Connect with us

WASANNI

Za’a Iya Korata A Chelsea – Sarri

Published

on

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Maurizio Sarri ya ce, aikinsa na horarwa na fuskantar barazana bayan lallasar da suka sha a hannun kungiyar Manchester City da ci 6-0 a gasar firimiyar Ingila.
A karon farko kenan tun shekarar 1991 da Chelsea ke shan mummunan kashi irin wannan a hannun wata kungiya a gasar firmiyar Ingila, in da a wancan lokaci, Nottingham Forest ta yi ma ta dukan- kawo-wuka da ci 7-0.
Sarri da kaftin din Chelsea, Cesar Azpilicueta sun bai wa magoya bayan kungiyar hakuri kan lallasar da suka sha a hannun Manchester City a filin wasa na Etihad, abin da ya rikito da kungiyar zuwa mataki na 6 a teburin gasar.
“Ban taba Magana da shugaban kungiyar nan ba tun lokacin da nafara aiki saboda haka ban san menene yake faruwa ba tabbas dai banji dadin irin wannan rashin nasara ba mai muni” in ji Mauricio Sarri, dan kasar Italiya
Yaci gaba da cewa “Za’a iya korata tunda ba kungiya tab ace kuma kamar yadda kowa yasani idan kungiya bata kokari mai koyarwa ake fara dorawa laifin kuma idan za’a dauki wani mataki akansa ake fara dauka”
Sargio Aguero ya sake taka muhimmiyar rawa a fafawar ta ranar Lahadi, in da ya jefa kwallaye uku shi kadai, yayin da Manchester City ta sake komawa saman teburin gasar da maki 65, in da saka karbe ragama daga hannun Liberpool.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: