Connect with us

KASUWANCI

An Shirya Samar Da Karin Rijiyoyin Mai 37 A Nijeriya

Published

on

Hukumar Kula da Albarkatun mai DPR ta sanar da cewar, an amince da samar da jimlar karin rijiyoyin mai guda 37 don kara yawan sarrafa danyen mai a Nijeriya zuwa ganguna 189,850 a kullum.
An jiyo cewar, daga cikin ribiyoyin mai guda 37 guda 29 an sanya a sahun samar da ci gaba, inda kuma hukumar ta DPR ta ware sauran guda 8 da aka hada su a guri guda.
Hukumar ta sanar da hakan ne a cikin kundin ta na kwanan na na nasarorin data samu a shekarar 2018, wanda wakilinmu ya samo daga gunt Ma’akatar Mai da Albarkatu dake garin Abuja a ranar Juma’ar data gabata.
Daga cikin wasu nasaraorin na 2018, DPR ta bayyana cewar, ta amince da rijiyoyin mai guda 37 da kuma ware guda 8 daga cikin 29 na samar da ci gaba harda sababbin guda 7, inda man da za’a sarrafa zai kai kimanin gangunan danyen mai 189,850 a kullum in an kaddmar dasu.
Hukumar ta kara da cewar, ta samu nasarar sanya ido akan ayyukan hakar rijiyoyin mai guda 50 da 10 da ake tunani da muma guda 39 na ci gaba masu zurfin kilomita 1,260.74.
Acewar humumar, an kuma samar da bayanan 3D seismic daga cikin zurfin da ya kai yawan 3,272.11 da aka amince tare da amincewa da bayar da lasisin haka rijiyoyin mai guda 39 daga cikin su guda 25 suna gudanar da ayyukan hakar rijiyar mai.
Hukumar ta ci gaba da cewar, danyen mai na Nijeriya samfarin da aka ware a ranar 1 ga watan Disamabr shekarar 2018, ya kai yawan gangunan danyen mai biliyan 36.971, inda ya kai kashi 1.93 da kuma yawan 51.79 a shekaraun baya.
DPR ta kara da cewar, yawan adadin samfarin danyen mai na condensate da aka sararafa ya kai ganguna 1,973,995 a cikin watan Yunin shekarar 2018.
Hukumar ta ci gaba da cewa, an kuma wanzar da bayar da lasisin sarrafa mai na kan tudu ta hanyar yin amfani da yanar gizo, inda kuma amincewr akayi ta ta hanayar sanya ido ta ROMS da tsarin defo-defo da tsarin shigowa da fitarwa ta EPS data LBPS da kuma ta ROS.
DPR ta sanar da cewar, a cinin shekarar ta sake sabuntawa sabuwar amincewa da fannin zaiyi amfani dashi akan yarjejeniyar, inda ake sa ran zai rage rikicin CHA.
Ta kara da cewar, adadin iskar gas ta kasa ta kai tiriliyan 199.09 na zurfin kafa a ranar 1 ga Janairun 2018.
Wannan acewar Hukumar ya karu da kashi 0.18 samada na ranar 1 ga Janairun 2017, inda ta kara da cewar, an gano sababbin hudu a cikin shekarar data gabata.
Sabuwar hakar ta kai zurfin kafa biliyan 37.43 ta iskar gas ta NAG.
DPR ta ce, a dubin data yi na fiye da 2019 an kara inganta fannin, inda hukumar ta bayyana cewar zata kuma janyo masu hakar mai da kuma kamfanonin dake sarrafa man tare da yin alkawarin ci gaba da bin ka’ida yadda kamfanonin cikin gida zasu dinga hako man da kuma sarrafa shi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!