Connect with us

MAKALAR YAU

Faduwar Kwankwasiyya A Kano

Published

on

Ranar Asabar da ta gabata aka fara babban zabe na kasar nan. An yi na shugaban kasa da ‘yan majalisa kala biyu. ‘Yan majalisar dattijai da wakilai.
Sakamakon zaben ya zo da bazata mai yawa. Za a dade ana bayar da misali da wannan sakamako. Dalili shi ne, an yi wasan kura da kungiyar Kwankwasiyya a lokacin zaben. Kafin a yi zaben mutanen kungiyar Kwankwasiyya suna da karfin gwiwar za su yi wa APC tumbur na siyasa. Suna da yakini za su samu kujerun Sanatoci da ‘yan majalisar tarayya, a shugaban kasa a Kano suna fatan samun mafi karanci kashi 25 ko mafi girma kashi 40.
A ranar da PDP ta karbi bakuncin Atiku Abubakar a filin kwallo na Sani Abacha, Kwankwasiyya tana bugun kirji cewa ranar zabe kawai take jira. A zatonsu, yadda sukayi ‘SAUKALE’ ga fastoci da banonin APC, haka zasu yi wa ‘yan majalisar dattijai biyu masu ci da na tarayya 15 masu ci ‘SAUKALE’ ‘yan Kwankwasiyya su maye gurbinsu.
Duk abin da suka zata bai faru ba. A cikin mazabu 484 na jihar Kano, PDP ta samu mazaba 36 ne kacal. A cikin kananan hukumomi 44, PDP ba ta samu ko daya ba. Duk ‘yan takarar PDP babu wanda ya ci karamar hukumarsa. Madobi inda nan ce mahaifar Madugun Kwankwasiyya bata tsira ba. Akwai mazaba 12 a Madobi da kyar da makyarkyata PDP ta samu uku. Daga karshe dai Kwankwaso ya taho da ‘yan majalisar tarayya tara, ya tashi ziro, ya na kan kujerar sanata ya fasa.
Al’adar wanda ya shiga zabe ne ko dai nasara ko faduwa. Menene ya jawo Kwankwasiyya ta fadi?
INA DA AMSOSHI GUDA GOMA:
NA DAYA, fankama da kuri da cika-baki. Kwankwasiyya ba a cika tsaya wa a yi aiki da lissafi na hakika ba, akasari ana gini ne da molonka da farfaganda. Akwai masu zabe kashi bakwai a Kano, sune: matasa da mata da masu ra’ayin addini da ‘yan kasuwa da ‘yan boko da sarakai da sauran talakawa. Kwankwasiyya da salon matasa take tafiyar da duk lamuranta, sam -sam bata la’akari da kashi shidan. Matasa ‘yan nishadi ne, ‘yan cakwakiya da holewa, suna iya bin mai kuri da fankama da cika baki. Shi ne dalilin da ya sa ko ina yaje Kwakwaso kan yi taken INA MATASA?.
NA BIYU, Rigima marar dalili da Ganduje. Idan kuka bi a tsanaki, kwata-kwata Kwankwaso ba shi da wani gagarumin sabani da Ganduje. Kwankwaso ya ari rikicin rashin samun mukami na su Dr Dangwani da Comrade Aminu Abduslam ya yafa akansa a madadinsu. Wannan ta janyo baraka mai girma a gidan Kwankwasiyya, inda Kwankwaso ya rasa manyan kwamandojinsa guda uku da Muktar Ishak Yakasai da Abdullahi Abbas Ciranci da Murtala Sule Garo.
NA UKU, Canjin sheka, ‘yan Kwankwasiyya sun canza sheka daga APC zuwa PDP. Wannan ya jawo kassara karfinta. Da yawa daga cikin wadanda Kwankwaso ya bari a PDP da ya yi zamansa a APC zasu kasance tare da shi. Amma ba zasu iya saki na dafe, suna cikin gwamnati ga jam’iyya a hannunsu su tafi neman wani abu kuma na daban a gurin wani ‘Indibidual ko kungiya ba’, su Abdulmumin Kofa da Barau Maliya sun so bin Kwankwaso, tunanin komawa PDP shi ya dakatar da su.
NA HUDU Sabani da Shekarau, da da Kwankwaso ya dawo jam’iyyar PDP sai ya zo da buri mai tarin yawa, har ya shige gona da iri. Hakan, ya jawo ya samu sabani da Sanata Ibrahim Shekarau, dankon zumunci da kokarin aiki na siyasa tsakanin Kwankwasiyya da mutanen Shekarau don tunkarar Ganduje da aka fara samu ya wargaje gaba daya. Daga karshe gurbin da Kwankwasiyya ta bari a APC Shekarau ya maye shi.
NA BIYAR, Son zuciya wajen fitar da ‘yan takara. Bayan Kwankwaso ya dawo PDP sai ya dauko sirikinsa wanda sam-sam a wahalar rigima da Ganduje babu wanda ya ke jin duriyarsa. Haka kuma wadanda suka biyo shi daga gidan Shekarau tsagi mafi girma na su Salihu Takai sai aka wofintar da su. Haka aka yi wajen fidda ‘yan takara na matakin sanata da majalisar wakilai. Da yawa ma an yi musu turin jeka ka mutu. Misali Ali Madaki da an barshi a majalisar tarayya, an dauko ko Aminu Dabo ko Farfesa Hafizu haka zai zaunar da gidan kuma an samu abokin karo ko kuma maimakon a baiwa Rabiu Sulaiman Bichi takarar Sanata tare da Barau, sai aka tura Ahmed Garba Bichi, Ahmed Garba ya dade yana barci a majalisar tarayya.
NA SHIDA, Kasawa matuka a majalisar dattijai. Gaskiyar magana a majalisa Kwankwaso babu wata gudunmawa da ya bayar ko ga Kano Central ko Najeriya. Yaje dumama kujera ne kawai. Hankalinsa ya tafi kaco-kam ga neman takarar shugaban kasa, ko dalilin bulo daya bai kawo mazabarsa, yana cikin masu dumama kujera. Sannan sai da ya yi shekara uku da rabi ya zo Kano tunda ya tafi. Babu helo ba fito tsakaninsa da mutum dubu 758 da suka zabe shi, balle miliyan uku da rabi na Kano Central. Sai dai labarinsa kake ji a Ile Ife ko Makurdi ko Agege ko Ogbomosho.
NA BAKWAI, Sabawa da tarbiyyar Kano da al’adunta. Mutanen Kano suna son addini, suna son mutunci da girmama dan adam da kaskan da kai da nutsuwa. Ba ruwan Kwankwaso da wadannan abubuwan, wasu masu binsa ma sun ce suna binsa ne saboda ya yi wa wasu rashin mutunci, har MUMBARIN ASHAR yana da shi, zai iya zagin kowa, zai ma iya cewa za a kamo gwamna ba ruwansa. Wannan ya saba da duk al’adun siyasa na Kano. In kana yi zaka biya farashi. Mafi kuskuren abin da ya yi gab da zabe shi ne ramuwar da ya saka kafar wando da malamai zai yi.
NA TAKWAS, Batawa dana kusa da shi. Tunda Kwankwaso ya shiga PDP ko mutum daya babba a APC bai dawo ba daga baya saboda shi ya shiga. Amma su Aminu Dabo da Farfesa Hafizu da Janar Dambazau da Bala Gwagwarwa da kuma da yawan mabiyansa suka rika sulalewa suna komawa APC. Wadannan manyan dakaru ne kuma katanga ce da ta lullube shi. Hakan ya jawo tsirarar Kwankwasiyya.
NA TARA, Mamaye wajen kamfen dinsa da kansa. Kwankwasiyya ta zagaya 44 LG, amma yawo ne kawai ba isar da sako ko yada manufa ba. Su kansu maku takarar ba a sauraronsu sai RMK, shi kuma jawabansa daga ‘zaman doya da manja’ sai in an je wani gurin a ce an yi ‘Cikin Shege a Abuja’ ko kuma a ce ku ce ‘Ana HEGE’ A wasu guraren kuma sai a yi ‘Jan Baki Sari Koto’ ko ‘Dan Akuyannan Damushere’ wadannan babu ma’ana cikinsu. An dauki lokaci kawai ana yawon barkwanci, wanda kamata ya yi a bar wa su BOSHO da GWANJO ko 2Face.
NA GOMA, Buhari ikon Allah ne.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!