Connect with us

LABARAI

Zaben Gwamnoni: Shugaba Buhari Ya Nemi ’Yan Najeriya Su Zabi APC Sak

Published

on

Zaben Gwamnoni: Shugaba Buhari Ya Nemi ’Yan Najeriya Su Zabi APC Sak

Daga Nasir S. Gwangwazo, Abuja

 

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kira ga masu jefa kuri’a a kasar da su zabi ’yan jam’iyyarsa ta APC daga sama har kasa, domin hakan ne kadai zai taimaka ma sa wajen hanzarta cimma burinsa na ‘Next Level’.

Shugaban ya bayyana hakan ne ranar Laraba a sakonsa ga ’yan Najeriya kan zaben da za a gudanar ranar 9 ga Maris, 2019 na gwamnoni da ’yan majalisun jihohi a dukkan fadin kasar.

A cikin sakon bidiyon mai mintuna 3:35, wanda ya fitar a kafofin sadarwarsa na yagar gizo yau Laraba da yamma ya ce, “a matsayina na dan jam’iyyar APC, Ina mai gabatar da ‘yan takararmu gabadaya gare ku, domin idan ku ka zabe su, mu na da kyawawan manufofi da akidu managarta na cigaba, wadanda kuma ba za mu ba ku kunya ba.”

Buhari ya ce, “a yayin da manyan zabukan karshe na 2019 ke tafe ranar 9 ga Maris, ‘yan Najeriya za su zabi gwamnoni da ’yan majalisar dokoki na jihohi, Ina mai mika sakon ta’aziyyata ga iyalin wadanda su ka rasa rayukansu da wadanda su ka ji raunuka a dalilin hatsari ko aikata wasu miyagun laifuka a lokatun zabe.”

Shugaban sai ya kuma yi kira ga ’yan kasar kada su yi kasa a gwiwa wajen fitowa zaben, inda ya ni da su yi fitar farin dango a cikin nutsuwa da kwanciyar hankali ba tare tayar da zaune tsaye ba su kada kuri’unsu, ya na mai cewa, dukkan zabubbukan su na da amfani kamar yadda na shugaban kasa da ‘yan majalisar tarayya su ke da shi.

Sai ya yi kashedin cewa, kada a karya dukkan dokokin zabe, domin ya na mai tabbatar da cewa jami’an tsaro su na nan a ko’ina don kare masu kada kuri’a, ya na mai fatan cewa, zaben gwamnonin zai fi na shugaban kasa nagarta har a wajen masu sa ido daga kasashen duniya.

“Ina nan a kan wannan alkawari. Mu yi kokarin ganin mun aikata abinda ya kamata, domin a zabi nagartattun shugabannin da za su taimaka ma na wajen kai wa ga mataki na gaba (Next Level),” a cawar Shugaban Najeriya Buhari.
labarai

Share This

Share this post with your friends!