Connect with us

TATTAUNAWA

Ba Za Mu Ci Amanar Al’ummar Jihar Kano Ba, Inji Abba Kabir Yusuf

Published

on

Wannan hira ce da dan takarar Gwamnan jihar Kano a karkashin Jam’iyyar PDP, INJINIYA ABBA KABIR YUSUF ya yi da manema labarai ciki har da wakilinmu na jihar Kano, IBRAHIM MUHAMMAD, ya tabo bautuwa dama a kana bin day a shafi shirye shiryensa ga al’ummar jihar Kano in ya samu nasara lashe zaben da za a gudanar na kujerar gwamna, ga dai yadda hirar ta kasance.

Za mu so muji wane irin buri kake da shi a wannan takara da kake na Gwamnan Jihar Kano?
Kamar yadda al’ummar Jihar Kano suka sani, mun fito wannan takara ta neman Gwamna ne bisa kishi da muke dashi na inganta rayuwar al’ummar Kano, kuma mun fito ne musamman mu da mukayi aiki a Gwamnatin Kwankwaso wanda kowa yaga irin ayyuka na alkhairi wanda Gwamnatin baya ta aiwatar a Kano na raya da inganta rayuwar al’umma musamman ayyuka da suka shafi ilimi da kiwon lafiya da ayyuka na samar da tituna, Gadoji da inganta harkokin kasuwanci da noma. To ni musamman dana fito wannan takara na fito ne domin in dora a kan dukkan ayyuka wanda Gwamnatin Kwankwasiyya ta yi a baya, musamman abin da ya shafi harkar ilimi, mu a wajenmu ilimi shi ne ginshikin rayuwar al’umma idan babu shi an shiga wani hali, saboda haka mu muna da kudurori masu kyau a kan harkar ilimi, muna so mu ci gaba da bai wa dalibai ilimi kyauta, mu ba su kaya na sawa, suje makaranta kyauta mu basu littattafai da sauran kayan aiki a aji kyauta da duk abinda suke bukata don ingantasu suma su girma su sami ilimi da zai anfani al’umma wannan shi ne abinda muke sa a gaba, tallafawa ilimi, mu inganta rayuwar Malamai ta ba su hakkokinsu da aka danne musu na aiki da rashin basu albashinsu da wannan. Akwai hobbasa da Gwamnatin baya ta yi na zakulo yara zunzurutun ya’yan talakawa masu kwakwalwa amma babu gata ta biya musu kudade, munaso mu in muka sami Gwamnati zamu ci gaba da zakulo ya’yan talakawa masu fasaha da kwazo da suka ci jarabawa a sakandire mu debe su mu kaisu kasashen waje su yi karatu tun daga digiri na farko zuwa na biyu dana uku domin mun ga anfanin abin.Yau a cikin wadanda aka kai waje fiye da 3000 yawancinsu sun gama sun samu ayyuka a kasashen duniya daban-daban masu muhimmanci suna yi wasu sun dawo gida suna yi, muna da niyya zamu dawo da wannan, sannan akwai gurabe a jami’oi na Gwamnatin Tarayya da Kano take da kaso a ciki, wanda wannan Gwamnati ta yanzu bata lura da su, dalibai suna nan anki a samo musu a cike su, za mu tabbatar mun cikesu don anfanin dalibai, akwai makarantu na addinin musulunci musamman tsangayu da ya kamata ace Gwamnati ta farfado da yadda ake gudanar da su a zamanance ta taimakesu ta ingantasu da inganta rayuwar malamansu ta taimakawa dalibansu da suke zaune a mawuyacin hali suna karatu. Muna so mu ingantasu ta yi musu ajujuwa mu tabbatar an taimaka wa sha’ani na addini.

Wani shiri gwamnatinka ta tanadar wa mata?
Akwai fanni da ta shafi mata duba da daraja da kimarsu da mutuncinsu da kuma raunin zuciyarsu da suke da bukatar a taimakasu, su suka haife mu suka renemu suke bamu tarbiyya harkar iyaye mata baza mu yi wasa da kulawa da ita ba, musamman lafiyarsu. Mata masu juna biyu wanda suke zuwa haihuwa asibiti ga talauci aje a kai su asibiti ba abin da za a karbi wannan haihuwa sai kaga mace ga yunwa in tazo haihuwa sai kaga ta rasa ranta ko dan ta haifeshi cikin wahala ko a rasau su biyun gaba daya, wannan abu ne da ya damemu kuma da yardar Allah daga cikin kudurinmu shi ne mu tabbatar irin wadannan mata, mun sama musu damar kulawa da haihuwa kyauta su sami haihuwa lafiya. Na taba zuwa Asibiti wata mata ta haihu an fito ana neman yaya za a yi a karbi wannan jaririn sai watace ta bada dankwalinta aka dora yaron rigarma da za a sa masa yaro ya shigo duniya da sanyi yana kakkarwa babu, saboda haka wannan yana daga abin da yasa Gwamnatin Kwankwaso ta baya ta shigo da tallafi ga mata.
Bangaren Tattalin Arzikin al’ummar Kano kuma fa?
Akwai magana na tattalin arziki musamman yan kasuwa mun san yadda ake takura musu da wahalar da su dasa musu haraji na babu gaira babu dalili da yadda hukumomin hana fasa kwauri ke shiga shagunansu su kwashe musu kaya saboda keta doka, za mu yi kokari mu kwato hakkinsu mu bunkasa kasuwancinsu. Akwai maganar yan kasuwa na kasashen duniya manya da suke shigowa kasar nan an daure musu gindi ana kwace kananan kasuwanci da ‘yan kasuwarmu suke yanzu dan kasar Chaina ne yake Hula, biredi da awara wannan ba abune da ya dace ba, za muyi kokari mu kwatowa musamman kananan yan kasuwa yancinsu.Yanzu akwai tabarbarewar tarbiyyar matasa, muma a baya matasa ne mun san yadda iyaye da shugabanni suka bamu tarbiyya muka kai inda muke a yanzu. A yau abu ya lalace gwamnati ta yi fancakali da wannan tarbiya yanzu ita ce take sayo kwaya saboda kawai rashin kishi tana bai wa ya’yan talakawa kwaya. Jami’an Gwamnati su ba su makamai suce ku tafi ku sari mutane, wannan muna Allah wadai da su. Muna da kudurin taimakon nomama musamman kananan manoma wadanda taki da magunguna na zubawa shuka ke musu tsada, wani lokacin taki mai al’mundahana da ake durawa kasa ake sayar musu duk wannan zaluncin za mu hana shi mu farfado da kanfanonin Gwamnatin jiha nayin taki da magungunan kwari da za a sawa manoma farashin da ba zai gagaresu saye ba sannan a koya wa manoma yin noma na zamani da noman rani. Akwai bangaren bada ruwan sha kowa ya san kokarin da Gwamnatin baya ta yi ta sayo manyan bututun ruwa ya shiga kananan hukumomi, amma yau babu ruwa a fanfuna sai yan turin kura ke debowa su sayar ko yana da kyau ko ba shi da kyau talaka ya saya hakan na hassasa kamu wa da cutuka daban-daban, za mu inganta samar da ruwa mai tsafta mu yi rijiyoyin burtsatse da za a sa musu kan fanfuna da kananan matatun ruwa don bada ruwa ga al’umma.

Wane kira kake da shi ganin cewa ana tunkarar zaben Gwamnoni dana yan majalisun JIha nan gaba kadan a kasar nan?
To Kano kamar yadda ake cewa Kano tunbin giwace koda me ka zo Kano an fi ka, mu musamman irin tarbiyar da wadatar zuci na mutanen Kano da tsayawa da akida,amma abin bakin ciki zabe yazo da akayi na shugaban kasa daya wuce wancan satin mu dai bamu san yanda akayi ba,abinda muka gani bamu san yayay wannan abu ya faru ba.Allah shiya barwa kansa sani,wadanda sukayi dangwale su suka sani,saboda haka abinda ya faru ya faru,muna fata muna kira ga al’ummar jihar Kano musamman mata domin sune kasha 80 bisa 100 na yan dangwale kada su sake yarda su saida mutuncinsu su saida rayuwar yaransu wadanda muke so mu taimaka mu ciyar mu shayar mu tufatar suma su sami ilimi su yi rayuwa mai albarka su zama wani abu, idan mata suka yarda N200 da 300 da 500 da aka ba su na koko da kosan safe shi kuma wannan abu da mu ka yi a baya muke so mu zo mu sake inganta rayuwarsu da yaransu in Allah ya yarda in mun sami Gwamnati suna cikin wannan daula da walwala, yanzu duk wannan abu da ya faru a zabe ina kudin? Duk wacce ta je ta saida ‘yancin ta taje ta dangwalawa abin da ba shi ya kamata a zaba ba, yau ina wannan kudi babu, kuma za ta jira shekara hudu Allah ya kiyaye da ita da ya’yanta suna cikin wannan muna fata wannan jiha tasu ce su zo su fito kwai da kwarkwata su kada mana kuri’a su zabi wannan abin da suke kauna wanda suke cewa gida-gida su tabbatar kuma jam’iyyarsu suka zaba ita ce PDP mai lema kar a rudar da su babu inda gida-gida yake face a jam iyya mai alamar lema. Muna kira gare su suji tsoron Allah su tausaya wa ya’yansu da kansu da mazajensu da al’ummar Kano kada azo ayi abin da za a yi dana sani.

Mun gode
Nima na gode
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!