Connect with us

MANYAN LABARAI

Dage Zabe: Ka Da Mu Karaya Akwai Fata –Saraki Ga Al’ummar Nijeriya  

Published

on

Shugaban majalisar dattawan Nijeriya, kuma jigo a jam’iyyar adawa ta PDP, Dakta Bukola Saraki, ya saki wani sakon karfafa gwiwa ga al’ummar Nijeriya yau Asabar, bayan da hukumar zabe mai zaman kan ta ta dage zabukkan da za a fara gudanarwa a yau Asabar.

Sarakin ya bukaci al’ummar Nijeriya da cewa kada su karaya, su tabbatar da sun fito a mako mai zuwa sun kada kuri’unsu, duk da a cewarshi babu dadi dage zaben, amma akwai fata, muddin al’ummar Nijeriya ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen kada kuri’a a mako mai zuwa.

‘Lallai akwai matukar bakin ciki yadda aka dage zabe, ‘yan sa’o’i kadan kafin a fara gudanar da zaben, bayan kusan dukkan al’ummar Nijeriya ta gama shirinta tsaf don gudanar da zaben, amma abun mamaki sai ‘yan Nijeriya suka samu sako dage zaben, wand aba karamin girgiza su ya yi ba, Allah kadai ya san irin wahalar da al’ummar Nijeriya suka fuskanta sakamakon dage wannan zaben.’ Inji Saraki

Saraki Ya kara da cewa: Na yi matukar tausaya ma ma’aikatan gwamnati da suka tafi garuruwansu don su yi zabe, da ma sauran ‘yan kasuwar Nijeriya da suka bar harkokin kasuwancinsu don su je su kada kuri’a, kamar yadda na ce a baya, Allah kadai ya san asarar da mutane suka tafka sakamakon dage zaben nan da aka yi.

‘Muna sa ran al’umma zasu dage su jajirci su sake fitowa mako mai zuwa don su kada kuri’unsu, sannan muna rokon hukumar zaben da ma gwamnatin tarayya da su tabbatar da sun yi maganin duk wani abu da zai iya kawo cikas ga zaben nan gaba, saboda ba karamin illar wani tsaiko zai sake haifarwa bag a al’ummar Nijeriya.’ Inji Saraki
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!