Connect with us

KASUWANCI

Gwamnatin Tarayya Za Ta Sayar Da Dam 6 A Fadin Kasar Nan — Fashola

Published

on

Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewar, ta kammala dukkan shirye-shirye don sayar da
Dam dinta guda shida ga ‘yan kasuwa masu zaman kansu da kuma mayar da shirin ta na BOI. Ministan wuta, gidaje da ayyuka Mista Babatunde Fashola ne ya sanar da hakan a lokacin taro karo na 29 na masu ruwa da tsaki a fannin wutar lantarki da aka gudanar
Minna cikin jahar Neja, inda ya ce, manufar itace don a baiwa cibiyoyin ilimi da ‘yan kasuwa dama dake cikin kasar nan. Fashola yaci gaba da cewa, wannan duk tsarin gwamnati ne akan kudurin ta na kara samar da wuta a karkara da shugaban kasa ya amince da hakan a 2016. Acewar sa, “ muna nufin sayar kanan da Dam din guda shida da akayi watsi dasu shekaru da dama da suka shige don amfanin jami’oi mallakar gwamnatin tarayya da ‘yan kasuwa, inda gwamnatin ce zata dinga bayar da daukin kudi kai tsaye, sabanin zargin da aka dinga yi a wasu kafafen yada labarai, kuma ina kalubalantar wadanda suke yin zargin dasu bayar da kwararriyar hujja.
Abewar sa, a yanzu haka akwai kasuwanni sha biyar da ake shirin kammalawa tare da, Ariaria, Sabon Gari da kuma kasuwar Sura dake Aba, Kano da kuma Legas a matsayin yin gwaji. Ya kara da cewa, akan kasuwanni kuwa shaguna guda 37,000 dake Ariaria, da kuma kimanin13,000 a Sabon Gari da kimanin 1,000 a Sura sun wakilci matsakaitan sana’oi ganin cewar, mafi yawancin alummar mu a nan ne suke samun kudin shigar su kuma a gefe daya, kamfanin samar da wutar lantarki na DISCOs babban kalubalen da yake fuskanta shine na samar da wuta. A wata sabuwar kuwa, duk da barazanar da kamfanin samar da wutar ya yi a kwanan baya a kan samar da wutar, Fashola ya kara jaddada cewar, kamfanonin samar da wutar sune suke kawo cikas akan samar da wutar a kasar nan. A karshe ya yi nuni da cewar, manyan kalubale a tsarin samar da iskar gas sun hadada, yadda za ‘a Samara dashi da tura shi ganin cewar a yankin akwai megawatts data kai yawan 2,000, sauran kalubalen kuma sune, tura mitocin wuta zuwa ga masu amfani da wutar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!