Connect with us

RAHOTANNI

Zaben 2019: An Gudanar Da Zaben Majalisun Dokoki A Jihar Kogi Ba Tare Da Na Gwamna Ba

Published

on

Duk da cewa jihar Kogi na daya daga cikin jihohi bakwai da ba a gudanar da zaben gwamna ba, saboda wa’adin mulkin gwamnoninsu bai cika ba, hakan bai hana masu kada kuri’a fitowa, don zaben ’yan majalisar dokokin jiha ba wanda a ka gudanar a jiya Asabar.
Wakilin LEADERSHIP AYAU LAHADI, wanda ya zagaya rumfunan zabe daban-daban da ke birnin Lokoja, ya gano cewa, masu jefa kuri’a sun yi fitar farin dango tunda sanyin safiya, don kada kuri’arsu ga ’yan takarar da su ka kwanta mu su a rai.
A yayin da a ka gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da lumana a wasu rumfunan zaben, wasu rumfunan kuma an samu tirka-tirka, inda wasu da a ke zargin ’yan dabar siyasa ne su ka rika bi rumfunan zaben su na sace akwatunan zabe, inda su ka rika rantawa a na kare ba tare da sun samun tirjiya ba.
Rumfunan zabe da wakilin LEADERSHIP AYAU LAHADI ya dudduba sun hada da rumfar zabe ta Inuwa Ndagana mai lamba 005 da ta Bishop Crowder mai lamba 006 da ta Amoley mai lamba 015 da ta SUBEB mai lamba 017 da kuma rumfar zabe ta Rimi mai lamba 001, inda a nan ne masu kada kuri’a su ka koka da matsalar na’urar tantance masu jefa kuri’a (Card Reader) wacce ta daina aiki
Sauran wuraren da wakilin na LEADERSHIP AYAU LAHADI ya ziyarta su ne mazabar Unguwar Kura mai lamba 006 da mazabar Attah mai lamba 005 da kuma mazabar Maiyaki Frontage mai lamba 004.
A wuraren da dama dai an gudanar da zabukan cikin tsanaki, sai dai dan abinda ba a rasa ba.
Tunda sanyin safiya ma’aikatan zaben hukumar INEC su ka kasance a mazabun da a ka tura su, don gudanar da zaben, kuma akasarin kayayyakin aiki sun isa cibiyoyin a kan lokaci, a yayin da kuma masu jefa kuri’a su ka fara kada kuri’ar da misalin karfe takwas na safe bayan jami’an zaben sun tantance su.
Har ila yau Jami, an tsaro sun kasance a kowacce rumfar zabe, don kare lafiyar masu kada kuri’a a yayin da kuma wasu jami’an tsaron su ka rika karakaina cikin birnin Lokoja da kewayenta cikin shirin ko ta kwana.
Rahotanni daga sassa daban-daban na jihar da LEADERSHIP AYAU LAHADI ya samu sun yi nuni da cewa an gudanar da zabukan na majalisun dokokin lami lafiya sai dai dan abinda ba a rasa ba na tashin hankali a wasu wuraren.
A na dai dakon samun dukkan sakamakon zabukan na majalisun dokokin jihar ta Kogi a gobe Litinin.
Jihar Kogi mai kananan hukumomi 21 na da kujerun ’yan majalisun dokoki 25 kuma ’yan takara da su ka fito daga jam’iyyu daban-daban ne su ke fafatawa a zaben. Jami’an INEC a bakin aiki a yayin da masu kada kuri’a ke kan layi don kada kuri’arsu a jiya Asabar a birnin Lokoja.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!