Connect with us

LABARAI

Shugaba Buhari Ya Bunkasa Rayuwar ‘Yan Nijeriya A Cikin Shekara Hudu, Inji Dakta Mahmud

Published

on

An bayyana cewa, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi gaggarumin kokari a wajen bunkasa kusan dukkan bangarorin rayuwar jama’ar Nijeriya a cikin shekara hudu da ya yi yana mulkin kasar nan, a kan haka ya kamata dukkan ‘yan Nijeriya su fito don sake zabarsa a karo na biyu don ya ci gaba da gudanar da ayyukan bunkasa dukkan fannoni rayuwar jama’a, Shugaban Kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa (Buhari Sopport Organization), Dakta Mahmud Muhammed Abubakar, ya bayyana haka a tattaunawarsa da manema labarai jiya a babban ofishin kungiyar dake uguwan Utako Abuja.
Dakta Mahmoud wanda kuma shi ne babban Darakta na kungiyoyin yakin nemann zaben shugaba Buhari a Nijeriya yana kuma rike da mukamin shugaba a bangaren kungiyar da matar shugaban kasa Aisha Buhari ta kafa don yakin neman zaben shugaba Buhari, ya kuma bayyana cewa, a ganin yadda gwamnatin APC a karkashin shugabancin Muhammadu Buhari ta karbi ragamar shugabancin kasar nan da kuma irin barnar da jam’iyyar PDP ta yi wa ginshikin tattalin arzikin kasar nan dole a yaba da irin ci gaba da aka samu a cikin wannnan dan karamin lokacin, ‘Jami’iyyar PDP ta kawoi matsala a kusan dukkan bangarorin tafiyar da rayuwar jama’a, a kan haka ne kuma shugaba Buhari ya taba kusan dukkan bangarorin rayuwar al’ummar kasar nan baki daya’ ini shi.
Ya kuma kara da cewa, in har ana bukatar ci gaba da irin ayyukan alhairin da shugaba Buhari ya faro a zangon mulkinsa na faro, to dole a ba shugaban kasa wa’adin mulki a karo na biyu don a a tabbatar da dorewar ayyukan da aka gudanar.
Daga nan kuma Dakta Mahmuod ya yi kira ga al’umma Nijeriya musamman masu jefa kuri’a su tabbatar da sun fito a ranar Asabar 16 ga watan Fabrairu 2019 sake jefa wa shugaba Buhari kuri’ar da za ta tabbatar masa ci gaba da shugabanci a karo na biyu, ‘Ya kamata mu fito a cikin tsari ba tare da tashin hankali ba, mu kada kuri’armu tare da kuma tsarewa da kuma raka ta har a bayyana sakamakon zaben” inji shi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!