Connect with us

SIYASA

Ba Mu Amince Da Sakamakon Zaben Jihar Kaduna Ba – Ashiru Kudan

Published

on

Dan takarar kujerar Gwamna Jihar kaduna, Honarabul Isah Mohammed Ashiru Kudan, ya ce basu amince da sakamakon zaben da aka gudanar a Jihar kaduna ba, domin haka sun bukaci hukumar zabe INEC da ta soke sakamakon zaben ba tare da wani bata lokaci ba.
Honarabul Isah Mohammed Ashiru ya bayyana haka ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a gidansa dake Kaduna.
Ya ce, su da Uwar Jam’iyyar PDP na Jihar Kaduna, basu gamsu da yadda aka gudanar da zaben ba, wanda suka yi zargin an tafka magudi a wurare daban dabam na tashoshin zabe, domin haka a cewarsa, sun yi watsi da sakamakon zaben.
Isah Ashiru ya ce, haka an gudanar da zabe ba tare da an yi amfani da na’urar tantance masu yin zaben ba ” Card Reader “, musamman a kananan hukumomin zariya, Giwa, IKara,Soba,Birnin-Gwari, Kaduna ta kudu, Kaduna ta Arewa, IGabi, da Kubau.
Ya ce an tafka magudi a wadannan kananan hukumomin tare da tursasa ma wakilansu masu sanya ido a runfunan zaben.
Haka nan, sun yi zargin an yi amfani da jami’an tsaro saboda a canza alkaluman sakamakon zaben wanda ya ce basu amince da sakamakon zaben ba.
Ashiru ya kawo dalilai cewa ta yaya za’a yi a ce kuri’un da aka Kada a zaben Shugaban kasa, amma wanda aka kada a zaben Gwamna ya fi shi yawa, a cewarsa, hakan ya nuna karara an tafka magudi sosai a wannan zabe.
Ya kara da cewa, wuraren da suke da rinjayen magoya baya, an ki kai kayan aikin zaben da wurin, sannan ga tursasa ma wakilansu da aka yi.
Har ila yau, Isa Ashiru ya ce, a Kakuri Gwari suna zargin an yi Amfani sojoji wajen yunkurin lalata alkamunan zaben.
Daga karshe, ya ce sun rubuta sun mika korafinsu ga hukumar zabe INEC, a ga me da abubuwan da suka gano a zaben wadanda basu amince do su ba, kuma ba zasu amince da sakamakon zaben ba.
Honarabul Isa Ashiru Kudan, ya yaba wa Al’ummar Jihar Kaduna, saboda yadda suka jajirce suka fito suka yi zabe cikin natsuwa domin Jam’iyyar PDP ta lashe zabe amma ga abin da ya faru.
Haka ya bukaci dimbin magoya bayansu da su Kwantar da hankalinsu, su saurari irin matakin da zasu dauka domin ganin an yi adalci. A cewarsa
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: