Connect with us

TATTAUNAWA

Samun Man Fetur A Bauchi, Babbar Ci Gaba Ne Ga Arewa, Inji Alhaji Sale Moriki

Published

on

Tun a farkon shekarar da ta gabata gwamnatin tarayya ta amince da yaddar tan a samun man fetur a garin Alkaleri ta jihar Bauchi, wanda kuma a farkon wannan shekara ta 2019, har ila yau gwamnatin tarayya ta amince da a fara gudanar da binciken tabbatar da bayanin binciken cewar a kwai man fetur a karamar hukumar Alkalerin da aka bayyana.
A kan haka wakilinmu da ke Zariya BALARABE ABDULLAHI ya sami da damar zantawa da dattijo sauran mazan jiya, kuma mai tsokaci kan al’a murran yau da kullun a tarayyar Nijeriya mai suna ALHAJI SALE MORIKI, da ke gudanar da harkar kasuwancinsa a kasuwar P/Z a Sabon Garin Zariya. Ga dai yadda tattaunwarsa da wakilinmu ya kasance,

Me za ka ce kan batun samun man Fetur a garin Alkaleri ta jihar Bauchi?
Babu ko shakka wannan muhmmiyar Magana ce, addu’ar da ya kamata al’ummar Nijeriya musamman na arewa su hyi shi ne Allah ya sa gwamnatin tarayuya ta yi kyakkyawa tsari na yadda wannan al’amari zai tabbata, kuma al’ummar arewka da sauran al’ummar Nijeriya su amfana, musamman ma dai al’ummasr arewa.
Domin mu da mu ke bi- biyan al’amurran da suke faruwa a batutuwan da suka shafi samun man fetur da ake gano wa a arewa, mun san an dade ana sa abubuwa da suka shafi siyasa da kuma abubuwa da dama da suke kawo cikas da duk wani bincike da aka dora dambar yi a lokutan baya da suka shafi gano man fetur a wasu sassan arewacin Nijeriya.
Domin a shekarun baya, za ka sami agwamnatin tayarra ta bayar da umurnin fara yin binciken gano man fetur a wasu sassa na arewa, sai ka ga an fara binciken amma daga baya sai a sa wasu dalilai marasa karfi, a dakatar da binciken da aka fara tare da kwashe kayayyakin da aka fara gudanar da binciken.

To laifi wanene na kasa ci gaba da binciken batun man fetur a jihohin arewa ?
Babu ko shakka laifin na shugabannin arewa ne da suka gabata, kuma wannan batu a bayyane yak e, domin duk abin da ake bukata na ma’adinai a kwai su a jihohin arewa, matsalolin rashin alkibla daga wasu shugabannin arewa ne ya sa ko da an fara binciken sai a wayi gari, ka ga an dakatar da binciken, ba tare da bayyana wasu dalilai ma su karfi ba.
Wato dai matsalolin suna da yawa, na farko da rashin kishin wasu shugabanninmu na arewka, da kuma rashin kula da abin day a kamata a ce sun sa ido a kan su da suka shafi arewa, na kan gaba a kan matsalolin da suke addabar jihohin arewa zuwa wannan lokaci, kuma gyaran da ake tunani ba zai tabbata ba, sai an yi wushisshire – gyara zama a tsakanin wadanda ake ganin sune shugabannin a arewa, ko kuma wasu da ake ganin suna Magana da yawun al’ummar arewa. Amma a wannan karo na gano alamun man fetur a jihar Bauchi, za a sami canji daga ire – iren
binciken da aka yi a shekarun baya.

A baya ana alakanta matsalolin da siyasa, kamar yadda kai ma ka fadi a baya, to ya ka dubi wannan yunkuri kuma gwamnatin tarayya ta yi da ya shafi binciken man fetur a jihar Bauchi ?
Ni a halin yanzu in ma siyasar aka sa a shekarun baya na binciken duk wani ma’adini da aka gano a arewa, to a yau a cire siyasar a dubi arewa da al’ummar da suke arewa, shi ne kawai mafita.

Wasu gudunmuwa ka ke ganin ya zama wajibi al’ummar arewa su bayar, domin ganin wannan bincike ya haifar da da mai ido ?
Ni shawarar da na ke bayar ga duk wanda ya sami wata dama, ya yi kokarin amfani da damar kafin ta kubuce ma ka,wato da yawa, damar da ‘yan arewa suka samu da ya shafi na gwamnatoci, sai akasarinsu suka yi watsi da damar suka sami shagala, amma yanzu tun da akai damar, sai a yi kokari na ganin tarihi bai maimaita kan sa ba.
Kuma abin dubawa ma shi ne duk wani dan kudancin Nijeriya, ya san a kwai ma’adinai da dama a arewa, ba ma fetur kawai ba,tun da sun sami damar rike madafun iko, ba za su bari a sami nasarar duk wani binciken ma’adinai a arewa ba, abin day a dace ‘yan arewa mu fahimta shi ne,
sa hankali8 ga al’amurra, shi ne mafita.Sai a hada kai a je siyasa gefe guda, a rungumi arewan baki daya, domin samun mafita, ba mafitar da za ta cutar da wata jinsi ba, in an yi haka, sai a tsirar da ‘ya’yan arewa da suke cikin matsaloli ma su yawan gaske.

Ya ka dubi yawan kungiyoyi da aka kafa su da sunan arewa, ka na gani9n ba za su sa ido ga wannan matsala ba.
Ai duk yawan kungiyoyin da suke arewa, tamkar yawan tsintsiya ne da ba yin shara da su,lokaci ya yi da za a yi koyi da kudancin Nijeriya da suke kafa kungiyar al’ummarsu guda daya, ta haka ne suke samun nasarar da suke samu, ba yadda kungiyoyi da ake kafa su a arewa, amma sai ka
ga suna raba kan al’umma, ko maganar da bai dace sun yi a madadin al’ummar arewa ba, sai kuma babbar Magana da yadda kungiyoyin ke raba kan al’ummar arewa, wadannan batutuwa, duk tsofaffin labarai in an waiga baya na yadda mafiya yawan kungiyoyin ke gudanar da ayyukansu da sunan arewa ko kuma al’ummar arewa.
Kuma lokaci ya yi da shugabanni da kuma wadanda ke kafa kungiyoyi da sunan arewa, su fAhimci al’umma sun fara gane tafiyarsu, domin a nan gaba , ‘ya’yanmu ko kuma jikokinmu, za su fito karara su bayyana ma su kura – kuran da suke tafka wa da sunan arewa ko kuma al’ummar arewa.
Kuma har abada tarihi ba zai manta da Sardauna da ayarinsa ba, na yadda suka sadaukar da rayuwarsu, suka tallafa wa al’uuma da damar da suka samu, domin kowa ya san Sardauna da ayarinsa ba su yi hada’u da dukiyar al’umma ba, bayan gushewar Sardauna ba a sami wadanda suka zama jagororin arewa irinsa ba, sai dai ma su amfani da sunansa domin biyan bukatun kansu.

A karshe, me ka ke son al’ummar arewa su lura das hi, domin ci gaban arewan da kuma al’ummar arewan ?
Ai su yi domin Allah, kamar yadda Sardauna ya yi, domin kowa ya san matsalolin day a fuskanta, a dalilin kishin day a ke domin ci gaban arewa, sai su tashi tsaye, domin yin koyi da shi a bayyane ba a boye ba, ta haka sai a sami ci gaba a arewa, su kuma su yi mutunci ga al’ummar arewa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!