Connect with us

BIDIYO

Sharhin Fim Din ‘Laila Adam’

Published

on

Suna: Laila Adam
Tsara Labari: Ibrahim Birniwa
Kamfani: Family Inbestment
Shiryawa: Sani Indomie
Umarni: Ali Gumzak
Jarumai: Ali Nuhu, Sadik Sani Sadik, Aisha Aliyu Tsakiya, Isa Bello, ‘Yar Gatan Baba, Ibrahim Bala. Da sauran su.

A farkon fim din an nuna Aliyu (Ali Nuhu) ya dawo gida daga wajen aiki a sakamakon labarin da ya samu na rashin lafiyar matar sa Laila (Aisha Aliyu Tsamiya) sai dai kuma bayan dawowar ta ya samu har taji sauki a sakamakon maganin da ta sha, hakan yasa ya cigaba da ririta ta har ya hanata yin girki ya dauke ta suka je cin abinci a restaurant. An nuna Aliyu mutum ne mai tsananin son matar sa gami da bata duk kulawar da take bukata.
Ana tsaka da haka ne wata rana Laila ta fita sai aka samu akasi wani mai mota ya buge ta wanda dalilin hakan yasa taji rauni a hannun ta, nan fa mai motar wato Safwan (Sadik Sani Sadik) ya dauke ta a motar sa don kaita chemist inda za’a sanya mata magani, sai dai kuma bayan zuwan su chemist din suka tarar wajen a rufe yake, hakan yasa ya kaita gidan sa yayi mata magani a raunin da taji, bayan fitowar ta kuma ya bata katin sa akan lallai ta neme shi daga baya.
Saidai kuma Laila tana zuwa gida ta yaga katin da ya bata sannan ta cigaba da sabgogin ta. Shi kuwa Safwan tun bayan haduwar sa da Laila sai yaji kaf duniya babu wadda yake so sai ita, domin har a sannan bai san da cewar tana da aure, yayin da itama Laila haduwar ta da Safwan tasa taji ya burge ta musamman a yadda yake nuna mata tsananin kulawa da soyayya, hakan yana ko bayan ta yaga katin da ya bata (complementary card) sai ta koma cikin sharar da ta saka ta binciko katin ta dauki lamabar sa ta kira sa, hakan yasa Safwan yaji dadi kuma yasan hakan shi yana gab da cimma ruwa, anan suka tsara yadda za su hadu da Laila a gidan sa.
Hakan yasa Laila ta yiwa mijinta Aliyu karyar zataje unguwa ta fice ta tafi gidan Safwan Wanda bayan zuwan ta har girki yayi mata taci abinci sannan suka shiga cikin daki. Tun daga wannan lokaci Laila da Safwan sukayi ta cin karen su ba babbaka, aduk sanda yake son ganin ta haka take tahowa gidan sa su hole, daga bisani ma har yawon shakatawa suke fita wanda dalilin hakan ne yasa wani abokin mijinta ya ganta tare da Safwan suna shan ice cream, ganin su ne yasa ya gayawa mijinta Aliyu, saidai kuma Aliyu bai gasgata shi ba yana ganin kamar kazafi aka yiwa matar sa.
Su kuwa iyayen Laila ganin yadda mijin ta yake kyautata musu ne yasa suka nuna matukar bata yi masa biyayya ba basu yafe mata ba, jin hakan ne yasa Laila ta soma kokarin gujewa Safwan amma sai yayi mata garkuwa da wasu hotunan ta wanda indai ta guje ta zai nunawa mijin ta dole tasa ta cigaba da amince masa har zuwa wani lokaci da Safwan yaga wata dalibar sa a makaranta wato Siyama (Hafsa ‘yar gatan baba) wadda ta kasance kanwa ga Laila, ganin ta ne yasa ya nuna yana son ta da aure, ita kuma dama ta jima tana son shi don haka bata musa ba ta amince masa, saidai kuma bayan Laila ta samu labarin abinda ke faruwa sai taki amincewa Siyama ta auri Safwan, hakan yasa Laila suka fara samun sabani da kanwar ta Siyama wanda har a karshe Laila ta bawa Siyama labarin duk abinda ya faru tsakanin ta da Safwan, jin hakan ne yasa Siyama ta fuskanci Laila kuma taci alwashin fasa auren Safwan.
Yayin da shi kuma Safwan suka hadu da Aliyu mijin Laila a wajen cin abinci har suka kulla abota wadda ta kai Aliyu har gidan Safwan anan ne ya gane Laila tana cin amanar sa, hakan ne yasa Aliyu yaje yaci zarafin Laila yayi tur da halin cin amana irin nata.

Abubuwan Birgewa:
1- An samar da wuraren da suka dace da labarin wato (locations)
2- Marubucin yayi kokari wajen gina labarin, sannan kuma kalaman bakin jaruman sun yi dadi. Wato (Dialogue)
3- Daraktan yayi kokari wajen ganin fim din ya tafi yadda ya dace.
4- Camera ta fita radau, haka ma sauti ba laifi.

Kurakurai:
1- Lokacin da Aliyu ya dauki matar sa Laila (Aisha Tsamiya) don zuwa cin abinci a restaurant, yanayin shigar ta gami da kitson kanta da ta sake shi a baya hakan yafi kama da wadda bata da aure, sai gashi kuma bayan ya kaita gidan wata kawarta inda zata sayi wasu kaya me kallo yaga bayan ta yafa mayafi har kallabi tasa ta nade kanta da gashinta gaba daya, ya dace ace a can waje ne ta rufe duk wani tsiraici fiye da yadda tayi a cikin gida gaban ‘yar uwarta mace.
2- Lokacin da Safwan (Sadik Sani) ya buge Laila da mota, bayan ya dauke ta don zuwa chemist, yanayin yadda ta sake dashi suke hira hakan sam bai nuna alamun cewa tana da aure ba, duk da kuma alamu sun nuna cewa Laila kamilar mace ce mai ilimi, amma babu alamun kamun kai a cikin irin sakewar da tayi dashi.
3- Lokacin da Safwan ya nufi chemist da Laila don a saka mata magani a raunin da tayi, ganin chemist din da suka nufa a kulle bai kamata Laila ta amice da zuwa gidan sa cikin sauki ba, ya dace ta nuna masa sai dai suje wani chemist din domin a matsayin ta na matar aure sam bai kamata ta amince da zuwa gidan wani Dabier namiji ba musamman akan ciwon da bai kai ya kawo ba, idan ma tattaunawar da ta gabata a tsakanin su ake son nuna wa to ya dace ayi amfani da hanyar da mai kallo zai gamsu da zahiri ake nuna masa ya hanyar samar da wani wajen ko da kuwa a cikin wani chemist din ne idan mai chemist din baya kusa amma ba sai a gidan sa ba.
4- Lokacin da Siyama taje gidan Laila ta bata labarin cewar Safwan zai aure ta, kalaman bakin Laila da na kanwar tata basu hau da muryoyin su ba.
5- Bayan haduwar Laila da Safwan me kallo yaga Safwan ya bata katin sa da nufin ta kira sa, amma sai aka ga ta yayyaga katin ta watsa a shara, bayan wani lokaci kuma sai akaga Laila taje wajen sa a karo na biyu, sa’in da ya bukaci tace masa tana son shi amma ta tabbatar masa da cewar tana da aure, shin dama a lokacin da suka sake haduwar Laila bata da lambar shi? Idan har bata da lambar shi ta ina suka tsara inda suka hadu a karo na biyun? Domin sai bayan sake haduwar tasu ne a scene na gaba aka nuna Laila ta nemo katin da ya bata a cikin sharar da ta saka, kuma a jikin katin ne aka nuna ta dau lambar Safwan din ta kira sa, ya dace a fara nuna lokacin da ta dau lambar tasa a wayar ta kafin haduwar su ta biyu da aka nuna.

Karkarewa:
Fim din ya nishadantar domin an yi nasarar rike me kallo har zuwa inda ake son a kai sa, sai dai kuma labarin bai gama direwa ba, domin ba’a nuna makomar auren Laila da Aliyu ba, shin zai mayar da ita gidan sa ne bayan cin amanar da tayi masa? Haka kuma ba’a nuna karshen Safwan ba (Sadik Sani) wanda ya zamo fasiki mai zaman dadiro da matan aure, ya dace a nuna makomar sa ko don hakan ya zamo darasi ga masu hali irin nasa. Wallahu a’alamu!
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!