a ma yi shi ba,” in ji Yusuf.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!