Connect with us

TATTAUNAWA

Zan Kashe Kaina Muddin Gwamnatin Bauchi Ta Ki Biyana Kudin Giratutina, in ji Alhamdu

Published

on

ALHAMDU B.  DAN’AZUMI Wani tsohon malamin makaranta ne wanda ya shafe shekaru 35 yana koyarwa a karkashin ma’aikatar ilimi ta Ningi da ke Bauchi, ya sha alwashin cewar muddin gwamnatin jihar ba ta biyashi kudin giratuti da na fansho da yake binta ba zai kashe kaisa muddin ranar Juma’a (Yau) ta yi ba a bashi kudinsa ba. kodayake ya so ya kashe kansa din ma tun a ranar Litinin a ofishin NUJ da ke Bauchi inda aka dakatar da shi, yanzu ya sha rantsuwar cewar zai kashe kansa zuwa yau Juma’a, a bisa haka ne KHALID IDRIS DOYA ya zanta da shi domin jin dalilinsa na daukan wannan mummunar matakin, ga hirar:

Ka bayyana min sunanka da inda ka fito?

Sunana Alhamdu B. Dan’azumi, na zo nan ne daga karamar hukumar Ningi ta jihar Bauchi. Nine shugaban masu dauke da cutar nan mai karya garkuwar jikin dan adam (HIB) a karamar hukumar Ningi, kuma nine mataimakin Sakatare janar na kungiyar masu dauke da cutar a matakin jihar Bauchi gaba daya.

Mene ne ya kawoka cibiyar ‘yan jaridu da ke Bauchi?

Na zo nan cibiyar NUJ ne domin a nan ne kawai zan bayyana kukana kuma a ji, na bayyana damuwar da ke cikin zuciyata wanda har hakan zai kai a taimaka min ko a ki taimaka min, amma ina da kyakkyawar zuciyar cin cewar ubangiji zai shige gaba na samu waraka kan damuwata.

Abun da ke damuna gaskiyar maganar ina cikin mawuyacin hali, damuwowi sun yi min yawa, yanzu haka basussuka sun yi min yawa a sakamakon dauke da cutar HIB da muke mafa da shi kusan shekaru 20, na sha wahalhalu na jinyace-jinyace sosai a rayuwata, don haka kudaden mutane sun yi ta hawa kaina tsawon shekaru na gagara biyansu. Sannan kuma, tsautsayi ya samu ‘yata, na yanka gidana na mika ga wani domin ya bani kudi da tunanin zan zo in fanshi kana nan gaba shi ma yanzu yana nan hakan, na kuma aurar da ita wannan ‘yata din wacce ta samu matsalar ido a shekarar 2011 yanzu haka ko taburma guda daya ban yi mata ba. ni ba ma wannan ba, bashin mutane ne da ke kaina na tsawon lokaci in samu in biyasu, kudaden da ake bina a takaice ya kai wajen dubu dari takwas 800,000 gaskiya ina cikin mummunar rayuwa, don haka ina son kawai na samu walwala, wannan zancen da nake yi da kai layuka da yawa bana iya yawo a ciki a sakamakon kudaden mutane da ke kaina, yau kwanana 31 rabuwana da Ningi ina gudu ne domin kada su ganni, tsakanina da su sai dai waya, kuma na fada musu cewar a ranar Juma’a ina zuwa zan dawo, don haka zan koma Ningi ranar Juma’a.

Abun da ya sa na sanya ranar Juma’a a wannan ranar ce zan cika kwanaki 35 da barin Ningi, yanzu ina son ne ku fada wa gwamna M.A na jihar Bauchi shine gwamna na shine uba a gareni a jihar Bauchi, shi ne kuma wanda hakkina yake hanunsa, ya taimaka ya bani kudin giratuti dina da sauran hakkokina Ariyas da nake bi, domin in je in biya kudaden da ake bina, na amshi gidana da na jinginar na kuma yi wa ‘yata kayan aure dan abun da ya rage daga cikin kudin zan yi amfani da shine wajen mallakar kayan noma wanda zan ke yi domin taimaka wa rayuwata domin samun abincin da zan ke ci a gidana. Muddin hakan bai wakana ba kuma gwamnati ta ki biyana kudin giratuti dina, wallahi tallahi ina shaida maka ina shaida wa duniya cewar muddin har ranar Juma’a aka ki bani kudina to zan kashe kaina ta hanyar rataye kaina ko kuma na sha guba na mutu kawai.

Na yanke wannan shawarar ce domin domin na sauwake wa kaina dumbin damuwowin da suke kaina domin na shafe shekaru 35 ina aikin gwamnati na koyarwa na kammala aiki a bani kudina an ki a bani, na zo ina cikin damuwa, zamana a cikin iyalaina ya gagareni, uwata tana da rai yau kwanaki 31 na gagara ganin idonta, don haka kawai lallai a biyani kudina daga yau zuwa Juma’a muddin M.A ya ki biyana kudina na giratuti ya tabbatar a dalilin kin biyana kudina ya sani ya kuma rubuta ya ajiye ni Alhamdu B. Dan’Azumi zan kashe kaina, kuma duniya ta sani idan na kashe kaina ga dalili.

Hankula sun koma kan batun zaben gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi, ba ka ganin ya dace ka dan yi hakuri a kammala zaben nan sai ka kawo damuwarka?

Gaskiyar magana ni ka ganni nan? zaben shugaban kasa ma ina son yi amma ban iya yi ba a sakamakon dumbin damuwowi, ni ba zan canza muradina ba, muddin har zan kai Juma’a ban samu kudina ba kowa zai ji mummunar labari domin zan kashe kaina wannan matsayatace na zarratar babu kuma sauyi fa.

Shekarunka nawa a duniya?

Shekaruna sittin 60 a duniya, matana 3, inda ya yara shida.

Da a ina ne ka yi aikin gwamnatin har ka yi ritaya?

Na yi aiki ne da hukumar ilimi ta karamar hukumar Ningi. Ni malamin makaranta ne, na kammala aiki a shekarar 2016 watar June a ranar 30.

Ana biyanka kudin fansho?

An fara biyana fansho a shekarar 2017 a watan Afrilu, don haka ina bin bashin fansho na wata tara, wata tara na kwashe ba a biyani kudina na fansho ba.

An hana kashe kai a doka kuma a addinance ma addinai biyu Muslim da kiristanci duk sun tafi kan cewar haramun mutum ya kashe kansa kai mene naka?

Dukka na gaskata laifi ne, yanzu a hukumancen bari na fada maka muddin M.A ya sani ba zai biyani kudina ba, idan a hukumance ana ganin laifi ne to a kulle ne a daure ni kawai, muddin ba haka ba zan kashe kaina, muddin za aka barni na taka a ranar Juma’a babu kudi a hanuna zan kashe kaina.

Tun yaushe ne ka fara tunanin kashe kanka da kanka?

Tun a watan Disamba na fara wannan tunanin. Ni fa ba ina cewa a bani kyautar kudi ne ko ina neman taimako daga wani ba ne, ko shi M.A ba ina cewa ne ya bani kyautar kudi ko bashi ba ne, a’a, kudina nake son ya bani na hakkina da nake bi.

Nawa ne kudinka na giratutin da kake bi?

Ga shi ina tafiya da dukkanin takarduna a hanuna, ga kudin giratuti dina da nake bi, naira miliyan daya da dari shida da wasu ‘yan dauri, N1.6M.

Basussukan da kake ta korafin ka amsa a hanun jama’a, wai shin mene ne ka yi da su ne?

Ka ga na farko akwai jiyar da gida (iyalaina), na fada maka ni ina dauke da cutar HIB kun sani mai dauke da wannan cutar na bukatar abinci sosai, domin ni da matata da ‘ya’ya biyu dukka muna dauke da wannan cutar, don haka ka ga akwai wahala sosai a tafiyar da rayuwa ga cin abinci ga yawan jinyace-jinyace.

Wai kai baka noma ne?

A zamana malamin makaranta a Bauchi na sani akwai dalibaina a ma’aikatu da daman gaske har wasu jihohin ketare ina da dalibai, kowa ya san yadda na yi aikin koyarwa, idan za a ka ci karo da wani wanda muka yi aiki da shi ko dalibin da na koyar zai fada maka, domin ni lokacin da na yi aiki ban son hutu ba ban san ranakun hutu ba, dukka ni aiki nake yi wajen koyarwa da dalibai, babu safiya da yammaci kowani lokaci aiki nake yi, don haka bana samun lokacin wani noma, bayan lokacin hudu ina shirya wa dalibai darasi na daban, daga shekarar 1981 da na yi aiki zuwa shekarar da na bar aiki a dukkanin makarantar da na yi aiki za ka sani na koyar tsakani da Allah ba za a samu wani malamin da ya wahala kamar ni ba, na bauta sosai wa gwamnati, na koyar sosai, don haka ni ban yi noma ba, amma yanzu ina son yi, idan an bani kudina zan sayi kayan noma domin babana manomi ne.

Wasu za su ce meye sa ka kawo wannan batun daidai zabe?

Ai kawai n agama zuwa matukar kurewa ne daidai lokacin zaben, ina ruwa na da zabe, damuwata na sani a hani hakkina, an ce maka daga yau zuwa ranar da za a yi zabe shi gwamnan ba zai iya fitar da miliyoyin naira don ya ci zabe ba? to in dai zai iya haka ni ma a bani kudina, ba zan sauya ba, muddin ranar Juma’a ta wuce ba a biyani ba sakamako marar kyau zai biyo baya kowa zai ji na kashe kaina.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!