Connect with us

TATTAUNAWA

Alarammomi Sun Amfana A Gwamnatin Ganduje – Tafidan Gwagwarwa

Published

on

Alhaji Ibrahim Safiyanu Tafidan Gwagwarwa Shi ne Babban Daraktan Hukumar Zakka da Khubusi na Jihar Kano, guda cikin ‘yan Gwagwarmayar tabbatar sake samun nasarar Gwamna Ganduje da Gawuna, Allurar dinke duk wata baraka da wasu makiya ke assawa tsakanin masoya Gwamna Ganduje da Gawuna. A Tattaunawarsa da Wakilinmu a Kano ABDULLAHI MUHAMMAD SHEKA Hon. Ibrahim Safiyanu Tafidan Gwagwarwa ya bayyana kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin wannan Gwamnati da alarammomi na hakika masu tsangaya, haka kuma ya yi tsokaci kan gobarar da ta afakwa Jam’iyyar PDP a Jihar Kano. Ga dai yadda tattaunawar ta kasance.

Za mu so ka gabatarwa da mai karatu kanka?
Alhamdulillahi da farko da sunanan Ubangiji mai kowa mai komai, tsari da amincin Allah su kara tabbata ga fiyayyen halitta Annabi Muhammadu SAW. Kamar yadda aka sani ni sunana Ibrahim Fafiyanu Gwagwarwa kuma ni ne babban daraktan Hukumar Zakka da Khubusi ta Jihar Kano ahalin yanzu.

Shin ko me zaka ce yanzu da ake gaf da gudanar da zaben Gwamna da kuma ‘yan Majalisar dokokin Jihar Kano?
Muna yi wa Allah godiya wanda kullum shi ne abin godiyarmu kuma shi ne jagoranmu aduk al’amuran wannan Gwamnati, kamar yadda kowa ya sani saura kwanki kadan suka rage a gudanar da zaben gwamna da kuma ‘yan Majalisar Dokoki a fadin kasar nan. Kamar yadda aka sani siyasar Jihar Kano ke zaman fitilar dake haske alkiblar siyasar kasar nan. Kuma alhamdulillahi tuni ‘yar manuniya ta nuna idan akayi la’akari da zaben shguaban kasa da na ‘yan majalisar Dattijai da na wakilai a fadin kasar nan, Jihar Kano ta kare kambunta domin itace kamar yadda Gwamna Ganduje ya sha ambatawa Jihar Kano ce ta baiwa shugaban Kasa Mujammadu Buhari Kuri’un da suka zarta na daukacin Jihohin Najeriya.
Saboda haka yanzu haka shirye shirye sun kammala al’ummar Jihar Kano ranar Asabar kawai suke sauraro domin fita domin yiwa Jam’iyyar APC luguden Kuri’a, kowa ya sani Jihar Kano Gwamna Ganduje da Gawuna ake kuma shi za’a zaba da sauran ‘yan Majalsun dokoki baki daya kwata.
Jama’a sun gamsu kwarai da gaske anga irin kabakin arzikin da wannan gwamnati ke kwararawa Kano da Kanawa, wanda a fadin kasar nan babu wani Gwamna da ya ko da kama kafar Ganduje wajen isar da romon demokaradiya ga al’ummar da suka amince da jagorancinsa. Amma baka ganin irin shirin da Jam’iyyar adawa ta PDP ke yi na ganin takwace wannan mulki daga hannunku?

Kamar ya rabon gadon ta ake Darakta?
Kana gani yau kwana biyu kenan Mai Girma Gwamna da Mataimakinsa Dakta Nasiru Yuisif Gawuna suka karbi daukacin shugabannin Jam’iyyar PDP guda 12 daga cikin 14 tare da dubban magoya bayansu inda suka yar da Kwallon magoro suka hutu da kuda. Cikin wanda aka karba akwai shugaban Jam’iyyar PDP na hakika Mas’ud Doguwa, ga tsohon Kakakin Majalisar
wakilai ta tarayya Imam Buhari, Yahaya Bagobiri da sauran jigajigan Jam’iyyar ta PDP. Wannan tasa na fada maka tuni PDP ta mutu a Kano har an yi rabon gadonta. Kuma ina tabbatar da maka ka ga shirin nan na mai girma Dakta Nasiru Yuisf Gawuna Na Operation Tsamar Nama ba zai bar sauran kowa cikin Jam’iyyar PDP ba yanzu haka ma ta zama kango. Amma mantawa kayi da Limamamin Kwankwasiyya wanda ana ta jin motsinsa a Jam’iyyar PDP har ma yana tabbatarwa da magoya bayansu cewar dan takararsu ne zai lashe wannan Zabe?
Su wadanan ai ba ‘yan PDP bane ‘yan kungiya ne kuma Gwamnatin Ganduje da Gawuna sun yiwa PDP tunbur balle wata kungiya, yanzu ai shure shure kawai Kwankwaso ke yi an rufe shafin siyasar sa baki daya, daga wannan zabe sai dai ya koma inda ya fito ya ci gaba da zaman defot. Mu a Jihar Kano mun san mai kaunarmu wanda baya rigima da malamai magada annabawa. Kuma kowa yasan kyakkyawar tarbiyyar Gwamnana Kano da kuma cikakken ilimin addini, wannan ta sa kullum malamai ke sa masa albarka.

Amma Darakta kwanannan aka ji wata tawagar Malam da kake magana sun ziyarci Kwankwaso tare da mika masa wilayarsu?
A’a masu bukata dai sun je domin neman na kalaci, amma malamai na hakika tare suke da Gwamna Ganduje, kuma muna da kyakkyawar alaka da su, abin da mai girma Gwamna da mataimakinsa suka sani shi ne malamai mutun ne mai kima don haka ba sosai ake jinsu a cikinj harkokin siyasa tsundun ba, amma kuma wannan bai hana su bayyana ra’ayinsu ba, kamar yadda jama’a shaida ne rukunin malamai masu daraja da kima kulluma suna kara jadadda amincewarsu da wannan jagoranci na Ganduje da Gawuna.

Mene zai tabbatar wa da mai karatu wannan batun naka?
Alhamdulillahi nasan dai duk wanda ya san Jihar Kano Jiha ce data yi shura ta fuskar harkar malanta kuma a Kano Bujaman Malamai suke masu daraja, na san kaji wasu kamar yada ka ambata sun ziyarci wancan Jam’iyyar data zama mushe, kuma bayan fitar sakamakon wancan ziyar kaji rukunin Alarammomin da suka bayyana wanda basa sukar kowa, amma
suna bayyana nasu ra’ayin, kuma kasan dai alaramma shi ba dan nanaye ba ne daman idan kaji sun yi Magana karshen tuka tiki tuk, yanzu haka alhamdulillahi kowa shaidai ne kafin fara kada kuguen siyasar da muke a halin yanzu daman alarammomi na Gawuna ne.
Ina tabbatar maka kaunar da ke tsakanin Mataimakin Gwamna da Majalisar Mahaddata Alkur’ani ta jima tun yana shugabantar karamar Hukumar Nasarawa, shi ne wanda ya damkawa alarammomin kantareriyar Mota, sannan kuma shi ne jagoran da baya hada lokacin kowa da na ahlullahi, komai nasu dabanne, haka kuma ina tabbatar maka da cewar hakan ya samo asali kasancewarsa shi masanin Akur’ani ne kuma daga gidan Alkur’ani ya fito, al’adar Alarammomi kuma suna tare da duk wanda ke kaunar Alkur’ani da ahlinsa.

An ya Darakta kusan irin shirin da wancan bangaren ke yi na ganin sai sun karbi wannan kujeru daga hannunku?
Har dariya ka bani wai yaro ya tsinci hakori, bari na tuna maka Zamani kowa da nasa, kamata ya yi wancan bangaren su gamsu da cewa suma Allah ya ara masu rana kuma sunyi abinda suka yi mai kyau ko akasin haka, don haka wannan lokacin tuni Kanawa suka dawo daga rakiyar shugabannin daure al’umma da igiyar zato. Abinda na ke so kowa ya fahimta, tun daga lokacin da jagoran waccan kungiyar ya daga daga Kano zuwa Abuja a matsayin wakilin al’ummar Kano ta tsakiya sau nawa ya shigo domin gudanar da wani taro ko kaddamar da wani aiki da ya kawowa yankin da yake wakilta cikin shekaru uku da doriya da ya shafe akan wannan kujera.
Yanzu ya tabbata kuma anyi walkiya jama’ sun gansu, kaji yadda kotu ma ta yanke nata Hukunci wanda hakan ya tabbatar da basu da wata nasara, amma har yanzu jagoran gangan din yana nan yana ci gaba da daure su da igiyar zato. Amma dai alhamdulillahi jama’a sun fahimci wannan Gwamnati Karkashin Gwamna Ganduje musamman idan aka dubi irin ayyukan da ake kwrarowa Kanawa.

Ya Kake kallon yadda zaben asabar din zai kasance bisa harsashen ka?
Wannan al’amari ne na Allah amma ina tabbatar maka da cewa ko iyakar abinda wannan Gwamnati ke yiwa Alarammomi, ga kuma yadda ake bayar da tallafi iri daban daban, kaddamar da manyan ayyuka, inganta asibitocinmu, samar da tsaftataccen ruwan sha, inganata harkar tsaro, hanyoyi da gadoji, tallafin harkar noma da sauransu, ko a iya wannan Kanawa sun gamsu da karawa Gwamna Ganduje zango guda domin ci gaba da ayyukan alhairin da yake shimfidawa a Jihar Kano.

Menene sakonka ga al’ummar Jihar Kano?
Alhamdulillahi sakona bai wuce fara mika godiya ga Allah ba da ya baiwa Gwamna damar sauke alkawurran da ya dauka alokacin yakin neman zabe, sannan kuma gashi wani abun al’ajabi harda karin abubuwan da bai ma yi alkawarinsu duk an aiwatarwa Kano, Saboda haka kamar yadda bahaushe ke cewa yaba kyauta tukuici wannan tasa muke kara jadaddawa jama’a bukatar ranar asbar mai zuwa a fito kwai da kwarkwata domin yiwa Jam’iyyar APC luguden Kuri’u domin karasa kai keyar masu adawa da ci gaban da Jihar Kano ke samu ahalin yanzu.
Haka kuma muna kara godiya ga ahlullahi bisa zabar Mataimakin Gwamna da suka yi tare da yi masa nadin Garkuwan Mahaddata Alkur’ani na Kasa wanda ake shirin gudanar nadin nan bada jimawa ba, muna fatan Allah yasa ayi zabe lafiya agama lafiya, Allah ya bamu nasara.
Mun gode
Nima na gode
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!