Connect with us

MAKALAR YAU

Hattara Dai Inyamurai (14)

Published

on

Bayan da sojoji ‘yan asalin arewa suka kama garin Abeokuta sai kuma suka je kurkukun garin inda suka fito da Donatus Okafar wanda yana cikin wadanda suka kitsa juyin mulki da aka kashe su Sardauba suka yi ta fesa masa duka sa’annan suka kashe shi. Wasu ma sun ce da ransa suka turbude shi.
A Kaduna kuwa tun kafin ranar 29 ga watan Yuli sojojin ‘yan asalin arewa suna ta jiran ranar da za a kara. In Mai karatu bai manta ba zai tuna da wasikar da su Sani Abacha suka aikawa Murtala Mohammed da Janar Yakubu Gowon. Bayan wannan kuma in Mai karatu zai iya tunawa da lokacin da Hassan Usman Katsina ya je Ikko aka kama cewar Ironsi ya tsare shi wanda ya sanya sojoji ‘yan asalin arewa suka kewaye filin jirgin saman Kaduna suna jiran a turo wani su gama masa aiki sai ga Hassan Usman ya dawo lafiya lau. Ganin irin halin da ake ciki Hassan Usman ya cewa dogarinsa Lt Ugokwe wanda ya ke Inyamuri da kada ya fara fita don kada a kashe shi.
A wannan lokacin kwamandan sojojin Kaduna Lt Col W. Bassey yana hutu. Wanda ke rike da wajen shine Lt Col Phillip Effiong shi ma ba ya nan. Shi ma Hassan Usman Katsina ba ya nan, babu wanda ke nan sai Samuel Ogbemudia mutumin Benin wanda ba Inyamuri ba ne kuma ina tsammanin babu ruwansa cikin abin da aka yiwa Sardauna. Wannan mutun ya fara ganin take-taken rigima a lokacin da Lt Bukar Suka Dimka dan asalin jihar Filato wanda a lokacin ya shawu ya yi tatul da giya ta nuna masa karya yana kokarin balle rumbun makamai. Kuma an fada wa Samuel Ogbemudia cewar an gan shi yana kai sakonni a gidajen sojoji ‘yan asalin yankin arewa. Wannan ya sanya ya bayar da umurni aka kame shi aka sakaya. Bayan da giya ta sake shi aka bincike shi amma ya ce shi ba ya nufin komai kuma ya ce an yi masa haka ne kawai don yana dan arewa. Bayan wani lokaci aka sake shi. Bayan wannan ne kuma aka sake kaiwa Samuel Ogbemudia rahoton cewa a lura da sojoji ‘yan asalin arewa suna yawan gilmawa a runbun adana makamai wadanda su ma aka kamo su aka tsare.
A wannan lokacin ne aka aiki Lt Col Aledander Madiebo Kaduna ana sauran minti goma (10) a kama inda ya ke shugabanta aka kuma mamaye filin jirgin saman Ikko. Wannan mutun ya yi iyakar kokarin kauce wa arewa don kada wannan bala’i ya faru yana can sai kuma ga shi ya fada cikin tarko. Abin da Madiebo ya fara yi yana sauka a Kaduna shine ya binciki wane hali Ikkon da ya baro ta ke. Wanda ya samu yana kulawa da signa shine Martin Adamu kuma dan arewa ne. Shi kuma Martin ya ce masa kada ya damu babu abin da ke faruwa sai alheri, amma sam wannan magana ba ta shiga kunnensa ba don ya na ji a jikin cewar akwai magana. Saboda haka sai ya baiwa Samuel Ogbemudia shawarar cewar a raba sojoji da makamai baki dayansu sa’annan a sanya sojoji ‘yan asalin arewa da ‘yan asalin kudu su tsare don kada a samu wata hatsaniya.
Wannan shirin ya ci nasara a wasu wurare amma a wasu wuraren abin bai yi nasara ba don a bataliya ta uku da ke Kaduna ba su yarda da wannan ba. Shugaban wannan bataliya Inyamuri ne mai suna Lt. Col I.C. Okoro kuma sojan da ke karkashinsa sun tabbatar masa da cewar babu abin da zai faru sai ya yarda da maganarsu.
Kamar yadda Samuel Ogbemudia ya bayar da bayani a littafinsa cewar an fara wannan rana lafiya lau kuma komai na tafiya daidai amma zuwa hantsi labari ya fara canzawa inda aka fara samun labarin abubuwan da ke faruwa kudancin Najeriya amma babu tabbacin su wane ne suka kai hari tsakanin ‘yan arewa da Inyamurai a wannan karon.
