Connect with us

LABARAI

Wani Matashi Ya Yi Alkawarin Kashe Kansa Idan Buhari Ya Fadi Zabe

Published

on

Wani matashi dake ikirarin zama dan a-mutun shugaban kasar Najeriya kuma dan takarar tazarce a jam’iyya mai mulki ta All Progressibes Congress (APC) watau Shugaba Muhammadu Buhari mai suna Adamu Kabir Matazu yayi barazanar kashe kan sa idan Buharin ya fadi zabe.
Matashin wanda ya rubuta sakon na sa a shafin sa na sadar da zumuntar zamani na facebook ya bayyana cewa: “Idan dai har shugaba Buhari ya fadi zaben da za’a gudanar a ranar 16 ga watan Fabreru to zan kashe kaina kafin ranar 29 ga watan Mayu.”
Ya kara da cewa shi zai kashe kan sa ne domin kuwa ba zai iya jure ganin an rantsar da Atiku ba a matsayin shugaban kasar Najeriya bayan ya kada Buhari.
Tuni dai maganar ta kisan kan nasa da ya wallafa a shafin sa ta ja hankalin al’uma tare da haifar da zazzafar muhawara a tsakanin masoyan bangarorin ‘yan siyasar biyu watau Buhari da Atiku.
Wasu dai na ganin bai aikata wani laifi ba kuma tsabar soyayya ce yayin da wasu kuma ke ganin tsabar rashin hankali ne da tunani.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: