Connect with us

TATTAUNAWA

Za Mu Ci Gaba Da Yi Wa Kasa Addu’ar Samun Nasarar Gudanar Da Zabe, inji Goni Hassan Minna

Published

on

GONI SHEIKH HASSAN MUSAN MINNA, Shi ne Shugaban Majalisar Mahaddata Alkur’ani Ta Kasa Mai Shugabanci a Jihohi 27 Na Najeriya, Gogagge, Mutafannidi sannan kuma mai kishin ganin an kawar da matslar barace barace da sauran abubuwan da ake jingina su da amajirci, A tattaunawarsa da Wakilinmu a Kano ABDULLAHI MUHAMMAD SHEKA, Sheikh Hassan Musa Minna Ya bayya na sararar da majalisar da yake shugabanta ta samu cikin shekara guda, musamman batun taron kasa da aka gudanar a Jihar Sokoto da kuma taron da ya tattara mahaddata alkur’ani 1,111 wanda aka gudanar da addu’o’in fatan samun nasarar gudanar da zaben shekara ta 2019 lafiya, Shugaban ya kuma bayyana shiri majalisar na taimakawa Gwamnati wajen yakar matsalar barace barace da kuma tsarin gudanar da kididdigar yawan tsangayu da kuma almajiran c

Da farko Goni ba boyayye bane wajen yin fashin baki kan abubuwan da suka shafi harkokin tsangayu, shin ko wane hali ake ciki bisa shirin majalisar na samar da kididdigar da majalisar ta tsara gudanarwa?
Alhamdulillahi muna karea yi wa Alla godiya da ya nuna mana wannan lokaci cikin koshin lafiya, sannan kuma ya zama dole mu kara jadadda godiyarmu ga mai alfarma srkin Musulmi Dakta Muhammada Sa’ad Abubakar wanda ako da yaushe yake bayar da dukkan gudunmawar da wannan majalisa ta nema domin kawo karshen matsalolin da suka jima suna addabar wannan tsari na harkokin tsangayu. Kamar yadda aka sani a lokacin taron da ya gudana a Jihar Sokoto Mai Alfarma Sarkin Musulmi Dakta Muhammad Sa’ad Abubukar ya bukaci wannan majalisar ta samar da kididdigar yawan tsangayu da al’amajiran cikinta, kuma alhamdulillahi bayan kammala wancan taro abinda muka mai da hankali akai kenan.
Da farko muna ta kokarin tabbatar da cikakken shugabanci a matakan jihohi domin ganin an fara gudanar da wannan babban aiki, wannan tasa bayan taron da ya gudana a Jihar Sokoto ina kara godiyawa sakataren Kwamitin Amintattun wannan majalisa kuma Sakatare Janar na Kasa wanda ya ke aiki ba dare ba rana wajen tabbatar da hadin kan wannan tafiya. Yanzu haka mun kusa kammala wannan aiki wanda muke fatan gabatarwa da Mai Alfarma shi domin sa albarka. Jihohi suna nan suna aiki gwargwadon iko domin ganin kowacce jiha ta kawo nata jerin sunayen tsangayun da kuma almajiran mu.
Ganin yadda wannan Majalisa ke tun karar gudanar da taruka na kasa wanda abaya ba’a saba ganin irin su ba, shin ko me wannan majalisa ta kudurce wanda ta ke fatan isarwa da sauran ‘yan uwa sakonsa?
Alhamdulillahi kamar yadda aka sani Alkur’ani ne ya fara sanar da mu muhimmancin zumunci da hadin kai, sannan kuma a kullum ina fada sakamakon irin rikon sakainar kashin da aka yiwa wannan tsari a baya yasa alarammomi suka ja da baya suka kuma zuba ido suna kallon yadda abubuwa ke gudana ba tare da sa baki aciki ba tun da ba’a shigo dasu ba. Amma muna kara godiya ga Allah da ya bamu Amirul Mumumina na wannan lokaci Al-Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar wanda shi ne ya fara waiwayar alarammomi kuma ya jawo su jikinsa tare da basu dukkan damar da ta kamata wadda ahalin ayanzu ‘yan uwa suka gamsu ana damawa dasu ta hanyar neman shawarwarinsu acikin abubuwan da suka shafi harkokin tsangayu,ba kamar abaya bad a ake amfani da alarammomi ofis da na mota wajen wakiltar alarammomi masu tsangayau na hakika.
Saboda haka ganin wannan hobbasa na mai alfarma ya sa wannan Majalisa shiga cikin wanna aiki ka’in da na’in, wanda muke a haduwa a wuri guda domin gabatar da jawabai tare da wayar da kan ‘yan uwa kan irin cigaban da duniya ta yi. Wannan ya taimaka kwarai idan aka dubi yadda alarammomi suka karbi harkar allurar rigakafi da sauran alluran rigakafin cutuka masu kashe kananan yara da mata alokacin nakuda. Yanzu kuma gashi har mun kai ga shirya taruka a matakin kasa tare da gudanar da taron addu’a wadda aka gudanar cikin kwanakin da suka gabata inda aka gudanar da saukokin Alkur’an har 1,111 domin fatan Allah ya sa ayi zabe Lafiya a gama lafiya.

Goni Ya kake kallon amsa kiran da ‘yan uwa suke aduk lokacin da kuka bada irin wannan umarni duk da kuna dukan jikin ku ne da danyen kara?
Wannan sunna ce ta rayuwa kuma duk wanda ke fatan bayar da tasa gudunmawar ga cigaban kasar sa dole sai ya yi bakin kokarinsa kafin sauran bangarorin su shigo domin tallafa ma sa, alhamadulilahi ba abinda zamu cewa ‘yan uwa sai godiya domin sun nuna mana suna da tarbiyar zumunci kamar da yadda muka taso acikinta, duk wanda ya yi harkar karatun tsangaya zaka same shi mai zumunci da girmama juna.
Bawai taron kasa ba kawai aduk lokacin da wani abun alhairi ko akasin haka ya samu wasu ‘yan uwa idan aka tsara zuwa taya murna ko jajantawa zaka tarar ‘yan uwa har doki suke wajen ganin sun halarci irin wannan wuri, don haka mu a bangaren shugabanci ba abinda zamu ce da ‘yan uwa sia godiya.

Yanzu haka ganin zabe ‘yan kwanaki kadan suka rage agudanar da wannan zabe na kasa, shin ganin kun gudanar da wancan taro, shi kenan yanzu ranar zabe ake jira ?
‘Yan Jarida kenan ina son tuna maka cewa mu alarammomi kullum cikin addu’a muke kamar yadda aka sani muna gudanar da karance karance sau uku akowacce rana, don haka yanzu nema muka kara himmatuwa tare da raba addu’o’i da ake a daukacin tsangayunmu domin fatan Allah ya zaba mana shugabannin na gari maus kishin al’umma, sannan kuma muna kara gudanar da addu’o’i daban daban domin rokon Allah ya kawo mana karshen matsalolin da ke addabar wasu sassan kasar nan musamman Jihohin Zamfara, Sokoto, Katsina, Kaduna da Maiduguri, wannan ko shakka babu muna kan aikinsa muna kuma kyautatawa Allah zaton zai amsa addu’armu.

Kenan idan mun fahimci Goni Majalisar ba kawai sai an hadu wuri guda kuke gudanar da wannan kyakkyawar hidima ga kasa ba?
Ina tabbatar maka da cewa mu kullum aikin da muke kenan domin kullum Alkur’ani a hannu yake muna ta karanta shi kuma Allah ya yi alkawarin masu yiwa alkur’ani irin hidima suna da babban rabo, don haka mu ke tawassili da wannan littafi mai tsarki domin Allah ya ta babbatar mana da nasara a zabukan dake gabatowa tare da dawo mana da cikakken zaman lafiya akasar nan baki daya.
Za mu so ka yiwa jama’a karin haske kan ayyukan wannan Majalisa musamman ganin yanzu ne aka fara jin duriyar irin wannan babban al’amari na hadin kan Mahaddata Alkur’ani?
Babban abinda muka fi mayar da hankali yanzu shi ne yiwa kasa addu’a sannan kuma muna kara nunawa ‘yan uwa muhimmacin karbar sauye sauyen da zamani ya zo dashi, musamman shirin nan na kawar da barace barace, muhimmanci tsaftar muhallin almajirai, cin abinci mai gina jiki, karbar alluran rigakafi aduk lokacin da hukumomi suka bukaci hakan, sai kuma tabbatar da samar da ingantacciyar kididdigar yawan tsangayunmu da kuma almajiranmu, wannan zai taimaka wajen sanin shige da ficen almajiranmu, da kuma damar samun tallafin hukumomi da kungiyoyi daban daban..

Mene Sakon ka na karshe?

Gaskiya babban sakon na farko shi ne ina kara kira ga ‘yan wa su ci gaba da baiwa wanna Majalisa hadin kan da ake bukata domin ganin mun tafi tare, haka kuma kamar yadda aka sani yanzu lokaci ya yi da ya kamata ‘yan uwa mu fara gwada karbar wasu daga cikin shawarwarin da gwamnatoci ke bayarwa, wannan ya hada da batun samar da ilimin zamani domin hakan zai taimaka wajen samun ayyukanyi amatakin gwamnati dakamfanoni, sai kuma tabbatar da tsaftar makarnatun mu na allo aduk inda suke, ko wane alaramma ya tabbatar da yasan yawan almajiran dake karkashin kulawarsa domin kaucewa shigar gurbatattu cikin almajiran mu domin bata mana suna.
Haka kuma ina kara godiya ga ‘yan uwa shugabannin wannan Majalisa tun daga matakin mazabu har kaina wanda nake zaman shugaban wannan majalisa mai albarka bisa irin jajircewar da ake aduk lokacin da aka bukaci fitowar ‘yan uwa domin yin wata hidima ta kasa, wannan abune mai kyau kuma yana tarin albarka , ina kuma tabbatarwa da ‘yan uwa zamu ci gaba kare duk wata kima da kuma martabar tsarin karatun mu natsangayu, wannan kuma ya hada da sauraron gwamnati domin duba abubuwan da ta ke fatan aiwatarwa wannan tsari namu mai abarka.

Mun gode

Nima na Gode

ikin tsnagayun. Ga dai yadda tattunawar ta kasance;
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!