Connect with us

LABARAI

Turmutsitsin Zabe; Shugaba Buhari Ya Mika Ta’aziyya Ga Gwamnatin Jihar Taraba

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tura wakilai domin su mika ta’aziyya ga gwamnatin jihar Taraba da kuma iyalan wadanda suka rasa rayukansu a turmutsitsin gangamin taron yakin neman zaben jam’iyyar APC, wanda ya gudana ranar Alhamis a garin Jalingo. Sakataran gwamnatin tarayya Mista Boss Mustapha wanda ya shagoranci wakilan shugaban kasar, shi ya bayyana haka a garin Jalingo ranar Lahadi, inda ya bayyana cewa shugaban kasa Buhari ya damu matuka da wannan lamari. Sakataran gwamnatin ya kuma jagoranci wakilan wajen ziyarar mutum hudu wadanda suka samu raunika, a asibitin tarayya da ke jalingo, ya kuma yi wa sarkin Muri Alhaji Abbas Tafida da gwamnan Darius Ishaku ta’azziya.
Mustapha ya bayyana cewa, shugaban kasa ya danganta mutuwar mutum bakwas lokacin taron gangamin yakin neman zabe a matsayin sadaukar da kai domin dimokaradayya, ya tabbatar wa masu zaman makoki cewa ‘yan uwansu ba su mutu a banza ba. A cewar sa, shagaban kasa ya yi wa wadanda suka mutu addu’an Allah ya jikansu, ya kuma bai wa iyalan su hakurin wannan rashi.
Da yake amsa ta’aziyar a madadin iyalan mamatan, shugaban kananan hukumomi Alhaji Haruna Kawuwa, wanda ya rasa matarsa, ya godewa shugaban kasa game da nuna soyayya tare da damu ga ‘yan uwan mamatan. Kawuwa ya tabbatar wa shugaban kasa cewa za su ci gaba da goyan bayansa tare da yin biyayya da manufofinsa, ina wa wakilan addu’a Allah ya kai su gida lafiya.
Kamfanin dillancin labarai ta kasa ta ruwaito cewa, a cikin wadannan wakilai har da ministan Abuja Mohammed Bello, gwamnan Adamawa Mohammed Bindow. Sauran wakilan sun hada da daraktan bunkasa fasahar ci gaban zamani Dakta Ali Pantami, mai Magana da yawun shugaban kasa Mista Femi Adesina, Sanata Ali Ndume da dai sauran su.
Wadanda suka rasa rayukansu wajen gangamin yakin neman zaben shugaban kasar sun hada da Alhaji Gudali Buba, Ardo Barkere, Alhaji Musa Namuddi da kuma Sukaina Hassan. Sauran sun hada da Amina Yahya, Zainab Yahya, Safiya Haruna Kawuwa da kuma Ummul Al-Hassan.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: