Connect with us

MANYAN LABARAI

Zabe: ‘Yan Sanda Sun Kara Tsaro A Ofisoshin INEC

Published

on

Mukaddashin babban Sufeton ‘Yan sanda na kasa, Mohammed Adamu, ya bayar da umurnin a tsaurara tsaro a duk ofisoshin hukumar zabe da ke duk sassan kasar nan.
Kakakin rundunar, Frank Mba, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Lahadi.
Ya ce, duk Kwamishinonin ‘Yan sanda na Jihohi 36 da Abuja, an umurce su da su samar da cikakken tsaro a duk ofisoshin hukumar zaben da kuma kayayyakin zabe na hukumar daga cutarwan kowa, kafin, a lokacin da kuma bayan zaben.
Wannan umurnin ya zo ne awanni kadan da hukumar zaben ta kai rahoto ga babban sufeton na gobara biyu da aka yi a ofisoshin hukumar da ke Abiya da Jihar Filato.
Sanarwar ta Mista Mba ta ce, mataimakin babban sufeton ‘yan sanda na kasa na wannan shiyyan an dora masu nauyin dubawa da tabbatar da tsaron a duk yankunan su.
“Babban sufeton ‘yan sanda yana tabbatar wa da ‘yan Nijeriya rundunar ‘Yan sanda a shirye take da ta sauke nauyin aikin da ke kanta na samar da tsaron da ya kamata a babban zaben da ke tafe,” in ji Mista Mba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: