Connect with us

TATTAUNAWA

Komai Zai Gyaru Tunda Buhari Ya Zarce – UGS

Published

on

INJINIYA SULAIMAN A. MUSA, wanda a ke yiwa lakabi da UGS, na daya daga cikin masana kuma dan siyasa mai fashin bakin al’amuran yau da kullum musamman a matsayinsa na dan jam’iyyar APC mai mulkin kasa, sannan kuma shugaban kamfanin tuntuba na kamfanin gine–gine na UGS Consultant. Ya bayyana wasu abubuwa wadanda jam’iyyarsu za ta saka a gaba bayan da ta samu nasarar lashe zaben shugaban kasa da kuma abubuwan da ya ke fata da shawara ga shugabanni. Wakilin LEADERSHIP A YAU LAHADI, MUSTAPHA IBRAHIM TELA, ya zanta da shi, inda ga yadda hirar ta kasance:

Kasancewarka dan jam’iyyar APC ga shi kamar gobe ne ko jibi za a fara gabatar da zaben gama-gari kuko ma babban zabe na Shugaban Kasa dana yan Majalissaun Dattawa da Wakilai na 2019. Ku kana da wata shawara ga yan Najeriya?
Godiya ta tabbata ga mahaliccinmu wanda ya kawumu wannan lokaci domin kaga kamar jiya ne ku shekaran jiya mukai zaben na 2015 wanda ya kawu Gwamnatin APC karkashin Jagorancin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari gashi yau shekaru hudu kenan da wannan zabe. Idan ka tuna a baya zakaga cewa kumai ta Jagwalgwale a Najeriya kama daga harkar Tsaro, Tattalin Arziki, Cinhanci da Rashawa da dai sauran matsaloli duk sun addabi Najeriya da al’ummarta, amma za ka ga yanzu harkar tsaro sai mu godewa Allah da ya bamu wannan dama ta ganin wannan yanayi ta yadda yanzu mudai anan bawata fargaba kamar yadda take a baya kuma kaga shi in ana maganar gyara to sai a hankali domin za ka ga cewa wannan wuri damu zaune da kai a halin yanzu za ka ga cewa idan akace ga kudi da kayan aiki kazo ka ginashi a yanzu ba yadda za’ayi ka iya ginashi a yanzu duk da cigaban zamani amman rusheshi dan kankanin lokaci ne akwai kayan aiki na zamani da zamu iya rusheshi yanzu yanzunnan to ka ga wannan ya nuna cewa gyara sai a hankali kasan dai Jam’iyyar PDP tayi barna tsahun shekaru 16 a Kasar nan kuma duk da haka a alkawaran Buhari zakaga cewa ba’inda zaka dub aba inda ba’a aiki raya kasa kudu da arewa da gwamnatin Buhari keyi, sabuda haka a bashi dama ta shekara Hudu ya kara za’a samu dai-daito da cigaban al’umma abashi dama kumai zai inganta na daidaita sahun Najeriya ta fuskar cigaba na kuwanni bangare na gina Kasa ta kuwacce fuska da ake bukata Najeriya ta zama.

Kullum ku yan Jam;iyyar APC kuna batun ayyukan raya Kasa kuma yan Jam’iyyar hamayya kamar PDP da maka mantansu na ganin cewa kunzu mulki baku da wani abu da ake kire Blueprint a turance kawai kame-kame kukeyi wanda shi ne ma ake ganin ya Jawu miliyoyin yan Najeriya na cikin bakin talauci da rasa aikinyi kamar yadda wata hukuma ta kididdiga ta bayar, Ina Batun Gina Dan Adam A Gwamnatin Kuta APC?
Ko da ya ke abun da kafada na hukumar kididdiga ni bansanshi ba kuma bace maka babu ba amma ni ban sanshiba, amman kasani inda Jama’ar Najeriya zasuyiwa Gwamnatin APC Adalci an san cewa duk Duniya ba’inda za’ace Gwamnatice zata zamawa al’ummarta aikinyi a iya sanina amman duk da haka Gwamnatin APC ta shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta yi rawar gani sosai wajen samawa matasa aikin yi da kuma hanyoyin dogaro da kai musamman ta fuskar bunkasa aikin gona wanda ke samawa miliyoyin yan Najeriya aikin yi. Haka kuma in ka duba ga harkar N-Power, Trader money, N-Sip da sauransu duk annan hanya ne data samarwa Al’ummar Najeriya aikin masu yawa, da ace PDP tayi irin wannan shiri a baya da APC da tazo dorawa zatai to da yanzu mastalar rashin aikin yi ta kau a Najeriya.

Akwai batun wasu da suke dauka cewa zabe ku’amutu ku airai me za kace a Jam’iyyar ku, kuma haka ne?
To duk wanda yasan Jam’iyyar mu ta APC ya san ba batun zabe ko amutu ku ai rai wannan ba’akidar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ba ne kuma kasani cewa ko’abaya ansha bayyana cewa Buhari ne yace zabe amma ba’abashi ba to ka ga to ai bahaka yake ba ba batun do or die a akidar APC duk wanda ya ce zabe shi kenan kuma kana jina akwai wani Jakada Amerika da yake cewa zaben baya ma da dama Buhari ya ci amma kollum cewa yake abi doka da oda kuma kanaji yana fada hukumar zabe ta INEC cewa tayi adalci duk wanda yaci zabe a bashi kuma yanzu kaduba saboda bin doka da oda yanzu Zamfara, Ribas APC ba ta da dan takarar Gwamna saboda bin doka to kuma kumai ma ya tasu yana cewa ba mulkin Soja bane don haka sai anbi doka domin yace abaya ma shima an daureshi shikara Uku ba tare da laifinsa ba don haka dai kumai na Buhari a doka yake cewa ayi.

Meya kamata ayi la’akari da shi wajen zaben shugaba da Gwamnoni da Sanatoci da sauransu a matsayinka na dan APC?
Kamar yadda shugaban Kasa da kansa ya ce a zabe shugaba nagari a kuwanni mataki to nima shi ne ra’ayina a zabi mutane nagari akuwanni mataki amman kuma inada ra’ayin a zabi shugaban kasar na APC domin kuda akwai kura-kurai a mulkin wanda baza’ace babu ba to amma in an zabe APC a wannan mataki ta kara shekara Hudu to ka ga tayi Takwas kenan inaga duk kura-kuran da’aka samu za’a gyarasu a wannan shukaru Takwas ni abun da nake fata kuma abun da nake so kenan wanda a 2023 in Allah yakaimu APC ba sai tayi Kamfen ba.

Yayin da kake ganin Nasarori da Jam’iyyar ku ta samu a Kasar nan na aiyuka yan hamayya da sauran masu bin diddigin al’amran siyasa nay au da kullun na ganin cewa ayyukan ku muta nen kudu ne kawai sukafi mura ta hanyar samun titian dama da 700 me za ka ce?
To sai ka gayamin abun da akaiwa Arewa tunda kafadi na kudu dan Jarida ni kuma sai inma bayani kan kididdiga da kuma abun da ake la’akari domin kai kafi kuwa sani ko dan dai bakasu aji a bakin ka. To bari in gaya maka wadannan ayyuka da mutanen kudu suka samu, muma munsamu abun da basu samu ba misali mufara akwai maganar aikin wuta na Manbila Arewa ne, Tashar Jirgin Ruwa ta Naija Arewa ne, hako man fetur a Bauchi Arewa ne, ga kuma maganar Titi daga Akonga zuwa Benue, titin Kano zuwa Abuja, da dai sauran su duk Arewa ne, kuma ba’aci abun da mutanen kudu suka samu yafi na Arewa kai tsaye sai ka duba lissafi kayi kididdigan kudi nawa aka kashe a Kudu nawa aka kasha a Arewa kuma kasani cewa Buhari Shugaban Kasa ne ba Shugaban Arewa ko Kudu ba ne, kuma shi ba irin Shugabacin Jonathan da Obasanjo bane da suka nuna banbanci karara suka fifita wani bangare akan wani bangare ba Buhari bai yarda da haka ba.

A karshe Injiya Sulaiman UGS meye shawarar ka ga duk wanda ya samu nasara a wannan zabe na wannan Asabar din?
To abun da nake so Shugabanni su sani shi ne Nasara daga mahallincin mu take in kaci shi ne in karasa shi ne kuma kuwanne ya kamata ya karba kuma ya yarda da kaddara in kafadi kayi nazari mai ya ka da kai kaddarace ku kuwa rashin kyautatawa al’umma ne ya saka fadi sai kayi nazari don gyaran gaba. Haka kuma in ka samu Nasara kasani cewa ba don kafi kuwa ba ne haka Allah yaso don haka akwai bukatar duk wanda aka zaba akuwanni mataki tundaga kan Kansila, Shugaban Karamar Hukuma, Dan Majalissar Jaha, Dan Majalissar Wakilai na dattawa har zuwa kan Shugaban Kasa adalci yana jiranka kayishi wajibine domin Allah zai tambayi abunda kayi musamman mu da muka san haka a addininmu kuma adalcinnan dole ne kayiwa dan Kudu kayiwa dan Arewa kayiwa Musulmi kayiwa Kirista kayiwa kuwa har mara Addini wajibin ka ne kayi masa adalci kuma kowa ya tsaya ya duba kura-kuransa yayi gyara musamman mu a Jam’iyyar mu ta APC mu saya muyi nazari za kyau duk inda akadan anyi kuskure a gyarashi kada a sake maimaitawa kuma kuwannen mu yaji tsoron Allah duk wani mukami da za’aba kuwanni mutum a tabbatar ya san abun kuma yana da kishin al’umma da Kasar sa to wannan shi ne shawarata ga wanda suka samu Nasara a zaben 2019 dama wanda suka sami akasin haka kuma ba maganar tashin hankali ba maganar fada ku wannen mu ya bada gudummuwa wajen zaman lafiya a Najriya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!