Connect with us

TATTAUNAWA

Sheikh Abdulhakami Ya Shawarci Malaman Jihar Kaduna A Kan Shiga Harkokin Siyasa

Published

on

Tun daga lokacin da aka kammala zaben shugaban kasa da kuma na majalisun tarayya da kuma na wakilai a tarayyar Nijeriya, a jihar Kaduna sai wani sabon salon siyasa ta bayyana na yadda wasu ‘yan siyasa da suka tsunduma takara suka suka fara amfani da wasu malamai da nufin samun mafita ga zabubbukan da suka shiga.
Batutuwan da malaman ke furtawa a fili ya na nuna inda su kansu suka karkata, wanda wannan ne ya zama silar zunden da ake yi wa ire–iren wadannan malamai, na cewar, sun karbo kwangila ne a fakaice daga wadannan ‘yan siyasa.
Fitaccen malamin nan da ke Zariya a jihar Kaduna kuma masanin shari’ar musulunci mai suna Sheikh Abdulhakami Muntaka Kumasie ya jawo hankalin ire –iren wadannan malaman na yadda suka dora wa kansu wasu ayyuka da mai duka bai dora su a kai ba zantawarsa da ya yi da wakilinmu da ke Zariya Balarabe Abdullahi. Ga yadda tattaunawarsu ta kasance:

Wasu malamai takwarorin ka na sifanta siyasar dimukuradiyyar da ake ciki da cewar ta addinin musulunci ne, me malam zai ce kan wannan batu ?
Babu ko shakka dimukuradiyyar da ake yi a Nijeriya a yau bai kama da siyasar musulunci ba, domin duk dokokin da ake aiwatar da dimukuradiyyar mutum ne ya tsara su, ba mai kowa mai komi ya tsara sub a, kuma tsare –tsare ko kuma dokokin dimukuradiyyar bai yi kama da Alkur’ani mai girma ba baki daya.

A yau an wayi gari, wasu malamai na aibanta duk wanda bai rungumi wannan dimukuradiyyar ba, musamman wani dan takara na musamman da malamai ke furtawa , cewar mutum ba musulmi ne ba kuma bai yi wa musulunci aiki ba ?
Alal hakika, duk wani malami da ya bayyana wannan ya tafka kuskure, kuma kuskuren da sani aka yi shi, domin duk wanda ya furta wannan batu, ya na da wata boyayyiyar manufa a gefe guda, in malami ya yi aikin da musulunci ya ce, ya kuma yi, to za a iya ce ma da madalla, in kuma ya yi akasin haka, jama’a ne za su yi ma sa rajamun Magana dare da kuma rana, wanda wadannan maganganun da za a furtawa malamin, zai zubar ma sad a mutunci a bayyanar jama’a, domin an gano inda ya taso da kuma inda ya nufa.

Wani nau’in dan siyasa ne ya dace al’umma su zabe shi?
To siyasa irn wanda ake yi a yau a Nijeriya, tamkar ka ce ga farfesu ne kan tebur, ga rowan sanyi da za a sha in ana shan farfesun, amma farfesun a kwai naman rago da nan alade da kuma kare aka hada wannan farfesu, to ya dace kai musulmi ka dauki matakin da ya dace kafin ka yanke shawarar shan wannan farfesu.
Kuma da musulmi da wanda ba shi da addin da mace da , duk suna da damar shiga siyasar Nijeriya, sai dai ya na da kyau musulmi ya yi taka tsan–tsan kafin ya yanke hukumcin zaben wanda zai zaba, tun da Allah ya cusa ma sa hankali a jikinsa, ko da kuwa wani malami ya bayyana wani abu sabanin abin da Allah ya ce a lokacin da za a zabi shugaban al’umma ako wane mataki na siyasa.
Ka da mu manta Sarkin Habashi Kisra, ba nusulmi ba ne, amma a mulkinsa ya tallafa wa musulmi dama da kuma mafaka na ka da a kasha su, ka da kuma a cutar da rayuwarsu, don haka mu dubi wannan gajeren kissa, kuma a lokacin da Kisra ya yi abin da aka bayyana, Annabi Muhammad [S.A.W.] ya san an yi, bai kuma yi hani ba, don haka in an sa kirista a cikin siyasa ba laifi ba ne.
Kuma ka da a manta da Bilkisu da Annabi Suleman ya aura, asalinta ba ma ba ce, ta kuma shiga sha’anin mulki, ta yi abubuwa na kasaita, har said a suka kai rana suke bauta wa, ubangiji ya yi ma ta rahama, ya kuma ta auri Annabin Allah.

A yau a jihar Kaduna wasu malamai na cewar, wancan siyasar ta musulmi ne waccan kuma ta kirista ne, me malam zai ce kan furucin da ke suke fitowa daga malamai ?
In har kamar yadda ka ce wadanda suka fadi wannan Magana malamai ne, to kamar sun sa son rai ne, domin biyan bukatunsu na boye, domin Shaddadu Bini Yusufus sakafi, babban mutum ne, ya shiga cikin musulunci, musulmi ne, ya yi yaki, ya kuma kasha mutane, ya na shan giya ya na caca ya na zina, amma in kirista ne, to ai Ahalal kitabi ne,ya dace wadanda ke kiran kansu malamai su gane kirista su gane bayahude da kuma Ahalal kitabi, domin in an fahimci haka an sami sauki, domin shi ahalin kitabi ne, kuma ahalin kitabi an yadda nusulmi su zauna tare da su, mu ci abincinsu mu kuma ci yankarsu.

A siyasance in ire–iren wadannan batutuwa suka ci gaba da fitowa daga bakin malamai, an ya ba za a sami matsalar da aka fita a jihar Kaduna ban a matsalolin rikicin da ake sifanta shi da addini ?
To, ya dace wadanda ke kirar kansu malamai su fahimci kifiri fa daban, ahalin kitabi kuma daban, mushiriki daban , yahudu shi ma daban, nasara daban kuma musulmi daban,ya zama wajibi malami da sauran al’umma su san wannan, musulunci ya yadda mu ci abincin kirista, domin su ahalin kitabi ne,ni har yau fiye da shekara hamsin ina da aboki kirista, kuma ga abin da Allah ya ce a tsakaninmu da su, to in wata siyasa ta dauki kirista ta sa shi a gabanta, sai a ce malamai ka da su yi?

A karshe, wani shawara za ka ba malamai ma su gwara kwakwalen al’umma a yau, musamman a jihar Kaduna ?
Da farko mu tuna fa ubangiji ya umurce mu da cewar lallai ne mu guji tayar da fitina, domin in fitinar ta tashi, ba za ta tsaya kan wanda ya tayar da ita ba, za ta shafi musulmi da kirista da ma wanda ba shi da addini,to sai malamai da suke furta son ransu, su fahimci ayyukan da mai duka ya dora ma su, kuma ayyukan suna nan a Alkur’ani da hadisai da sauran litattafan musulunci, kuma karatu da al’umma ke yi ne a yau, su ke gane malamin da in ya je mararraba, yak e bin hanyar day a ke so, ba hanyar da Allah ya ce yabi ba, ko kuma hanyar da aka ce ya nuna wa al’ummar da suke sauraronsa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!