Connect with us

LABARAI

Ba Zan Yi Sulhu Da Masu Garkuwa Da Mutane Ba – Gwamna Yari

Published

on

Gwamnan jihar Zamfara, Rt. Hon. Abdul’aziz Yari Abubakar, ya bayyana cewa, ba zai yi zaman sulhu tsakanin jiharsa da masu kai hare-hare da yin garkuwa da mutane babu dare babu rana kuma ya rantse da Allah duk ta’addancin da maharan su ka yiiwa al’ummar jihar Zamfara sai sun rama.
Gwamna Yari ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai jajen da ta’aziyya a garin Kawaye da ke cikin karamar hukumar Anka.
Gwamna Abdul’aziz Yari ya mika ta’aziyarsa ga iyalan wadanda su ka rasa rayukansu sakamakon ta’addancin maharan kuma ya jajenta wa al’ummar kan kona mu su gidaje da shagunan kasuwanci da motoci 11 da kuma kona mu su rumbunan hatsi.
Gwamnan ya bayyana cewa, wadanan maharan sun kira Sarkin Zamfaran Anka ta waya a kan sun gaji da wannan ta’addanci. Don haka su na bukatar sulhu, amma Yari ya tabbatar da cewa, “babu sulhu da wadannan migayan ‘yan ta’addan tsakaninmu da su. Don haka duk matakin da za mu dauka don kare kanmu da ganin bayansu shi ne za mu yi.
“Wallahi ko mu ko su, babu ja da baya. Kuma Ina mai tababtar ma ku da cewa ba ku fi karfin gwamna ba, kuma kada wanda ya sake zuwa ma na da maganar sulhu wallahi babu.”
A nan take ya nemi da kwamadan sojojin bataliyar da ke Zamfara da ya karo sojoji isassu da kuma sauran nau’o’in jami’an tsaro a yankin na Anka da jihar bakidaya.
Ya ce, “su ma ‘yan sa-kai za mu kara karfafa su, don wajen ganin bayan ‘yan ta’addar, kuma wannan umarnin karo jami’an tsaro yau zai fara aiki.”
Sarkn Zamfaran Anka, Alhaji Attahihu Ahmad, ya bayyana cewa, Kawaye mahada ce da ta hada dazukan Maru da Gusau Dansadau da Birnin Gwari ta ko’ina ‘yan ta’adda na iya shiga garuruwan mu dan haka ya kamata a ajiye bataliya ta sojoji ta har abada shi ne kawai zai magance harin wadannan ‘yan ta’ada.
Yau dai kwana biyar kenan da maharan wanda yawansu sun kai 300 a mashina da motoci kirar Hilas, su ka kai wa garin Kawaye dirar mikiya inda su ka kashe mutane 13 su ka banka wa garin wuta da motoci goma sun kone kurmus, kuma su ka yi awon gaba da hakimin gari da matarsa da mutane 33, wadanda yanzu haka babu labarinsu. Amma sun sako uwar gidan hakimin, amma amarya da hakimin su na hannunsu zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Haka kazalikama a kauyen Kware cikin karamar hukumar Shinkafi a ranar Alhamis ta da gabata maharan sun durar ma ‘yan sa-kai masu rakiyar ‘yan kusuwa daga Kware zuwa Badarawa inda su ka kashe ‘yan Sakai da wasu daga cikin ‘yan kasuwar mutun talatin da uku.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!