Connect with us

RAHOTANNI

Ba A Bi Doka Ba Wajen Soke Zaben Tafawa Balewa, Inji PDP

Published

on

Jam’iyyar PDP a jihar Bauchi ta bayyana cewar soke zaben karamar hukumar Tafawa Balewa da hukumar INEC ta yi sam ba a ginasa a bisa doron doka ba.
Jam’iyyar tana mai shaida cewan an gudanar da zabe bisa gaskiya da kuma ayyana sakamakon zabe cikin kyakkyawar yanayi a lokacin da baturiyar zaben karamar hukumar Misis Dominion Anosike ta ke bayyana sakamakon zaben a matakin karamar hukumar, jam’iyyar ta yi zargin ana shirya mata makarkashiya ne a kasa ya sanya aka shigo da wasu matsaloli a lokacin da jami’ar ta ce sanar da sakamakon zaben a ofishin INEC.
PDP ta shaida cewar an samu barazanar neman kawo rudani ne kawai a bisa tabbatar da cewar jam’iyyar ta samu rinjaye a yankin, don haka ne suka bayyana cewar a amshi sakamakon zabe bisa adalci domin kwanciyar hankalin jihar ta Bauchi.
Shugaban jam’iyyar PDP a jihar Bauchi, Alhaji Hamza K. Akuyam shine ya shaida hakan a wani taron manema labaru da suka kira a jiya, inda yake mai shaida suna kira da babban murya ga hukumar zabe da su tabbatar da ayyana sakamakon zaben da ya basu gagarumar nasarar lashe kujerar gwamnan jihar.
Jam’iyyar ta bukaci a amince da sakamakon zaben karamar hukumar Tafawa Balewa cikin hanzari domin samun nasararta da dawo da kwanciyar hankalin jama’an jihar, “INEC ta ayyana nasarar wanda ya ci zaben, alabashi dukkanin mai korafi yana da ikon zuwa kotu domin kalubalantar sakamakon zaben,” Inji PDP.
Akuyam yana mai daurawa da cewa, “Muna Allawadai da yunkurin soke zaben nan ba tare da bin dokokin zabe ba, wanda hakan ya nuna cewar zaben jihar Bauchi bai kammalu ba, wannan abun damuwa ne sosai,” Inji Akuyam.
PDP ta zargi Kwamishinan ‘yan sandan jihar da kuma shugaban sashin RRS na rundunar ‘yan sandan da ciwa wakilan jam’iyyarta mutunci a lokaci da bayan gudanar da zaben, wanda ta nuna cewar ba za ta amince da wannan matakin ba, tana kira da masu hurumi kan lamarin su shigo ciki.
Akuyam ya bukaci a sauya shugaban INEC a jihar Bauchi da kuma kwamishinan ‘yan sandan jihar cikin gaggawa, “A baiwa talakawa abun da suke so, a bamu zabenmu shine babban abun da muke so a halin yanzu,” A cewarsu.
Ya ce, za su bi dukkanin matakai muddin basu saba wa doka ba, amma ya shaida cewar dukkanin wani matakin da ya saba wa doka ba za su lamunceshi ba, “Dukkanin wani mataki na shari’a za mu bi domin ganin an tabbatar mana da nasararmu, idan wannan sake zaben da za a yi a wasu mazabu ya kasance a bisa doka za mu yi, amma muddin aka daurasa bisa rashin doka ba za mu kasance a ciki ba,” Inji shugaban jam’iyyar ta PDP.
Da yake tofa albarkacin bakinsa a wajen taron manema labarun wanda suka yi hadaka da Kakakin majalisar tarayya, kososhi a PDP da kuma shi kansa dan takarar gwamnan jihar Bauchi a karkashin PDP din, Sanata Bala Muhammad Abdulkadir, ya shaida cewar dukkanin alamu kawo yanzu suna cike da farin ciki da godiya wa Allah a bisa wannan gagarumar nasarar da ya samu, ya nuna hakan da soyayyar da jama’an jihar suka nuna masa, kana ya yi alkarin baiwa marar da kunya wajen kyautata musu.
Sanata Bala ya sha alwashin cewar zai bi matakan da suka dace domin ayyana masa sakamakonsu na hakika da zai bashi zarafin kasancewa gwamnan jihar ta Bauchi, a cewar shi; “Wannan abun da aka yi mana, an nuna mana kauna an nuna mana soyayya kuma an bamu dama, za mu tabbatar da nuna musu kauna wajen yin ababuwan da suka dace kamar yadda jama’a suka nuna mana kauna,” Inji shi.
Ya kuma ce, “Ina tabbatar wa jama’an jihar Bauchi za mu bi dukkanin matakan doka wajen jawo hankalan mutane da suke da wani tsari na badakala na sama da fadi da rashawa da suke son su yi amfani da shi domin kwace mana abun da Allah ya bamu; kuma ba za mu yi kasa a guiwa ba, mu ‘yan jihar Bauchi ne, kuma ‘yan Nijeriya, a cikin ikon Allah, Allah ya sa mun isa kuma za mu isa.
“Kuma ina shaida wa jama’an da suka zabemu shine za mu kasa za mu tsare har yanzu za mu kara domin tabbatar da bayyana mana hakikanin sakamakonmu,” Inji Kaura.
Wakilinmu ya shaida mana cewar Misis Dominion Anosike ita ce baturiyar tattara sakamakon zaben karamar hukumar Tafawa Balewa, ta shaida wad akin taron amsar sakamakon zaben gwamnan jihar Bauchi cewar ta fuskanci barazana da cin mutunci a lokacin da take kokarin tattara sakamakon zaben, wanda hakan ya jawo muhawara mai karfi a tsakanin wakilan jam’iyyar APC da PDP, daga karshe babban jami’in tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Bauchi Farfesa Kyari Muhammad ya sanar da soke zaben dukkanin mazabun da aka samu matsala, yana mai bayar da umurnin a sake gudanar da zaben a cikin kwanaki 21.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!