Connect with us

MAKALAR YAU

Damar Da Atiku Ya Rasa A Fagen Daga

Published

on

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, kuma Dan takarar Shugabancin Kasa a karkashin inuwar Jam’iyyar PDP a zaben da ya gabata na 23 ga watan Fabrairu, 2019, Alhaji Atiku Abubakar ya kyautu a ce ya rungumi kaddara ya yarda ya fadi zabe, wa-salam-wa-kitabihi. Ko shakka babu da ya yi hakan, da ya kara daga darajar Nijeriya a idon duniya musamman a kan harkar da ta shafi Demokradiyya, ya kuma samu girma da daraja a idon mutanen wannan kasa kamar yadda Tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya samu a zaben 2015, da ya zama Shugaban Nijeriya na farko da ke kan kujerar mulki ya kuma amince da faduwa zabe.

Alal hakika, rashin bin sahun Jonathan na rungumar kaddara da Atikun ya ki yi, ya kawo mana koma baya a harkar Demokradiyya a wannan kasa, ya kuma kawo wa shi kansa Atikun koma baya a sha’aninsa na Siyasa. Ko tantama babu, zabin da Dan takarar na PDP ya yi na yunkurin zuwa Kotu, ko kadan bai saba wa shari’a ba, bai kuma zama aibu ba. Dalili kuwa, hakan na daya daga cikin shika-shikan Demokradiyya na baiwa mai korafi cikakkiyar dama da ikon shigar da kara idan bai gamsu da sakamakon zaben da aka aiwatar ba ko wani abu makamancin haka. Shi yasa ya fi kyautuka mai korafi ya shigar da kara Kotu, ba ya dauki doka a hannunsa ko nema wa kanka da kansa mafita ba. Kazalika, irin rawar da Jonathan ya taka a 2015, na yarda da kaddarar faduwa zabe ne yasa aka yi wa ‘Yan Nijeriya musamman masu zabe a 2019 kyakkyawan zato na sake fitowa su zabi irin Shugabannin da suke so su mulke su. Tsohon Shugaban Jonathan a hakikanin gaskiya, ba karamin daga darajar Demokradiyyar wannan kasa ya yi ba, inda aka rika tsammanin wannan zabe na 2019 zai dora a kan wancan da ka iya sanya Demokradiyyar Nijeriya zuwa kokoluwa a fadin duniya baki daya. Idan aka yi la’akari da haka, Atiku ko kadan bai yiwa Nijeriya adalci ba, bai kuma taimake ta ba samsam. Don haka dole wannan ya bakanta wa duk Dan Nijeriya, saboda dama ce muka rasa sannan kafatanin duniya na kallon mu.

Duk duniya babu inda ake aiwatar da halastaccen zabe dari bisa dari. A tambayi tsohon Shugaban kasar Amurka AI Gore da Hillari Clinton, dukkanin su tsofaffin ‘Yan takarar Shugabancin kasa ne karkashin Jam’iyyar Democratic Party a kasar Amurka. Haka zalika, idan muka dawo gida Nijeriya karkashin jagorancin Uban gidan Atiku, tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo, murdiyar zabe da sata da kuma kama-karya sai da suka zama ruwan-dare babu ruwansu da kula da hakki ko ‘yancin al’ummar wannan kasa. Don kuwa a daidai lokacin da ake tattara sakamakon Shugaban kasa na 2007 a sassan kasar nan daban-daban, tuni sai aka jiyi Shugaban Hukumar zabe ta kasa na sanar da sakamakon zaben Umaru Yar’Adua a matsayin wanda ya lashe zaben, wanda hakan ba karamin abin kunya da rashin daraja ba ne har a wajen masu mulkin.

Har ila yau, zaben da aka yi na 2003 karkashin Obasanjon, duk sammakal babu wani canji illa magudi da murdiya. Chuba Okadigbo, mataimakin Dan takarar hamayya a wancan lokacin, sai da aka hana shi fita ya ya kada wa kansa da kansa kuri’a saboda motocin yaki na Soja da aka girke masa a kofar gida kamar wani Dan fashi da makami, aka kuma ja kunnensa cewa idan ya kuskura ko shi ko daya daga cikin iyalinsa suka yi yunkura fita daga cikin gidan, duk abinda ya same su su suka saya. Haka nan, irin abinda ya faru kenan lokacin da Hukumar INEC ta sanar da cewa Jam’iyyar Atiku ta PDP ta kayar da tsohon Gwamnan Legas Bola Tinubu, a matsayin Gwamnan Jihar tun kafin ma a kai ga aiwatar da zaben. A dai wannan shekarar ne Farfesa Jibril Aminu ya fadi zabe a matsayinsa na Dantakar Sanata a Jam’iyyarsa ta PDP a Jihar Adamawa, amma wannan Atikun ne dai ya fusata ya ji haushin Farfesa cewa, me yasa ya yarda ya fadi? ba tare da wani bata lokaci ba ya sa aka sake canza alkaluman zaben aka ce Jibril Aminun ne ya lashe zaben. Haka Farfesa Aminu ya kwashe tsawon shekaru hudu a majalisa, duk da cewa ya san ba shi ne halastancen Sanatan ba. Wannan sakamako irin na Farfesa, daya ne tak cikin irin wanda Gwamnatin Obasanjo da Atiku suka yi ta faman karfa-karfa suka rika sauyawa ba tare da la’akari da abinda al’umma suka zaba ba.

Haka nan, ko a wadannan zabubbukan da aka kammala kwanan nan, akwai zarge-zarge da dama akan ita kanta Jam’iyyar ta PDP na yunkurin aikata magudin zabe kuma kafatanin duniya kaf na da yakinin za su iya aikatawa. Abin haushi da takaici maimakon Atikun ya fara daukar matakin Shari’a, sai Lauyoyi suka ci gaba da tunzura shi don neman hanyar da za su ci gaba da samun abin na sawa a aljihu, wannan kadai idan muka kalla ya isa mu gane cewa, Atiku ba kasar nan ce a gabansa ba, illa bukatun kashin kansa. Don haka, Atiku bai yi abinda ‘Yan Nijeriya suka yi tsammani ba, kuma ko shakka babu ya ba su kunya!

 

 

 

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!