Connect with us

RA'AYINMU

Batun Masu Sanya Ido Na Waje Da Zaben 2019

Published

on

Sakamakon dage zaben Shugaban kasa da na ‘Yan Majalisar Tarayya da aka yi a makon da ya gabata, Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ta tantance masu sanya ido na cikin gida da waje kimanin 144.
Dari da sha shida a matsayin masu sanya ido na cikin gida, da ya hada da gwamnati, kungiyoyi masu zaman kansu, Shugabannin addini, kungiyoyin Afrika, Jakadun kasashen waje, Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Yammacin Afrika (ECOWAS) da sauran kungiyoyi daban-daban. Kazalika, masu sanya ido na kasashen wajen sun bayyana gamsuwarsu sakamakon binciken da suka yi na kokarin Gwmanatin Tarayya wajen baiwa ‘Yan kasa damar zaben wadanda za su mulke su a zaben da za a fara fafatawa gobe idan Allah Ya kai mu a fadin wannan kasa baki daya.
Wannan ne ke tabbatar da cewa, ko shakka babu akwai kalubale babba a gaban Nijeriya, don kuwa ko babu komai idon duniya kacokan na kanta don ganin yadda za ta aiwatar da wadannan zabubbuka da aka sanya gaba. Tabbatar da adalci da kuma bayyana sakamakon zabe na gaskiya ne kadai zai iya baiwa wannan demokradiyya tamu damar ci gaba da wanzuwa, tare da sake samun kima da mutunci a idon duniya baki daya.
Har ila yau, muna sake jan hankalin Hukumar zabe mai zaman kanta ta tabbatar da cewa, wakilanta ko ma’aikatanta sun kaucewa duk wani tsari na rashin gaskiya da ka iya zubar da kima ko mutuncin Hukumar. Dalili kuwa, bincikenmu ya nuna akwai zarge-zarge da dama da ake yi wa jami’an nata na kokarin hadin baki da karbar na goro a tabka magudin zabe. Ya kamata Hukumar ta kwana da sanin cewa, samun ingantaccen sakamako na wadannan zabubbuka ya dogara ne kacokan a kan aiwatar da zabe na gaskiya wanda ko’ina a duniya kan iya ba da kyakkyar shaida tare da yabawa.
Haka zalika, mutunci da kimar Nijeriya kadai na iya dorewa ne a idon duniya bisa la’akari da yadda Hukumar ta zabe da kuma ita kanta Gwamnatin Tarayya suka taka rawa wajen gudanar da zabe na gaskiya a fadin kasar baki daya. Haka nan, sanin kowa ne cewa, al’ummar kasa sun fi baiwa gwamnatin da suka zaba halak-malak goyon baya da hadin kai a kowane mataki fiye da gwamnatin da aka kakaba musu.
Babu shakka, a halin da ake ciki yanzu dole ne a yaba wa Majalisar Dinkin Duniya, Kungiyoyin Kasashen Rainon Ingila, Kungiyar bunkasa tattalin Arzikin Yammacin Afrika da sauran kungiyoyi daban-daban da suka nuna sha’awarsu na ganin an aiwatar da zaben Nijeriya yadda ya kamata. Haka zalika, muna sake yin kira ga Gwamnatin Nijeriya wajen ganin ta samar da wadataccen tsaro a kafatanin wadannan zabubbuka da aka sanya gaba. Dole ne a tabbatar an baiwa masu sanya ido na kasashen waje da ma na cikin gida kyakkyawan tsaro da kulawa, tare da baiwa al’ummar Nijeriya dama musamman don tabbatar zaben wadanda suke so su mulke so.
Haka zalika, muna sake yiwa wadannan masu sanya ido maraba da lale, muna kuma mika godiyarmu gare su dangane da kokarin da suka jima suna yi don ganin demokradiyya ta ci gaba da zama da gindinta a wannan kasa baki daya. Sannan muna sake yin kira ga masu sanya idon na waje da ma na cikin gida, da su jure duk wani abu na rashin dadi da ka iya haduwa da shi, su tabbata kuma sun kammala aikin da ya kawo su har zuwa karshen zabe. Kazalika, duk da cewa masu sanya idon ba su da wani hurumi na sawa ko hanawa a wajen zaben, amma suna da rawar da za su iya takawa na sanya ido tare da tabbatar da ganin an yi sahihin zabe kuma mai inganci.
A karshe, wajibi ne wadannan masu sanya ido su tabbatar sun yi gaskiya, sun kuma fitar da rahoto na gaskiya ba tare da bangaranci ko nuna fasha ba. Haka nan, dole ne su tsame kansu daga cikin rigingimu ko hayaniya da ka iya tasowa a filin zabe. Dole ne kuma su kula wajen yin magana da ‘Yan Jaridu ko manema labarai, duk abinda za su bayyana su tabbata suna da kwakkwaran dalili a kai kafin su kai ga bayyanawa ko sanar da su don gujewa fitina ko wani abu makamancin haka da ka iya kawo tasgaro ko rikici a zaben.
Haka zalika, ‘Yan Jarida da sauran manema labarai, ya zama wajibi su kula wajen bayar da rahoto na gaskiya, ba wanda zai kawo fitina a tsakanin al’umma ba. Bugu da kari, sauran al’ummar Nijeriya musamman masu amfani da zaurukan yada zumunta, mu ji tsoron Allah kada mu rika yada sakamakon zabe na karya wanda ka iya kawo tashin hankali da hargizi a tsakanin al’ummar wannan kasa baki daya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!