Connect with us

KASUWANCI

CBN Da EFCC Na Shirin Hana Masu Laifi Bude Asusun Ajiya A Bankuna

Published

on

A ranar Talatar data gabata ce, Jami’an  Babban Bankin Nijeriya CBN da kuma Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC suka gana da nufin kara karfafa yakn da akeyi da cin hanci da rashawa a Nijeriya.

A cikin sanarwar da CBN ya fitar, ya bayyana cewar, duk wani ko koma wani kamfani da aka samu a cikin watabadakala akan tattalin arzikin kasa a Nijeriya mai yuwa a hana masu bude asusun ajiya a bankunan dake kasar nan.

An gudanar da ganawar ce a shalkwatar CBN dake garin Abujainda ganawar ta basu damar musayar kwarewa da kuma kalubalen da ake fuskanata ta yaki da cin hanci da rahsawa a Nijeriya.

Director  sashen bayanai na CBN Isaac Okorafor ya bayyana cewar, EFCC da CBN sun samar da dabarun dakile cin hanci da rashawa da kuma yiwa tattalin arzikin Nijeriya zagon kasa, indahakan ya hadada, fasakwaurin shigo da kaya cikin Nijeriya da suka hadada, Shinkafa, kayan masaku, takin zamni, Alkama da kuma sauran kayan da aka haramta shigowa dasu cikin kasar nan da kuma dakile shigowar kudaden kasar waje cin Nijeriya ta haramtacciyar hanya.

Sauran fannonin da CBN da EFCC sukayi hadaka sun hadada, sarafarra kudi ta haramtacciyar hanya da kuma sanya ido akan yadda yan siya a kasar nan suke yin safarar kudi ta haramtacciyar hanya.

Mista Jeremiah Abue,  Darakta nasashen  CBN  ne ya jagoranci ganawara, inda CBN da EFCC suka amince da yin musayar bayanai da sanya ido akan hada-hadar kudi.

In za’a iya tunawa, CBN a karkashin inuwar kwamtin ma’aikatan banki suka bayyana cewar, dukkan wanda aka samu yana yiwa tattalin arzikin Nijeriya zagon kasa, za’a hana masa bude asusun ajiya a bankunan kasar nan.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!