Connect with us

MAKALAR YAU

Mace A Gabas Da Yamma: Wanne Ne Ba Wane Ne Ba?

Published

on

Shekaran jiya akai ranar Mata A Kimiyya (Women In Science) ta duniya. Rana ce da ake tunawa da matan da sukai fice a duniyar Kimiyya don a girmamasu ko don hakan ya zama wata hanya da zata ingiza ragowar mata su ma su fito a dama dasu a bangaren ilimin kimiyyar da yan uwansu maza sukaimusu nisa ta kowace fuska. Tare da cewa addinin musulinci yace neman ilimi (kowane iri ne) wajibine akan mace da namiji, to amma ko dai matan basu dauki wannan umarni ba ko kuma mazan sun yaudaresu sun dauka neman ilimin bautar maza shi kadaine ilimin da mace zatai bayan sallah da azumi. Yan kadan zaka gani daga mata sun taba wani abin yabawa a bangaren Kimiyyar. Yan kadan ka taba ji sun zama kamar Mary Curie a yayin da irinsu Albert Einstein da Issac Newton suka cika duniya. Haka take har a duniyar musulmi. Kafin kaji an ce Al-ijliya Al-Asturabiy ko Sutayta Almahmali to sai kaji ana maganar Ibnul Haytham, Al-jahidh, Alkhawarizmy ko Ibn Sina. Dama dai, kamar yadda Yubal Noah Harari ya fada acikin littafinsa “Sapiens”, haka tarihi ya faro tun tale-tale. Maza sune suka hana mata yin rawar gaban hantsi kuma suke zuwa daga baya su nuna kamar matan ne ragwaye. Mutum baki dayansa mai rauni ne (Wa khulikal insan dha’efa) ba mata kawai ba. Wasu ne kawai saboda son kansu suka juya lamarin kamar iya mace abin ya shafa.

Daga Yamma:

Ka duba allukan talla, kwalayen sabulu, gidajen talabijin, kwalbar turare da kalandun gidajen magani, ta haka zaka gane irin yadda wannan zamani ba ya ganin komai ajikin mace face surarta kawai da yake wasa da ita. Mutanen yamma basa ganin mace a komai sai amfaninta na jin dadinsu da kuma abar wasansu ta biya bukatunsu. Har sunayen turare sai kaji sun sanya sunan mace sun hada da abinda zai biya bukatun sha’awarsu. “Scandalous Woman” ko “Sedy Babe”. Har ta kai sun fara yin ‘yar tsanar da zata biya musu sha’awarsu da irin siffar macen da suke bukata! Ta haka zasu samu nasarar mace ta koma kwaikwayar ‘yar tsana ta hanyar abinda likitoci suke kira da “plastic surgery”.

Haka suke bukatar mace har takai sun dinkamata shimi kuma suka budamata wuyan yayi fadi domin su ga tsagar kirjinta. Suka janyo wuyan can baya domin su ga rabin gadon bayan ta. A haka dai suka tsuttsuke kayan mace kuma suka sanyata ta sanya takalmi mai tsini domin ta turo kirjinta kuma ta matsar da bayanta ya fito sosai. Na duba sai naga mafi yawan masu dinkawa mata kaya (fashion designers) a kasashen waje maza ne! Daga Gucci, Luois Buitton, Burberry, Dolce & Gabbana zuwa Calbin Klein duk maza ne! Maza ne suke bukatar mata su biyamusu bukatunsu na tattalin arziki da na sha’awa. Su zuga mace da kalamai masu dadi suna gayamata cewa babu wanda ya kaita kyau… gaskiya kafarki tana birgeni… bayanki ya fita sosai… kirjinki yana birgewa… duk a haka suka mantar da ita suna gayamata yin tsirara ado ne!

A haka sukai nasara akan mace har ta dauka rainon ‘ya’yanta wahalar da kai ne. Domin cimma burinsu na samun ma’aikaci cikin sauki, suka zugata da cewa zata iya aikata duk abinda namiji zai aikata ko da jikinta ba zai iya yin hakan ba. Maimakon su bata shugabar kamfani kamar sauran mazaje, sai suka bata sakatariya don ta tausasawa bakinsu. Suka cemata jikinta mallakinta ne don tana da ‘yanci ta basu su yi amfani dashi. Haka suka samu nasara akanta a waje kuma suka sa ta lalata gidanta. Biyu babu ko daya kenan. Yayin da ta tsufa kuma suka wurgata gidan tsofaffi don sun gaji da ita. Duk muryar Celine Dione sai da Shakira ta doketa. Yanzu kuma yayin su Rihanna da Nicki Minaj suke kafin su watsar dasu. To amma me ya sa duk tsufan Snoop Doggy Dog har yanzu ana yi dashi? Me ya sa har yanzu basu manta da Dr. Dre ba?

Daga Gabas:

Tun asali macen gabas aka fara yaudara har ta farfado kafin ta yamma ta fada gurin. Addini ne yazo ya nuna mace tana da hakkin zama mutum. Aka dinga bata gado maimakon gadarta da ake. Ya zamana zata iya zama malama maimakon jahilcinta da aka sanya take ganin ado ne. Addini ya sanya aka dena binneta domin a mutunta rayuwarta. A haka har ta yi wasu ‘yan shekaru tana cin wannan moriya kafin wadanda suka fi ta wayo su kara amfani da addinin ta mummunar hanya wajen gallaza mata. Masu rawaito hadisan karya suka yawaita wajen muzanta mace. Suka bi ta har lahira sukace wai Annabi (saw) yace mata sun fi yawa a wuta! Wannan ba maganar Manzon Allah bace. Acikin “Bible (Old Testament)” aka daukota aka yi mata isnadi har marawaita suka dinga rawaitowa.

Yayin da mace take dauke da sirrin Ubangiji acikinta a lokacin haihuwa amma a haka wasu suke ganinta a wata mai sharrin da har ya fi na shedan! Basu gayamata cewa mala’ikune suke sauka acikinta ba har suke rubuta arzikin danta acikinta da sirrin Ubangiji ba. Abinda yafi damunsu shine itace tafi yawa a wuta. Tare da cewa duk kashe-kashen da akai a duniya maza ne sukai, daga Ghenghiz Khan zuwa Adolf Hitler, amma a haka aka ce mace tafi shedan barna! Ina zaton musulmi sun kasa banbance tsakanin “sharri” da “makirci” ne shi yasa suke ganin kamar Allah yace mace tafi shedan sharri a yayin da shi bai ma fada ba. Kai ko “kaidi” da yace a “Suratu Yusuf” ba shine ya fada ba, rawaito maganar yake.

Yahudawa suna cewa mace sai ta yi tsarki har sau biyu matukar mace ta haifa ba namiji ba! Bayahude zai tsaya a gurin ibada yana godewa Ubangiji da bai yi shi mace ko kafiri ba! Yana ganin sharrin mace har ya fi na kafirci ko kwatankwacinsa ne agurinsa!

Hatta masu falsafa suna ganin mace sharri ce. Haka Aristotle ya fada! Tare da cewa Plato ya yi maganganu akan girman mace a littafinsa “Jamhuriyya (Republic)” amma shima yana godewa Allah da bai yi shi a mace ba saboda ya kalli yadda ake cutar ta ne. Shi kam Nietschez har umarni yake bayarwa akan duk mutumin da zai je gun matarsa to ya tafi da bulala!

Dawo Da Magana:

Yayin da mace take shan wannan azaba ta kowace fuska ta yaya zata iya zama wata gawurtacciya a kimiyya? An samu malaman addini mata dayawa amma idan ka kwatantasu da maza zaka ga yan kadanne. An samu masana Kimiyya mata dayawa amma in ka aunasu da maza to basu kai komai ba. Iya ji da kanta da mace take ya isheta azabar duniya balle kuma ana hadamata da busharar tafi maza yawa a wuta.

Mafita:

Ki yi ilimi kawai. Ki san addini daga inda ya dace ba agun yan kasuwar addini da suke fakewa da addini wajen cimma burinsu ba. Ki gane iya ina ne matsayinki don kada garin neman gira ki rasa ido. Kada wani ya yaudareki bayan kin tsuguna kin haifeshi kuma yace baki da hankali. Ki yi karatu iya kokarinki kuma kisan hakkokin da ake tsammanin ki bawa iyalinki da kuma wanda zaki karba daga iyalinki. Da ke da mijinki duk daya kuke amma shine shugabanki a zaman aure kamar yadda kike shugabar ‘ya’yanki a zaman gida. Shugaban mutane kuwa shine mai hidimtamusu da basu umarni. Tare da cewa kina da hakkin fita gun aiki amma kada ki yarda fita gun aiki yafi kula da iyalinki muhimmanci. Duk maza da mata, Allah ya haliccesu daya ne amma kuma ya banbantamusu rayuwa. Kada ki yarda.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!