Connect with us

LABARAI

Shugaba Buhari Ya Sha Alwashin Warware Rikicin APC A Jihar Zamfara

Published

on

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyaba fatansa na warware rikicin jam’iyyar APC, na jihar Zamfara a babban zabe mai zuwa cikin lokaci kadan. Shugaban kasar ya yi wannan furici ne a garin Gusau, lokacin gangamin yakin neman zabe a jihar ranar Lahadi. ‘A matsayina na shugaban wannan kasa wanda na yi rantsuwa kuma na yake girmama tsarin shari’a, zan ci gaba da yin hakan domin a samu gudanar da abubuwa yadda ya kamata. ‘Jam’iyyarmu ta yanke shawara ko dai ta yi zaben fidda gwani kai tsaye ko kuma ta yi ‘yar tinke a jiha guda takwas, amma sai aka samu matsaloli cikin har da jihar Zamfara.
‘Duk da haka dai, tun da lamarin yana gaban kotu a halin yanzu, ina fata tare da addu’a kafin ranar Asabar mai zuwa, kotu za ta yanke hukunci a kan lamarin, domin ‘yan takaran jam’iyyunmu su samu damar shiga cikin kowani zabuka,” in ji shi.
Shugaban kasar bai mika tutar jam’iyyar ba ga ‘yan takarar a jihar lokacin gangamin yakin neman zaben, domin girmama doka da oda. Ya tuna da alkawarin da ya yi wa ‘yan Nijeriya a gangamin yakin neman zaben shekarar 2015, na samar da tsaro da bunkasa tattalin arziki da kuma yakar cin hanci da rashawa, inda ya ce, duk kudin da aka amso na cin hanci da rashawa za a yi amfani da su wajen samar da kayayyakin more yaruwa.
Lokacin da yake yawo hankalin mutane su fito kwansu da kwarkwatansu wajen zaben ‘yan takaran jam’iyyar a zabe mai zuwa, shugaban kasar ya yi kira ga mutane da su bi doka da oda lokacin gudanar da zaben.
Tun da farko dai, gwamna Alhaji Abdulaziz Yari ya bayyana wa magoya bayan jam’iyyar a jihar a kan lamarin cewa, ya kamata hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta mutunta hukuncin kotu ta bar ‘yan takarar jam’iyyar su shiga cikin zaben. Yari ya godewa shugaban kasa a kan wannan ziyara tare da tabbatar masa cewa, jam’iyyar za ta samu nasara ga kowani kujera a zaben.
A bayaninsa, shugaban jam’iyyar APC Adams Oshiomhole ya yi kira ga shuwagabannin jam’iyyar da ‘ya’yan jam’iyyar da kuma magoya bayan jam’iyyar da su bi doka da oda, domi ya tabbatar da cewa jam’iyyar za ta lashe dukkan zabukan mai zuwa.
Kamfanin dillanci labarai na kasa ta ruwaito cewa, gangamin yakin neman zaben shugaban ya hada har da ministan tsaro Mansur Dan Ali da ministan harkokin cikin gida Abdulrahman Dambazau tare da gwamnonin jihar Zamfara, Borno da Sakkwato, Alhaji Ahmed Yarima, Alhaji Ali Modu and Aliyu Wammako da dai sauran su.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: