Connect with us

MANYAN LABARAI

Wuta Ta Kone  Na’urar Zabe Kurmus A Ofishin INEC Na Anambara

Published

on

Kasa da kwanaki biyar zuwa ranar da za a gudanar da zabukkan shugaban kasa da na ‘yan majalisar dattawa, wata ta tashi a ofishin hukumar INEC na jihar Anambara a yau Talata, wutar ta kone wasu kwantainoni biyu da suke shake da na’urar zabe kurmus.

Zuwa lokacin hada wannan rahoton, jami’an kasha gobara na jihar Anambara suna ta kokarin ganin sun kasha wutar, jami’an tsaro da suka hada da ‘yan sanda, jami’an tsaron farin kaya na DSS da sauransu sun yi wa wajen da gobarar ta tashi kawanya, saboda gudun afkuwar wani al’amari na daban, musamman da yake a ofishin hukumar zabe ne.

A daidai lokacin da yake tabbatar da afkuwar lamarin, shugaban hukumar INEC na jihar Anambaran ya ce; zuwa yanzu hukumar  ba za ta iya tabbatar da asarar da wutar ta jawo ba, saboda har yanzu ba a samu nasarar kashe wutar ba, amma dai tabbas na’urar zabe da takai yawan kwantaina biyu ta kone kurmus.

‘Ban san mai ya jawo gobarar ba, amma dai nasan wuta ta tashi a kwantainoni biyu da muka ajiye na’urar zabe, zuwa yanzu bamu san asarar da aka yi ba, amma dukkan na’urar zaben ta kone kurmus, kuma anan muka saba adana dukkan kayan zabe masu muhimmanci tun daga shekarar 2011, don haka ba wani bakon abu bane ajiye kaya a cikin kwatainar.’ Inji shugaban hukumar
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: