Connect with us

SIYASA

Zuwan Atiku Abubakar Kano Ya Sa Cikin Wasu Ya Duri Ruwa – Musa Falaki

Published

on

Ranar Asabar washe garin zuwan Dan Takarar Shugabancin Najeriya Karkashin Tutar Jam’iyyr PDP Alhaji Atiku Abubakar Wazirin Adamawa, Kungiyar Muryar Malaman Tafiyar Atiku Abubakar Na Arewacin Najeriya (Atiku Abubakar Ulama’u Forum For Northern Nageria) ta shirya taron
addu’a inda aka tara sama da malamai dari 500 wadanda suka taru a masallachin Sheikh Ahmadu Tijjani dake Kofar Mata a Kano, inda aka gudanar da saukokin alkur’ani mai Girma tare da gabatar da addu’o’i domin samun nasarar zuwan Atiku Abubakar Kano lafiya da kuma addu’ar fatan Allah ya bashi Nasara a zaben dake gabatowa.
Malam Musa Falaki Tsakuwa shi ne shugaban Kungiyar Muryar Malaman Tafiyar Atiku Abubakar na Arewacin Najeriya, Jaridar Leadershipa yau ta samu zantawa dashi jin kadan da kammala addu’ar inda ya bayyana cewa sun shirya wannan gagarumar addu’a ne kamar yadda wannan kungiya ta saba domin fatan Allah ya tabbatar da nasarar ziyarar Atiku Kano, sannan kuma tawagar Malaman sunyi rruwan addu’o’i ga ‘yan Takarkarun Jam’iyyar PDP a matakin Kasa da kuma Jihohi domin neman tabarukin Allah wajen samun nasarar Jam’iyyar PDP a Kasa baki daya.
Malam Musa Falaki Tsangakuwa ya ci gaba da cewa Allah ya bayyana gaskiya kowa ya ganta zuwan Atiku Abubakar kuma cikin Jam’iyyar APC ya duri ruwa domin Jama’a sunga irin dandazon jama’ar da suka fito domin tarar Atiku Abubakar, yace saboda yawan al’umma ko wurin da Atiku da mai masaukin sa Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso zasu sauka domin isa wurin munbari taron basu samu ba sai acikin mota aka kai masau amsa kuwwa suka gabatar da jawabansu. Ya ci gada cewa tunda ake taron siyasa a wannan karnin ba’a taba ganin taron da ya tara dan Adam Kamar wanda ya gudana alokacin zuwan Atiku Abuakar Kano na Ranar lahadin data gabata ba.
Yace wannan ya haskawa Jam’iyyar PDP cewa kowa ya kwantar da hankali Al’ummar Najeriya sun gaji da mulkin Tsintsiya, wanda yace ba abinda ta kawo kasar nan sai yunwa da matsanancin talauci, Saboda haka Malam Musa Falaki sai ya yiwa Dan Takarar Gwamnan Kano a karkashin tutar
Jam’iyyar PDP Abba Kabir Yusif Bushara da cewar da yardar Allah nan da ‘yan kwanaki Allah zai cika mana burin mu ka zama Gwamnan Kano, domin kowa ya shaida irin ayyukan alhairin da uban gidanmu Injiniyar Rabiu Musa Kwankwaso ya shinfidawa Kano da Kanawa.
Da yake tsokaci kan yamadidin da Jam’iyya mai mulki ke yi wai hayar Jama’a aka dauko tun daga Kamaru da Nijar, Falaki cewa ya yi daman ita tabarmar kunya daman hauka ake nadeta, wanda duk ya ga zuwan Buhari Kano ya ga Sarakuna biyu daga Kasar Nijar da tawagarsu da aka gayyato domin wai su dan Karawa taron armashi, kuma kamar yadda dan Hausa ke cewa ido ba mudu ya san kima, Kanawa sun san Kwankwaso haka Allah ya yi masa farin jinin al’umma duk inda ya kira dole a amsa, mu ba abinda za mu cewa Kanawa godiy domin sun cika alkawari da kuma amsa kirarin nan na su Kano ko da me ka zo an fika. Kuma zuwan Wazirin Adamawa Kano a sa cikin wasu ya duri ruwa domin an yi walkiya kowa ya gansu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!