Connect with us

SIYASA

Alhaji Aminu Ahmed Ya Zama Dan Majalisar Jihar Kaduna A Makarfi

Published

on

A ranar Lahadi, kwana daya da gudanar da zaben majalisar Kaduna da hukumar zabe mai zaman kanta ta jagoranta a karamar hukumar Makarfi, ta bayyana dan takarar jam’iyyar APC Alhaji Aminu Ahmed da cewar shi ne ya sami nasara a zaben da aka aka yi.
Da ya ke gabatar da sakamakon zaben da aka yi, wanda ya jagoranci zaben Farofesa Dangana Sunday, malai a Jami’ar Ahhmadu Bello da ke Zariya, ya bayyana cewar, Alhaji Aminu Ahmed na jam’iyyar APC ya sami kuri’a dubu dari 133, da dubu 957, ya yin da Alhaji Garba Mohammed, Yeriman Makarfi ya sami kuri’a dubu 22, da dari 652, ya sami zama na biyu a cikin wadanda suka fafata domin neman zama wakili zuwa majalisar jihar Kaduna, a wannan shekara ta 2019.
Fafesa Dangana Sunday, ya tabbatar da cewar, Alhaji Aminu Ahmed na jam’iyyar APC, shi ne ya sami kuri’u mafi yawa da ya ba shi damar zama zababben dan majalisar jihar Kaduna da zai wakilci karamar hukumar Makarfi daga wannnan shekara gta 2019 zuwa 2023.
A zantawar da wakilin LEADERHSIP A Yau ya yi da Zababben dan majalisar Alhaji Aminu Ahmed jim kadan bayan bayyana sakamakon zaben, ya nuna matukar godiyarsa ga Allah da ya tabbatar ma sad a wannan nasara na cin zaben da ya yi.
Alhaji Aminu ya kuma gode wa magoya bayan jam’iyyar APC na karamar hukumar Makarfi da sauran al’ummar karamar hukumar na wannan dama da suka ba shi, na ya zama wakilin karamar hukumar Makarfi a majalisar jihar Kaduna a karkashin jam’iyyar APC.
Alhaji Aminu Ahmed ya kara da cewar, a tsawon wakilcin da zai yi wa al’ummar karamar hukumar Makarfi a majalisar jihar Kaduna, zai yi wakilcin da al’umma za su amfana, da ganin an sami ribar dimukuradiyya daga gwamnatin jihar Kaduna a fannoni da dama.
Zababben dan majalisar jihar Kaduna daga karamar hukumar Makarfi Alhaji Aminu Ahmed, ya kammala da kira ga daukacin al’ummar karamar hukumar Makarfi, da su ba shi duk goyon bayan da ya kamata, tare da yi ma sa addu’o’in da za su zama silar samun yin wakilci nagari, ga daukacin al’ummar karamar hukumar Makarfi baki daya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!