Ganin yadda abubuwa suka kasance ya sanya Madiebo ya bugawa Lt col Ogbugo Kalu waya don ya samu sahihin labari. Yana samu ya ji abin babu tabbas sai ya tara sauran manyan sojoji ‘yan asalin kudancin kasa suka yi taro a gidan Effiong amma shi Okoro bai je ba.
A cikin dare aka fada wa Inyamurai inda ka fara Bismillah da wani mai suna Kyaftin I.U Idika. Daganan sai Okoro kuma wasu suka ce Lt Col Dimka ne ya kashe shi, shi da Sani Abacha.
Daganan kuma aka shiga kamo wadanda suka yi ta murna a lokacin da aka kashe Sardauna har suna shagali. A wancan lokacin akwai ‘yan arewa da suka je bikin amma a matsayin ‘yan rahoto inda suka fadi duk wadanda suke wajen da kuma abin da kowannensu ya yi aka hake su yau kuma aka yi ta kashe su. Amma kafin a kashe su sai da aka tara su aka kawo hoton marigayi Sardauna aka ce kowane ya rusuna ya gaida hoton. Suna rusunawa ne ake gama musu aiki.
Kamar yadda shi Madiebo ya fada a cikin littafinsa na wannan rikici ya ce an kai shi masauki sai ya yi sallama da mai gadinsa ya ce masa ya zo da wuri ya dauke shi. Yana ganin wannan mai gadi ya kauce sai ya samu wata kwana ya antaya da gudu inda ya je gidan wani abokinsa daganan aka sake masa kama aka fitar da shi Kaduna a boye. Da haka har ya isa Makurdi inda ba a san shi ba ya wuce sojoji bayan da ya nuna shi ma yana goyon bayan abin da ke faruwa watau yana fadin power north.
Sauran kuma watau Kalu da Okon da Ogbemudia da Olusegun Obasanjo duk sun samu tserewa amma fa sun tsallake rijiya ne da kundun baya. Shi dai Obasanjo har Maiduguri aka kai shi aka boye shi. Shi kuma Ogbemudia Abba Kyari ya taimaka masa shi da Hassan Usman Katsina inda suka fada masa tun da wuri ya kawar da jiki don a lokacin B.S Dimka ya tara abokansa suna nemansa don rufe shi a wakafi da ya yi kwanakin baya. Daganan ne suka kawo masa motar land rober ba tare da ya samu daukar komai ba ya karbi tikiti a hannun kare.
Daganan ko su Dimka suka bi shi har zuwa Kwantagora inda ya tsaya yana kara mai. Haka suka rika binsa sun harbi amma cikin yardar Allah harsashinsu bai kai inda ya ke ba. Haka suka yi ta binsa har cikin garin Owo na jihar Ondo ta yanzu sa’annan mai ya kare wa motar shi kuma ya watsar da motar ya shiga daji ya kama gudu. Da suka bincika ba su gan shi ba sa’annan suka juyo suka kyale shi. Shi kuma da ya ji an sarara ya sake komawa kan hanya inda ya samu wani mai mota ya taimaka masa ya iyar da shi garin Benin ya isa gida yana haki. Ko a can gidan ma sai ya samu wani wuri ya labe kafin kura ta kwanta.
Can kuma a bataliya ta biyar da ke Kano wadda ke karkashin Lt Col Muhammadu Shuwa duk lokacin da ake ta wannan ruguntsumi babu abin da ya faru sai a cikin dare aka kashe Inyamurai guda uku (3) da wani dan yankin Benin guda. Daganan kuma ba a kara samun wata hautsini ba sai a cikin watan Satumba wanda aka kashe sojin Inyamurai a filin jirgin saman Kano.
Ita kuma Benin babu abin da ya faru a wannan ranar ta 29 ga watan Yuli 1966 har ma yara ‘yan makaranta sun taru suna jiran isowar Aguiyi Ironsi a ranar 27 ga wata. Bayan da ya gama da Benin sai ya nufi Ibadan inda ya hadu da ajalinsa. Kuma shi kansa Sarkin Benin ya shiga tsakani inda ya tara manyan sojoji ya ce musu don Allah da Annabinsa kasar Benin ba ta saba da fitina ba tun tuni. Suna matukar maraba da baki ba ya son a zubar da jinin kowa a cikin kasarsa. Saboda haka kowane bangare ya mayar da takobinsa a kube domin Allah. Wannan magana ta wannan dattijon arziki ta ratsa dukkan bangarora biyu na soja kuma babu wanda ya yi wani abu a Benin. Saboda haka ba a kashe kowa ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!